#BIKIN_JARUMAN_KANNYWOOD: Ali Nuhu Ya Lashe Kambun Jarumin Jarumai - TopicsExpress



          

#BIKIN_JARUMAN_KANNYWOOD: Ali Nuhu Ya Lashe Kambun Jarumin Jarumai Na MTN Ali Nuhu ya yi nasarar lashe kambun Jarumin Jarumai na 2013 a bikin jaruman Kannywood da kamfanin sadarwa na MTN ya dauki nauyi a karo na farko. Nafisa Abdullahi ce ta lashe kambun a bangaren mata, sai gwarzon mai bada umarni Malam Aminu Saira. Sadi Sidi Sharifai ne ya samu nasarar zama gwarzon mawaki a wakarsa ta Daga Allah Ne. Sai kuma fim din Wani Gari da ya cinye kyautar fim din da ya fi kowane kyau a 2013. Sani Danja, Yakubu Muhammad, Adam A. Zango, Zuwaira Ismail, Rabiu Ibrahim Daushe, Yakubu M. Kumo da sauran su duk sun samu kyautuka a bikin. Wannan shi ne karshen kawo muku yadda wainar da ake toyawa kai tsaye a wurin bikin bada lambobin yabon, da ake gudanarwa a halin yanzu a Kanon Dabo.
Posted on: Sun, 24 Nov 2013 00:45:03 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015