#BREAKING NEWS Jiya a Wurin da aka tanadarwa manyan bakin #PDP - TopicsExpress



          

#BREAKING NEWS Jiya a Wurin da aka tanadarwa manyan bakin #PDP ya ruguzo akan mutane! A Jiya ne wata kungiya mai suna TRANSFORMATION AMBASSADORS OF NIGERIA (TAN) ta shirya wani gagarumin taro don nuna goyon bayan jonathan a garin Minna Jahar Niger, a filin Trade Fair Complex dake Jahar. Ana tsakiyar taron ne sai wani 6angare da manyan baki suke zaune wato VIP Seating Area ya rufto (Ya fado) kan wadansu mutane, cikin wanda abun ya rutsa da su akwai jiga-jigan Jamiyyar ta PDP na kasa da na Jahar ta Niger wanda suka hada da Ministan yada labarai na kasa wato #LABARAN MAKO, Gwamna BABANGIDA ALIYU, Sanata mai wakiltar Abuja GABRIEL ADUDA, da dai sauran manyan jamian tarayya na Jahar ta Niger, Jamian kungiyar (TAN) sunce angarzaya da wanda sukaji rauni Asibiti don yi musu magani. A wani jawabi da Gwamnan ya furta wato BABANGIDA ALIYU yace mutane su dauki wannan abu a matsayin kaddara kuma wannan yar manuniyace cewa #PDP zata samu nasara a zabe mai zuwa. Shima Ministan LABARAN MAKO yace; Hakika wannan ya nuna cewa JONATHAN shine zai lashe zaben 2015 don ko a Jahar sa ta Nasarawa zasu kawo wa JONATHAN kaso 95% a cikin kuriunsu. Mu kuma sai muce adduar bayin Allah ce take nuna tabbatuwar Allah ya kar6a: Muje zuwa wai Mahaukaci ya hau Kura. Via: Lecturer Aminu Muhammad Kaura (Lamk)
Posted on: Sun, 14 Sep 2014 06:23:06 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015