#GARE_KU Lalle ma babyn nan, ni zatai yiwa wayo bakina ya fada - TopicsExpress



          

#GARE_KU Lalle ma babyn nan, ni zatai yiwa wayo bakina ya fada kasa-kasa, ta dago kanta daga fuskar wayarta ta kalleni tace, mai kace ne, nayi ajiyar zuciya da na tabbatar bataji mai nace ba, na kalleta ina yaqe nace da ita, cewa nayi katin na naira nawa zaa sanya miki a wayar, tayi murumushi tace dani maza kenan akwai ku da qoqari Allah sarki ai ba da yawa nake so ba, ko na 2500 ya isa nayi SUB na 1500 na bar na 1000 a waya na, kasan kobe SUB dina zai qare. Yayi murmushi sannan ya sanya hannu a aljifunsa ya zaro dubu uku yan dari-dari sababi guda 3, ya miqa mata, yana qoqarin yayi magana ta katse hanzari da cewa, Thanks my Pop Corn, 500 change din na sayawa su siyama Snickers. Ta juya ta nufi adai-daita sahun da ke jiranta a bakin titi, wanda shima tuntuni gogan naku ya biya shi kudinsa. Ya bude kofar motar mahaifiyarsa ya shiga, sai bayan ya tadda motar ne ya tuna ashe 3000 da ya bata, kudin da mahaifiyarsa ta aikeshi ya sayo PIZZA HOT ne don taron baqin da zatai. Kash, a nan zan tsaya amma yan uwa mai zaku kira wannan gogan? Ita ma da mai zaa kirata? #PRINCE_AHMAD_AMOEVA 2B0EEE99 08066038946
Posted on: Tue, 03 Dec 2013 17:10:10 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015