**** Idan shedan ya ga ka bace kuma ka bi bataccen tafarki to - TopicsExpress



          

**** Idan shedan ya ga ka bace kuma ka bi bataccen tafarki to babu abinda ze yi da shi da muqarrabansa na daga mutane da aljanu se suyi ta yawo da hankalinka, sun mayar da kai dabba kuma wanda besan me yake yi ba. Tabbas duk wanda Allah be nufa da shiriya ba to babu wanda ze iya shiryar dashi. = Kimanin kwanaki biyar kenan a nan cikin garin #Gummi dake cikin jahar Zamfara a duk inda kaga tawagar Yan bidia babu zancen da suke yi se BAYYANAR INYASI A CIKIN WATA. Idan suka ga ahlussunnah a kusa dasu se su dinga cewa ...AI AYA CE DAGA CIKIN AYOYIN ALLAH, IDAN KANA DA RABO..., KUMA BA ABIN MAMAKI BANE YA BAYYANA A CIKIN WATA TUNDA GASHI CIKIN IKON ALLAH ANNABI SALIHU YA FITAR DA TAGUWA DAGA DUTSE... = Amma kuma ba anan gizo ke saqa ba, domin kuwa DA KANSU YAN BIDIAR KE QARYATA HAKAN. = Daga cikin muridinsu da ya fara qirqirar hakan; ya tara jamaarsa domin su gani amma daga qarshe suka gane qarya ce zalla har suke fadar SUN RENA MANA HANKALI NE SHI YASA... Akwai kuma wani malamin makaranta da matansa suka qaryata shi, suka ce da ace da gaske ne ai da ya tayar dasu daga bacci domin su gani... Yan makarantarsa kuwa, da suka je ya fesa masu qarya se suka zo gida suna nuna wata wai da nufin GA INYASI DA MALAM YA GANI A WATA, SE IYAYENSU (DUK DA SU MA YAN BIDIA NE) AMMA SUKA DINGA FADAR ... INDAI WANNAN ABIN ME DUHU DAKE CIKIN WATA NE IYASS TO QARYA YAKE DOMIN KUWA TUN MUNA YARA QANANA MUKE GANINSHI A CIKIN WATA. = YA ALLAH KA TSARE MANA IMANIN MU KA KUMA TSAYAR DA DUGA-DUGANMU AKAN SUNNAR ANNABI SAW.
Posted on: Tue, 19 Nov 2013 21:25:13 +0000

Recently Viewed Topics




© 2015