•Ina Wani Sauran Mai Imanin Kuma? Wata rana ne, wani mai kudi ya - TopicsExpress



          

•Ina Wani Sauran Mai Imanin Kuma? Wata rana ne, wani mai kudi ya sa aka sayo masa raguna da babbar Sallah domin ya rabawa talakawa marasa karfi. Mutumin nan ya sa aka kawo masa ragunan bayan masallaci. Bayan an idar da Sallah, sai ya mike tsaye ya ce: “jama’a ina mai tsoron Allah a nan?” sai wani bawan Allah ya daga hannu, sai ya nuna shi ya ce masa ya fita waje, suka je bayan masallaci ya zabi katon rago ya sa wuka ya yanka, mai kudin nan ya ce masa ya dauka ya kai gidansa, ya yi godiya ya dauka ya tafi. Mai kudin nan ya kara dawowa karo na biyu ya sake tambaya, wani ma ya daga hannu shi ma aka ba shi. A karo na uku sai mai kudin nan ya manta ya shigo cikin masallacin nan da wukar a hannunsa duk jini a jikinta sai ya kara cewa “ina wani mai tsoron Allah yake?” sai kowa ya ki daga hannu sai wannan ya dubi wannan, wancan ya dubi wancan, kowa ya ga wuka da jini a jikinta kuma duk wanda ya tafi baya dawowa, aka rasa wanda zai kara daga hannu, can Ladan ya ce “Ga liman nan ai ina tunanin cewa shi ne ya fi kowa jin tsoron Allah a cikinmu!” nan da nan Liman ya yi wuf ya ce “IN JI UWAR WA?” 🌝🌝🌝
Posted on: Tue, 01 Oct 2013 07:01:56 +0000

Trending Topics



And there came unto me one of the seven angels which had the seven
Obama and Co. is much worse than an embarrassment!!! And he is
If you like to eat, you should read this. Multinational

Recently Viewed Topics




© 2015