> JIBWIS GOMBE STATE NHQ JOS HADISIN SALLAMA DAYA An samu daga - TopicsExpress



          

> JIBWIS GOMBE STATE NHQ JOS HADISIN SALLAMA DAYA An samu daga Aishatu Matar Annabi (saw) tace “Annabi (saw) yana yin sallama guda daya ne acikin sallah” Sa`ad ibn Hisham Ibn Amir ya tafi zuwa ga Abdullahi Ibn abbas, ya bashi labari da wannan Magana ta Aishatu cewa Annabi (saw) ya kasance yana yin sallama guda ne acikin sallah.Sai Ibn Abbas yace tayi gaskiya (Muslim 2170). A cikin ruwayar Tirmizi “Lallai Manzon Allah (saw) ya kasance yana yin sallama acikin sallah, guda daya tagabansa, sannan ya karkata kansa zuwa dama kadan”(Tirmizi 1320). Daga salmata Ibn Ak,wa,i yace “ naga Manzon Allah (saw) yayi sallama guda daya”( Ibn Majah 1297). Don haka, an samu ruwayoyi daga Annabi (saw) cewa yayi sallama daya acikin sallah gurare da dama, haka kuma an ruwaito daga khalifofi guda hudu, Abubakar da Umar da Usman da Aliyu da kuma sauran sahabbai kamar ibn Umar da Anas da ibn aby aufa, da Aishatu matar Annabi (saw)da Sa,ad ibn aby Waqqas da salmata bn akawa.u, da jama,a da yawa daga Tabi,ai bayan sahabban. Saboda haka ya tabbata kenan Manzon Allah yana fita daga Sallah da Sallama daya tak. Sigarta shine ASSALAMU ALAIKUM. (Fathul Bary Li ibn Rajab 659 ko Aujazul Masalik 2145 ko Umdatul Qary 6123—124) Imamu Nawawi da Ibn Munzir sunce malamai sunhadu kancewa ba abinda ke wajaba ga mai sallah sai sallama daya tak ( Muslim Bisharhin Nawawi 380 ko Sahihu Fiqhus Sunnah 1127—326).* Aby Wa`il da Yahya Ibn Wasib da Umar Ibn AbdulAzeez da Hassan da Ibn Sirin da Qasim Ibn Muhammad da Aishatu (RA) da Anas da Aby Aliya da Aby Raja`ida Ibn Aby Awfi da Ibn Umar da Sa`eed bn Jubair da Suwaidu da qaisu ibn Aby hazim, kuma dukkansu an ruwaito daga garesu da Isnadi mai kyau, kuma AbdurRazaq ya ambaci Sallama daya daga Zuhuri. Tirmizi yace “ Jama`a da yawa daga cikin Sahabban Annabi (saw) da tabi’ ai da wasunsu , sun zabi yin Sallama daya a sallar Farilla”(Nailal Audar 2343 ). Imamu Ahmad ya ruwaito daga Abdullahi Ibn Aby Awfi cewa Annabi (saw) ya kasance yana fita a sallah ne da sallama daya tak (Musnad na Ahmad 1236 ko irwa il galil *232—33). A cikin wata ruwaya Annabi (saw) ya kasance yana fita a sallah da Sallama Daya wajen Fuskarsa akan sharadin Muslim.Haka kuma Ibn Majah da Ahmad da Nisa`i da Tirmizi da Hakeem da Ibn Hibban da Darul- Quduni sun ruwaito da lafazin cewa “Manzon Allah (saw) ya kasance yana yin sallama daya ne wajen fuskarsa(Nailal Audar 2341 —342).Ahmad yace Salih yace Ibn Muhd yace lalle shi zuhair amintacce ne mai gaskiya.Haka kuma Abu Hatim da wasunsu duk sun tabbatar da haka, kuma hakika Bukhari ya ruwaito Wannan yana nuna amincinsa..Amma Bukhari ya takaita akan fadinsa yayi sallama ba tare da ambaton adadi ba, ya dai ce ATTASLIMU ba TASLIMATANI ba,don haka ATTASLIMU shine asalin kalmar wato MASDARI.MASDARI kuwa baya Magana akan adadi,wato kadan ko mai yawa,don haka sallama daya ta shiga. An tambayi Malik akan sallama daya a cikin sallah,sai yace haka al`amarin yake.Shugabanni magabata sun kasance suna yin sallama daya ne,sallama biyu ta karfafu ne a lokacin Banu Hashim.Laisu yace mun riski shugabanni magabata da sauran mutane suna sallama daya ne a cikin sallah “ASSALAMU ALAIKUM”(Mukhta sar Iktilaful Ulama,u Lid Dahawi 1590kuma Ahmad ya ruwaito cewa mutanen Madinah sun kasance suna sallama dayane a cikin sallah,kuma yace sallama biyu ta daukaku ne a cikin zamanin Bany Hashim ma`ana a cikin Mulkin Bany Abbas.Faruwar sallama biyu daga Kuhfa ne wato Iraqi.A wannan lokacin Mutanen Madinah sun kasance suna sallama daya ne tak kamar yadda suka gada daga Annabi,sai akai amfani dakarfin mulki wajen tilastasu ga sallama biyu .Laisu yace “masu Magana akan sallama biyunma, mafiya yawansu sun amince akan idan Mutum ya takaita akan sallama daya ta isar masa, kuma sallarsa ta inganta”.saboda haka Ibnul- Munzir ya ambaci ijima,I kan sallama daya. An ruwaito daga Ibn Umar yin sallama daya ga liman da wanda yake sallah shi kadai, da kuma yin sallama uku ga wanda yake Mamu kuma akwai wani tare da shi agefen hagu.Malik da Dara-Qudani sun tafi akan haka cikin abinda suka ruwaito cewa “Annabi(saw) ya umarcemu da muyi wa limamanmu sallama, kuma sashin mu yayiwa sashi sallama”(Dara Kuduni Hadisi na 1373).Hakika Annabi (saw)yayi sallama daya da Abubakar da Umar da Usman da Umar Ibn Abdul-Azeez. (mudawwana juzu,I nadaya shafi 196) kuma hadisin ingantaccene daga Aishatu (R.A).Hakeem yace hadisin ingantaccene akan sharadin Bukhari da Muslim.Hakama Sheikh Ahmad Shakir alokacinda yake tahaqiqi kan sunanuttirmizi, yace: sallama daya ingan taccene daga Annabi (saw) nikuma inacewa wannan hadisin har ma Albani wanda yake ingantawa ko ya raunana yadda yaga dama, shima ya inganta wannan hadisin a cikin sahihu ibnu majah (750). Kuma hakika an ruwaito sallama biyu daga Abdullahi Ibn Mas`ud,kenan kaga ashe sallama biyumma akwai hadisi * tokaga Ashe sallama daya ko biyu duk wanda kayi sallarka ta inganta , saidai sallama daya tafi yawan hadissai ingantattu, shiyasa bukari bai ruwaici hadisin sallama biyuba
Posted on: Fri, 12 Jul 2013 10:26:01 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015