!!! KOFAR ILIMI 1 !!! Wata rana bayan manzon Allah s.a.w yayi - TopicsExpress



          

!!! KOFAR ILIMI 1 !!! Wata rana bayan manzon Allah s.a.w yayi wafati, sai wani bayahude mai ilimi yazo wajen sahabbai yace dasu Ga wata tambaya idan kuka bani amsarta zan muslumta,sukace masa kayi tambayarka,bayahudennan yace ((AKWAI WANI ABU GUDA 1 WANDA SAMA KO QASA GABAS KO YAMMA KUDU DA AREWA ALLAH BAISAN DASHI BA,WAI WANE ABUNE WANNAN? Shiru tsawon lokaci baa bashi amsaba,sai bayahude yace idan baku bani amsaba to na qureku kuma na qure addininku,yana gama fadin wannan magana ABU ZARRIN ya tashi cikin azama ya nufi gidan IMAMU ALI IB ABITALIB yace ya Abal Hassan kazo ka ceci addinin dan uwanka kaga baya raye kaji abinda ke faruwa. Cikin hanzari IMAMU ALI ya iso wajen,Abdullahi ibn Abbas yace sabida hanzari Imamu ALI A.S bai idasa sanya mayafin saba sai daya iso wajen,yace ina bayahuden yake yi tambayarka,bayahude ya maimata tambayarsa,IMAMU ALI ya gaya masa nine ALI BIN ABUTALIB dan uwan manzon Allah saw,yacewa bayahude amsar tambayarka itace ((ABINDA ALLAH BAISAN DASHI BA SAMA KO QASA,GABAS KO YAMMA,KUDU KO AREWA SHINE ABOKIN TARAYYA,maana ALLAH BAISAN YANADA ABOKIN TARAYYABA SAMA KO QASA GABAS KO YAMMA KUDU KO AREWA)) bayahude ya ranqwafa akan guyawunsa gaban IMAM ALI yace LA ILAHA ILLALLAH MUHAMMADUR RASULULLAH ALI WALIYULLAH Dama Manzon Allah s.a.w yace NINE BIRNIN ILMI ALI SHINE KOFAR
Posted on: Mon, 27 Jan 2014 19:23:06 +0000

Trending Topics



ass="stbody" style="min-height:30px;">
1531 RANGER HWY, WEATHERFORD- Large sale - ITEMS FROM 2

Recently Viewed Topics




© 2015