**** MAKIRCIN SHAIDAN GA DAN ADAM **** (2) A lokacin da ya wuce - TopicsExpress



          

**** MAKIRCIN SHAIDAN GA DAN ADAM **** (2) A lokacin da ya wuce mun tsaya a dai-dai inda ** Manzon Allah SAW ya ce, “idan suna karatun Alkur’ani fa?” Sai Iblis ya ce, “sai a narkar da ni, kamar yadda ake narkar da darma a cikin wuta.” **Sai Manzon Allah SAW ya ce, “to idan suka yi sadaka fa?” Sai Iblis ya ce, “sai in ji kamar mai sadakar nan ya dauki zarto ya rabani gida biyu.” **Sai Manzon Allah SAW ya ce, “me ya kawo haka, ya aba marrata?” Sai Iblis ya ce, “domin a cikin sadaka akwai kyawawan abubuwa guda hudu: *1. Hakika mai sadaka Allah Madaukaki Yana saukar masa da albarka a cikin dukiyarsa. *2. Kuma Yana soyar dashi a wajen bayinSa. *3. Kuma Yana sanya sadakarsa ta zama hijabi tsakaninsa da wuta. *4. Kuma Ubangiji Yana yaye masa Talauci da masifu.” **Sai Manzon Allah SAW ya ce, “to me kake cewa a kan Abubakar?” Sai Iblis ya ce, “ya Muhammadu, ai Abubakar bai bi ni ba a lokacin Jahiliyya. Yaya zai bi ni a wannan zamani?” **Sai Manzon Allah SAW ya ce, “to me kake cewa a kan Umar?” Sai Iblis ya ce, “ai ban taba cin karo da Umar ba face sai na yi ta kaina.” **Sai Manzon Allah SAW ya ce, “to me kake cewa a kan Usman?” Sai Iblis ya ce, “ina jin kunyar wanda mala’ikun Ubangiji suke jin kunyarsa.” **Sai Manzon Allah SAW ya ce, “to me kake cewa a kan Aliyu?” Sai Iblis ya ce, “kaicona, ina ma na rabu da shi , shi kuma ya rabu da ni. Amma ina! bai yarda da haka ba. **Sai Manzon Allah SAW ya ce, “na gode wa Allah da Ya azurta al’ummata, kai kuma Ya tsiyataka, har zuwa ranar Alkiyama.” Sai Iblis ya ce, “ba mai yiyuwa ba ne. Ina ka ga tsirar al’ummarka alhali ni ina raye zuwa lokaci abin sani? Yaya za ka dinga farin ciki a kan al’ummarka, alhali ni ina mai shiga cikin jikinsu da magudanar jininsu da tsoka, kuma alhali su ba sa ganina. Kai, wallahi na rantse da Wanda Ya halicce ni kuma Ya jinkirta min zuwa ranar tashi, sai na hallakar da su gabaki dayan su. Jahilansu da malamansu.Wadanda suka iya karatu da wadanda ba su iya karatu ba. Da kuma masu bautar Ubangiji, sai dai bayin Ubangiji tsarkakakku. **Sai Manzon Allah SAW ya ce, “to su wane ne tsarkakakku a wajenka?” Sai shaidan yace,“ya Muhammadu, yanzu ba ka san cewa duk wanda yake kaunar duniya da dukiya baya cikin tsarkakakkun bayin Allah Madaukaki ba? Amma idan kaga mutum baya kaunar duniya, baya kaunar dukiya kuma ba ya kaunar yabo balle a yabe shi, to hakika nasan wannan yana daga cikin bayin Allah tsarkakakku. To wannan sai na rabu da shi domin ya fi karfina. Hakika idan bawa ya dawwama a kan son dukiya da son a yabe shi kuma zuciyarsa ta ta’allaka sha’awe- sha’awen duniya, to hakika shi wannan ya tattare dukkan abin da na siffanta maku. ## “Yanzu ya Muhammadu, ba ka san son dukiya na daga cikin manya- manyan zunubai ba? ## Yanzu ya Muhammadu, ba ka san cewa son shugabanci yana daga cikin manya-manyan zunubai ba? ## Ya Muhammadu, ba ka san cewa ni ina da ’ya’ya dubu saba’in ba? Kuma kowane daya daga cikinsu yana da rundunar shaidanu guda dubu saba’in a karkashinsa? *Akwai daga cikinsu wanda na wakilta shi a kan tsofaffi, amma matasa kuwa babu wani sabani tsakanina da su. *Amma kananan yara kuwa sai shaidanu su dinga wasa da su kamar yadda suka ga dama. *Akwai daga cikinsu wanda hakika na wakilta shi ga masu bautar Ubangiji. *Akwai daga cikinsu wanda na wakilta shi ga masu gudun duniya, suna kaiwa suna komowa a tsakaninsu, kuma suna fitar da su daga wannan hali zuwa wancan hali, daga wannan kofar zuwa waccan kofar, har sai sun fitar da su daga hanyoyi zuwa wadansu hanyoyi. Ni kuma sai na bata musu tsarkin aikinsu, alhali suna masu bautar Allah Madaukaki ba tare da tsarkakewar aiki ba, alhali kuma su basu sani ba. (ZAMU CI GABA IN SHAA ALLAHU) Ya Allah Ka Kare Mu Daga Sharrin Iblis Laantacce....... admin Auwal bauchi
Posted on: Sat, 26 Oct 2013 15:05:42 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015