•••SARKAKIYA••• »»LABARIN RAYUWAR AMINATU Ta - TopicsExpress



          

•••SARKAKIYA••• »»LABARIN RAYUWAR AMINATU Ta kasance cikin wata kazamar rayuwa,ta hadu da ciwon hauka alokacin da take cikin tsakiyar budurcinta. Allah sarki aminatu marainiyar Allah tin tana yar shekara biyar a duniya mahaifanta suka mutu rayuwarta tacigaba da kasancewa awajan qanin mahaifinta, Alhaji Usman Ibrahim Alkens tasha baqar azaba a hannun matar kawunta Saratu irin matan nan ne marasa imani da tausayi bata duba maraicin Aminatu ba,ahaka tayi ta gana mata azaba iri iri tin tana karama har lokacin da ta zama budurwa Aminatu yarinyace kyakykyawa me matsakaicin tsayi farace amma ba fari na sosai ba tanada kira sosai ta cikakkiyar mace son kowa kinwanda yarasa Tin tana aji uku{primary 3} a makarantar sakandire , ta hadu da wani saurayi me suna Abdulrahman, sunyi matuqar shaquwa da Abdulrahman sosai ya kuma tallafawa rayuwar aminatu da ko wane irin taimakon kasancewar baya so ya ganta cikin kunci ko damuwa duk dade Abdulrahma ba wani bane kuma ba dan wani bane, Bashi da sanaar data wuce koyarwa malamin makaranta me karamin albashi, amma yayi rawar gani sosai wajan gina rayuwar aminatu, cikin nishadi da kuma walwala. Duk duniya aminatu bata da wanda yafi Abdulrahman, tana son shi so na haqiqa tana son shi son shi kamar yadda uwa take son danta bata da wani buri a rayuwar kamar ta wayi gari ta ganta agidan Abdulr ahman a matsayin matar sa ta sunnah, domin ta huta da irin cin kashin da Saratu take mata Tana aji shida a makarantar sakandire, anan ne wani mummunan al.amari ya faru akanta, al.amarin daya jefa rayuwar ta cikin rudani da tashin hankali Toh fa! Wani saurayi me Suna SALIM dashi taci karo acikin rayuwar ta Salim surayi ne dogo me kyakykyawan diri shekarun sa ashirin da takwas a duniya, babu yarinyar dazata ga Salim bata so zama dashi amatsayin miji ba Salim dan gata ne gaba da baya mahaifinsa hamshaqin me kudi ne kuma shi kadai ya haifa, dan gata ma aqasar waje yayi karatun sa yana dawowa, ya samar masa wani babban aiki me albashi da tsoka. Alokacin da Murjanatu tazo hutun ta na qarshe wanda daga shine zatayi candy, acikin hutun ne Salim ya hadu da ita yaji duk duniya babu macen da zai so kuma ya aura sai ita, saboda haka kai tsaye ya tunkare ta da maganar, amma taqi amincewa dashi, kasancewar Abdulrham ne za6inta kuma za6in mahaifanta. Duk wani irin jan hankali na samarin birne babu wanda Salim baija hankalin ta dashi ba amma taqi amince masa, daga nan ne fa ya canja salon takunsa ya tunkari mahaifanta da maganar tare da sauqe musu wani kaso me yawa na kudi baa dau wani tsawon lokaci ba ya canja tunanin kawunta, kwadayi ya shammaci zuciyar sa ya amince zai aurar da Aminatu ga Salim a satin data kammala karatun ta, yayi watsi da alqawarin da yayiwa Abdulrahman da mahaifan sa kafin hutun Aminatu ya kare ta koma makaranta, rayuwar ta tayi matuqar canjawa, duk tabi ta rame tayi baqi kasancewar kawunta yayi mata iyaka da Abdulrahman ya kuma bada ita ga Salim bayan ta koma makaranta da kamar sati uku, ta fara rashin lafiya me kama da ciwon hauka Makaranta ta bata kulawa ga jinyar ta amma babu wani sauqi da ya samu a wajanta ganin haka yasa su daukota su dawo da ita gida, a duk lokacin da ciwon ya motsa duk mutumin dake kusa da ita tana masa shaqa irin ta mutuwa wasu kuma takan kashe su har lahira. Bayan andawo da ita gida duk wani me maganin da aka dauko yayi mata aiki kashe shi take ta kashe masu maganin sun kai biyar a gidan su. Sakamakon haka tasa kawunta yayi watsi da rayuwar ta, ya kore ta acikin gidan sa ta koma rayuwar mahaukata marasa gata masu kwana a kasuwa ko bola, ta kashe mazaje da yawa masu yin qoqarin yin mata fyade a halin haukan ta. Waye zai tallafawa rayuwar Aminatu ya ceto ta daga ciwon haukan daya addabi rayuwar ta??
Posted on: Mon, 04 Nov 2013 19:38:44 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015