~~~{TUNASARWA}~~~ Ukubobi goma da zasu samu duk mai wasa da - TopicsExpress



          

~~~{TUNASARWA}~~~ Ukubobi goma da zasu samu duk mai wasa da sallah... guda 5 a duniya, 3 a yayin mutuwa, 2 a cikin kabari.. UKUBOBINSA A DUNIYA 1. Za a cire albarka a cikin rayuwarsa 2. Za a shafe kamannin salihai daga fuskarsa 3. Duk aikin da zai aikata ba za a bashi lada ba 4. Adduarsa ba za a karba ba 5. Bashi da rabo a cikin adduoin bayi na gari UKUBOBINSA A YAYIN MUTUWA 6. Zai mutu wulakantacce 7. Zai mutu yana mai jin yunwa 8. Zai mutu yana mai jin kishirwa, koda za a shayar da shi da kogunan duniya ba zasu rabashi da kishirwa ba UKUBOBINSA A CIKIN KABARI 9. Za a kuntata kabarinsa har sai hakarkarinsa sun sabawa juna 10. Za a kunna wuta a kabarinsa yana jujjuyawa akan garwashinta Ya Allah ka bamu ikon bauta maka kuma ka kara mana juriya da jajircewa wajen bautarka... Ameen Allahu Akbar!!!
Posted on: Thu, 31 Oct 2013 17:34:06 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015