#WANNAN-TAMASU-AURE-CHE Farfado da soyayyar aure Mazaje da yawa na - TopicsExpress



          

#WANNAN-TAMASU-AURE-CHE Farfado da soyayyar aure Mazaje da yawa na kukan cewa da mace ta yi haihuwar fari, to soyayyar tan a raguwa ga mijin ta zuwa ga yaran ta, su matan na fadin makamanci haka, amma akwai abubuwa da dama ma su kawo naqasu ga soyayyar ma’aurata tun kafin a je ga batun haihuwar ma. Halin Ko In Kula Na Ma’aurata Ga Soyayyar Su Bayan Aura, wasu ma’auratan na yin kuskure da rashin kula da soyayyar su har hasken ta ya dusashe a hankali, su kan tasa wasu al’amuran rayuwa, kamar neman kudi da harkokin yau da kullum sama da soyayyar da ke tsakanin su, ba su tattalin ta, ba su kula da ita, ‘yan abubuwan nuna soyayyar da ake yi kafin aure, irin su qure adaka dan burge juna, kyauta da kyautatawa, a tunanin su, daman dan a yi auren a ke soyayyar, to tunda an cimma buri shi ke nan ba batun nuna soyayya kuma, ita kuwa soyayya kamar sabuwar shuka ne, ko da a ce ana ruwan sama da zai shayar da ita, to dole sai an runqa nome mata ciyayi, da sa ma ta taki da maganin qwari, in ba haka ba sai ta mace. Tsoron Nuna Soyayya Akwai ma’auratan da ke danne soyayyar su, su qi nuna ta saboda tsoron sakamakon da hakan zai haifar ga rayuwar su. Wasu mazan na qin nuna soyayyar su ga matan wai don gudun raini, mata kuma na cewa in ka nuna ma namiji soyayya sai ya wulaqanta ka. Duk soyayyar da a ka boye ko a ka danne, to a hankali za ta mace, aure kuwa ba soyayya kamar abincin da ba gishiri ne, duk irin yadda ya tsaru sai ka ji shi salam a cikin baki. Qaranci ko Rashin Natsuwa Duk lokacin da masoya biyu su ka hadu su na soyayya da niyyar qulluwar aure a tsakanin su, to za ka taras akwai wani abu da ya hada su har soyayyar ta qullu tsakanin su. Kowannen akwai wani abu day a gani a jikin dayan wanda ya burge shi har ya tsirar da wannan soyayyar cikin zuciyar shi, sannan akwai wani dadi da wata natsuwa das u ke hangen samu in Allah ya yi su ka zama ma’aurata. Misali, kamar mace da ta yi hangen in ta auri wane za ta samu rayuwar hutawa da jin dadi domin alamun hakan day a nuna ma ta, sai bayan auren ta taras bah aka ba ne, to wani fanni na natsuwar da ta ke fatan samu daga wannan aure ya kau, wannan dole ya kawo naqasu cikin soyayyar ta ke ma mijin na ta. Ko namijin da auri mace da fatan samun natsuwa ta fannin kula da tsare ma sa gida, ko natsuwar sa ta fannin sha’awa, sai ya samu akasin haka ko abin da bai kai yadda yak e so ba, to dole soyayyar tat a ragu cikin zuciyar ta. To da an sami raguwar soyayya, sai raguwar tausayi da raguwar kyautatawa, wanda hakan su ma a hankali su ke naqasa soyayya, domin zuciya ba ta iya ci-gaba da son mutumin da bai kyautata ma ta. Lokacin soyayya na da zafi- zafin ta, ma’aurata na kau da kai daga kuskuren junan su, amma in soyayya ta fara daqushewa, dan abin da bai kai ya kawo ba sai ya zama dalilin sa-in-sa tsakanin ma’aurata, wanda zai haifar da yawan gardama a tsakanin su, kowa na ganin laifin kowa, har runqa fada ma juna baqaqen maganganu Canje-Canjen da Aure Ke kawowa Ga Soyayya Lokacin soyayyar samartaka, masoya su na tare kuma sun a son juna, amma ba wani qulli tsakanin su mai wajabta wata sadaukarwa. Kowannen su shi kadai yak e kuma kan shi kadai ya sani, mace tan a da dammar ta je duk inda ta so ba lallai sai masoyin ta ya sani ba balle har ta nemi izinin shi, shi kuma namijin cikin kadai ya san day a ciyar, ba nauyin kowa da ya rataya a wuyan shi. Amma da anyi aure wasu sabbin al’amura za su shigo cikin soyayyar ma’aurata, nauyin kula da gida daukar ciki da haihuwa ga mace, kai kawo da fadi tashin da maigida zai ta yi don ganin ya samar ma iyalan san kayan buqatar rayuwa, da wasu nauyuka sadaukarwa da aure ke shigo da, duk sun a dauke hankalin ma’aurata daga soyayyar da ke tsakanin su har ya kasance sun a auren ne amma ba soyayya a cikin. Tasirin ‘Yan’uwa da Abokai Wasu ‘yan’uwan mata da na miji ko abokan su, ma su jin haushin irn kyakykyawar soyayyar da ke tsakanin ma’aurata, na iya hura wutar rikici tsakanin su, ta hanyar yada maganganun qarya don ganin wannan soyayya ta samu naqasu. Tasirin Sinadaran Rayi Soyayya lokacin samartaka ta na da wani zaki da armashin da ya sha banban da kowace irin soyayya, masoya su na cikin tsananin so da qaunar juna, su na kewar junan, su na nuna kulawa ga juna, su na jin dadin kasancewa da juna, hatta murmushin da su ke ma juna daban ne da ko wane irin murmushin da su ke yi. A lokacin babban burin su shi ne kasancewa tare har abada. In Allah Ya qaddara su ka auri juna, soyayyar su lokacin amarci kuma ta fi ta lokacin samartaka, su kan ji kamar su na cikin wata aljannar duniya, wannan jin dadi har ya kan bayyanu a siffar su, inda annuri da annashuwa za su qaru a fuskar su. Amma a hankali sai soyayyar ta runqa ja da baya,to bayi allah amin afuwa don zan dakata anan sai wani lokachin idan mai kowa mai komai yakaimu by ahmad a baba admin00
Posted on: Sun, 29 Sep 2013 23:20:28 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015