** kashi na 3, labarin Niu lang da Zhi nu ** Amma, yaya mutum zai - TopicsExpress



          

** kashi na 3, labarin Niu lang da Zhi nu ** Amma, yaya mutum zai iya hawa can sama ? Ganin Niu Lang na bakin ciki kwarai, har yana neman kashe kansa, tsohon bijiminsa ya yi magana cewa, ‘Mai gida, sai ka kashe ni, ka shiga cikin fatata, za ka iya yin shawagi.’ Niu Lang ba ya so ya kashe bijiminsa, amma bijimin ya yi ya yi har Niu Lang ya yarda. Domin Niu Lang shi ma ya sani, ba ya da sauran hanyar da zai bi domin ceton Zhi Nu. Shi ya sa tare da hawaye a cikin idanunsa, ya kashe tsohon bijimin. Niu Lang ya shiga cikin fatan bijimin, ya dauki yaransa biyu, ya tashi zuwa can sama. Amma ba a yarda ya shiga cikin fadar sarkin aljanu ba. Sarkin aljanu ya ki yarda da shi da ya sadu da Zhi Nu. Niu Lang da yaransa suna ta rokon sarkin aljanu, suka gurfana a gaban sarkin aljanu, suka yi kuka, har a karshe dai sarkin ya yarda da su sadu a cikin dan lokaci. Da Zhi Nu ta fito daga cikin gidan yari, ta ga mijinta da yaranta, ta ji murna kwarai da gaske, tana ta kuka, har ta kasa magana. Amma, lokaci ya wuce cikin sauri, an kama Zhi Nu, za a sake mai da ita cikin gidan yari. Niu Lang ya bi ta yana gudu, sauran kadan zai kama hannunta. Amma matan sarkin ta cire fin da ke cikin gashin kansa, ta shata layi a tsakanin Niu Lang da Zhi Nu. Sai layin nan ya zama babban kogi. Niu Lang da Zhi Nu, daya ya tsaya a gefe nan, daya ma a gefe can, suna hangen juna, amma ba za su sadu da juna ba. Daga baya, shekara da shekaru, Niu Lang da Zhi Nu ba su iya gamuwa da juna ba, ban da ran 7 ga watan Yuli a bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin. A ran nan, tsuntsaye da yawa sun zo, sun kafa gada a kan kogin da fikafikansu domin Niu Lang da Zhi Nu da yaransu sun sadu da juna...... Laifin dadi qarewa... Inanan tape da wani sabon labari, idan kuna biye dani insani...
Posted on: Thu, 04 Jul 2013 02:38:16 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015