003"""ruwan bagaja""" dai in je wurin dutsen can, watakila ko na - TopicsExpress



          

003"""ruwan bagaja""" dai in je wurin dutsen can, watakila ko na sami ruwa ma in hadiya. Na tasam ma dutse haikan, ko da na isa gindin dutsen, sai na ga wani babban kogo, na yi tsammani ba a rasa ruwa cikinsa. Saboda haka na kutsa kaina ciki, na yi ta shiga. Can na yi zurfi da lafiya, sai na ji an ce, Kai! Mutum ko aljan? Da jinhakanan, sai na kadu, hantata ta dauki rawa. Na yi ta maza dai na ce, Mutum ne. Daga nan fa sai na ga wani tsoho ya taso mini tukuf da shi, yana da tasbaha a hannunsa. Ya tambaye ni labarina, na kwashe masa duk, tun daga farko har karshe. Ko da ya ji niyyata ta in debo Ruwan Bagaja ce sai yayi kara, kara mai tsanani, ya ce, Karyarka kuwa ta sha karya, dan samari. Wannan jawabi nasa ya tsinke ni. Da na ga ya natsa na ce, Baba, kai mutum ne ko aljan? Abin da ya sa na ce masa haka, don na gasuma ta kawo masa har ga kirji. Ya amsa mini ya ce, Ni mutum nedan uwanka, shekarata saba in a nan ina ibada ban taba ganin wani mahaluki ba sai fa kai yau. Ya shiga ba ni labarinsa, da labarin garinsu, da danginsa. Kwamfa ashe babana ne, wan Liman. Ko da Liman ya kan rika ba ni labarinsa, yana cewa ya bi uwa duniya, ba a san inda ya ke ba. Da ya gama, ni kuma na bayyana masa ko wane ne, sai muka rungume juna, muna kuka don murna. Ya tambayeni labaringida duka, na tsuguna na kwancemasa bakin jaka. Na kwana biyu nan gunsa na huta, ina cin ya yanitatuwa domin su ne abincinsa. Bayan mun saba da juna na ce masa ya buga mini kasa, ya gaya mini labarin niyyata. Ya buga kasa, ya ce, Ruwan Bagaja dai akwai shi a duniya, amma yana hannub aljannu. Karewa ma ba shi a bisa kasan nan da mu ke takawa. Da ya gama labarinsa nace, To, tun da dai akwai shi a duniya sai im mutu gun nemansa. Don Liman ba shi ya haifeni ba, ba ni bari a kunyatad da shi. Bayan na yi kwana saba inina tafiya, sai na isa Tambutu. Nayi shiri irin na fatake, na isa fun Sarki, na ce ni falke ne, kayana suna baya, za su zo bayan kwanauku, Abin da ya sa na ce haka donna baro wadansu shanu ne a baya na wani falke. Ka san tafiyar mara wuri sai cin zango, saboda haka na wuce su. Kullum da yamma sai in dami taro, in sayo miya, im bi kofar gidan da a sauka, in warwatsa ko ina. Abin da ya sa na ke haka, don ina da wani aboki ne, attajiri. To, ko da yaushe ya zo ganina da maraice, idan zai zauna mu gaisa, sai in cemasa, Kash! Yara kuwa sun bata gun da miya! In ya juya yamma in ce ai nan me duk miya ce. In yajuya kudu, do arewa, ni kan ce ai nan ma duk sun bata shi. Watau don ya ce lalle ni mai arziki ne. Dukan almajiran garin ni ke cishe su tun da na zo. Alhali kuwa da kyar na ke ci da kaina. Abin ikon Allah, dai kuwa suka fara tsammanin haka. Na ci bashi gunsa kamar na rabin jaka, kullum sai in yi ta yoi masa romon baka, ina cewa, Idan shanuna sun zo ba ni sayar wa kowa sai shi kadai, ya kama ko wane sa ya karya yadda ya ke so,don ni ke da abina. Da aka kwana kamar uku ba su zo ba, sai ran nan ya ga wadansufatake. Sai ya ce, Mu tambaye su labarin shanunka. Na ce, I, hakanan ne! Na tinkare su na ce, Shin kun baro wadansu shanu masu yawa nan baya? Suka amsa, suka ce, I, gobe suna isowa. Watau shanun can da na baro fa suka gani. Da na ga dai idan sun iso gobe karyata ta kare, sai na taafi gidan attajirin nan, na ce, Ina son fam hamsin kafin su iso da safe a yi ciniki. Nan da nan ya ba ni, watau jaka guda ke nan. Da fitata maimakonim bi hanya shararra sai ba yabki daji. Bayan na yi tafiyar kwana arba in da daya, sai na isa wani gari wai shi Saburi, wani babban birni ne. Amma duk garin jahilai ne na innalillahi, ba wanda ya san ko alif sai ni fa da na isa yau. Ni kuwa ban san kome be cikin Alkur ani, sai wata aya da na ke jimalam na ja kullum, in yana ashan, wai ita Muduhammatani. Da zuwana na sami wata doguwar tasbaha, na nufi wajen Sarkin, na ce ni malami ne. Ya ce, Daga ina? Na ce, Daga kasashen Larabawa. Da Sarki ya ji haka, ya yi murna da zuwana, ya ce, To, ina za ka? Na ce, Nan na zo. Kullul ina mafarki da kasan nan, ana gaya mini in zo in rika yi muku salla don za a sa ku aljannaku duka domin adalcinka, ya Sarki. Da Sarki ya ji haka, ya tara manyan gari duka ya gaya musu. Na sami wata shida cur ina yi musu salla, ban san abin da na kefadi ba sai Muduhammatani ko yaushe. Duk yaran gari aka kawo su in koya musu karatu. Bayan kwana kadan kowa ys hardace Muduhammatani. Wanda ya iya kwarai sai ya rika fadi da irin muryoyi dabam dabam, ko ya bude murya, ko ya shake, ko kuwa ya yi wata iri dabam, ya iyake nan. Bayan na yi wata kamar bakwai, ran nan sai wani babban malami ya fado garin, Sarki ya bashi labarin shaharata a kasar duka. Ka san malamai da son kure yan uwansu. Sai ya zo mukagaisa. Ni kuwas na tara kudi da yawa don sai abin da na ce a ke yi a garin, har am mai da ni kamar gunki. Da malamin man yazo muka gaisa, na ce, Ina sunanka! Ya ce, Sunana Malam Zurke dam Muhamman. Kai ina sunanka? Na ce, Malam Alhaji Imam. Malami uban malamai! Dagari ya waye aka je jun salla, ya jiban iya kome ba, sai ta fara sarana gun Sarki,
Posted on: Fri, 05 Jul 2013 23:23:15 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015