004.HIKAYAR DAN DAKO DA YAN MATA .. Mai jiran kofa ta dubesu, ta - TopicsExpress



          

004.HIKAYAR DAN DAKO DA YAN MATA .. Mai jiran kofa ta dubesu, ta gan su da siffar fatake, ta ce, “Ku jinkirta in sanar da ‘yan uwana!” Ta shiga ta sanar da sauran yam mata akan wadan nan fatake. Suka ce, “Je ki, ki shigo da su.” Ta bude musu kofa, suka ce da ita, “Yalla mu shigo da yardarki?” Ta ce da su, “Ku shigo!” Halifa ya shiga da Ja’afaru da Masruru a halin suna a siffar fatake. Yayin da yam mata suka gan su, kuma suka ga suna da almar dukiya a tare da su, sai suka tashi suka tare su da fara’a, suka gaishe su, suka girmama su. Suka ce, “Marhabin, maraba da bakinmu, mun yi murna da ganin ku, amma mu na da sharadi guda a wannan gida, kada ku yi magana a kan abin da babu ruwanku a ciki.” Su ka ce, “Na’am, mun amince da wannan sharadi.” Suka zauna, yam mata suka kawo musu abinci da abinsha. Bayan sun zauna, sai Halifa yayi duba izuwa ga dan dako da samari uku, sai ya ga samarin nan uku duka ido daya-daya ke gare su, kuma duka na hagu ne. Ya yi al’ajabi a kan wannan abu. Ya yi duba izuwa yam mata uku da abin da ke gare su na kyawo da cikar halitta, ya dimauta, ya yi al’ajabi. Suka zauna cikin hira da zance. Yam mata suka zo wa Halifa da giya tatacciya, ya ce, “Ni Alhaji ne!” Ya tashi daga cikinsu. Yarinya mai jiran kofa, ta tashi ta dauko tasa, zananniya, ta sa ruwa a cikinta, ta wanke ta sosai, ta zuba madara a ciki, ta diga ruwan sanyi ta garwaya shi da sukar ta rufe, ta dauko ta ajiye a gaban Halifa. Ya dauka ya sha, ya gode ma ta, ya ce a cikin ransa, “Babu makawa in saka wa wannan yarinya gobe bisa ga aikinta na alherin kyautatawa bako.” Yayin nan suka koma ga zancensu. Yayin da dare ya kusa rabawa, sai shugabar yam matan nan ta tashi, ta rike hannun Jekadiya, ta ce da ita, “Ya ‘yar uwata, ki tashi bisa ga biyan bukatata, mu biya bukatarmu.” Ta ce, “Na’am, ya ‘yar uwata.” Yayin nan kuma Mai jiran kofa ta tashi, samari uku, masu ido daya, suka bi bayanta, ta na bayan shugaba, Jekadiya na gabansu. Suka mika tsakiyar gida, suka shiga cikin wani daki. Bayan sun shiga ciki, suka yi kiran Dan dako, suka ce da shi, “Kai ne na farko da zuwa a wannan gida, don haka kai ba bako ba ne.” Ya ce da su, “Me kuke so in yi muku?” Sai suka nuna masa wasu karnuka guda biyu, daga babbakun karnai, da dagumi a wuyansu. Yam mata, suka ce da shi, “Ka taimaka mana ka jawo mana wadan nan karnuka zuwa tsakiyar dakin nan.” Dan dako ya rike su, ya shigo da su tsakiyar daki. Shugabar yam mata ta tashi, ta zare damuttsanta, ta dauki bulala, ta ce da Dan dako, “Gabato mini da karya daya daga cikin karnukan.” Ya jawot a da daguminta, ya gabatar da ita. Karya na kuka, tana rauda kanta zuwa ga yarinya. Yarinya ta sabkar mata da duka. Karya na kuka tana kururuwa, ba ta gushe ba tana dukan ta, har damuttsanta suka gaji, yayin nan ta yar da bulala daga hannunta, ta rungume karya a kirjinta, tana shafe mata hawaye, tana sumbatarta. Yayin nan ta ce da Dan dako, “Ka mayar da ita ka kawo ta biyun.” Ya zo da ita, ta aikata mata tamkar yadda ta aikata wa ta farko. Duk wannan abu ya faru a gaban samari uku da Halifa da Waziri da Sarkin Fada. Zuciyar Halifa ta dimauta, kirjinsa ya kuntata da wannan abu da ya gani, ya kyibci Ja’afaru, ya tambaye ta dalilin aikata wannan abu. Ja’afaru ya yi masa ishara da tuni akan sharadin yam mata. Sai ya yi kawai. Sai shugabar yam mata ta dubi yarinya Mai jiran kofa ta ce, “Ki tashi ga zuwa biyan bukatar ki.” Ta ce, “Na’am, ya ‘yar uwata.” Yayin nan shugabar yam mata, ta hau kan gadonta na marmar, jikinsa na dinari, kafafunsa na azurfa, ta ce wa yarinya Jekadiya, “Ku zo mini da abin da ke gareku.” Mai jiran kofa ta hau bisa gadon daga gefenta. Jekadiya ta shiga cikin taska, ta dauko jaka ta handalas, koriya, ta tsaya gaba ga yarinya, shugabar yam mata, ta warware jaka ta fitar da molo daga cikinta, ta gyarta tsakiyarsa, ta kada molo, ta yi waka, waka mai dimauta zuciyar ma’abota bege. Jekadiya na cikin rera wakarta ta soyayya, sai shaukin bege ya debi yarinya mai jiran kofa, ta tashi ta yayyaga tufafinta, ta fadi kasa somammiya. Yayin da jikinta ya yaye, Halifa ya gani a gare shi tabo na dukan bulala. Ya yi al’ajabi da haka, gayar al’ajabi. Jekadiya ta tashi, ta dauko ruwa, ta yayyafa mata a fuska. Ta farka, ta kawo mata tufafi, ta tufasashsheta. Halifa ya juya ga Ja’afaru ya ce, “Ko ka lura da tabo na bugun bulala a jikin wannan yarinya? Ni bani da ikon na yi kawai a kan wannan al’amari, lalle ne mu tambaye su akan kasancewar wadan nan al’amurra.” Ja’afaru ya ce, “Ya shugabana, sun shardanta mana a kan kada mu yi magana kan abin da babu ruwanmu a cikinsa, kuma mun amsa musu haka.” Samarin nan uku, masu ido daya-daya, suka ce, “Kaiconmu, da ba mu shigo wannan gida ba, mun kwana a wurin kwananmu, hakika kwananmu a nan ya gurbata mu da masifar da tsatso ke yankewa a gare ta.”zamu cigaba gobe karfe 9:00pm insha allahu
Posted on: Thu, 20 Feb 2014 22:04:45 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015