004"""ruwan bagaja""" yana cewa a gwada mu da shi a ga wanda ya - TopicsExpress



          

004"""ruwan bagaja""" yana cewa a gwada mu da shi a ga wanda ya fi. Sarki ya ce, A a, Malam Alhajiu Imam ba ya shafuwa nan kasar duka. Zurke dam Muhamman dai ya nace da tambaya don a kunyata ni, a yi mini dariya. Ran nan Sarki ya kira ni ya gaya mini duk abin da malamin nan ya gaya masa. Da na ji haka, sai na ce a raina, Yau fa karyar maza ta kare. Sarki ya ce, Ban ji ka ce kome ba. Na ce, Ina tuna jahilcin yaran almajirai ne masu ja da manya. Lalle dai karamin sani kukumi ne. Na ce Sarki ya aika a yi shela gobe da safe yaro da babba kowa ya zo, a taru a yi kure. Da Sarki ya ji haka, sai ya ce, Rika mini nan, malami uban malamai! Da gari ya waye duk aka taru. Sarki ya aika aka kirawo ni. Na zo na zauna tsakar taro. Ina zaune sai ga yara uku da wagagen littattafai. Na ce, Daga ina kuka fito? Suka ce, Dagamasaukin Malam Zurke dam Muhamman. Jim kadan sai ga malamin ya taho, taf, taf. Aka ba shi buzu ya zauna. Ga jama a makil. Bayan mun gaisa da shi, na ce, Wadanne littattafai ne ka kwaso? Ya ce akwai Attaura, Zabura, Linjila, Alkur ani, Samarkandi, Lawwali, Sani. Wadansu ba ni iya tuna sunannakinsu ban ko taba ji ba. Da na ji haka na ce, Af! Duk wadannan ba ka hardace su ba tukuna, sa an nan ka ke son jayayya da ni? Ya dube ni ya yi murmushi. Sa an nan ya ce wa wadansu yara, Ku kauda su can gefe, mu da kai za muyi. Ina amfanin sanin littafi kawai, karatun aku. Aka kauda su waje daya. Bayan an natsu, an yi shiru,na share kasa, sai ka ce mai shirin haddi, na za wata alama haka . Na dubi Malam Zurke na ce, Mene ne wannan? Ya ce, Nun ara ce. Na ce, Haba! Sake dai. Ya ce, Ra. Na ce, Haka a ke ra, a gidanku? Ya ce, Lam ara ce. Na ce, Wane makaryacin malami ne ya koya maka haka? Duk ya kare tsince-tsincen bakakensa na Alkur ani masu kama da wannan alama, na ce karya ya ke. Da ya ce ya bs ni gari sai na ce, Ku matso ku gani. Sa an nan na dubi mutane na ce, Wannan ba ra ba ce, ba lam ara ba ce, ba nun ara ba ce, tsayawar wata dareb farko ke nan. Jahilai suka dubi zanena suka ce, Hakanan ne, malam! Hakanan ne malamin malamai! Haka kuwa tsayuwa wata ya ke. Na dubi Malam Zurke, na ce was yara, Ku yi masaeho da ature. Suka bi shi Eho! Eho! Eho! Eho! Daga nan ko ta kan littattafansa bai biya ba, ya yi wajen gari, yara na jifa. Ya tsere da kyar. Ka ji rabona da wannan malami.
Posted on: Fri, 05 Jul 2013 23:27:51 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015