{16} …Rayuwar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam A Lokacin - TopicsExpress



          

{16} …Rayuwar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam A Lokacin Aikin Hajji°°°°°°°° .......... h- Sauran Al’amurra: Dangane da abin da ya shafi sigogi da yanayin shugabancin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ga mutane, a wannan lokaci na Aikin Hajji, akwai wasu abubuwa da dama da ya gudanar waxanda suka taimaka matuqa ga cin nasararsa. Abubuwan na iya taqaituwa a cikin waxannan ginshiqai: i) Kyakkyawan Tsari: Tun a garin Mina, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yiwa Aikin Hajjinsa kyakkyawan tsari, ta hanyar kimtsa jama’a da aje kowa daga cikinsu wurin da ya dace da shi. A inda ya tsara su gwargwadon kusancinsu zuwa gare shi. Qarami na bi wa babba. Kamar dai yadda Abdurrahman xan Miswar ya riwaito cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya gama yi wa mutane huxuba a Mina sai ya saukar da kowa inda ya dace da shi. Ya ce: “Muhajiruna su sauka a nan”. Sai ya nuna wani wuri dama ga alqibla ya ce: “Ansaru kuma a nan”. Ya nuna wani wuri hagu ga alqibla ya ce: “Sauran mutane su sauka a nan”. (SD:1951/SA:1719). A wata riwaya kuma aka ce: “Yana qare huxubarsa sai ya umurci Muhajiruna da su sauka a gaban masallaci, Ansaru kuma bayansa. Sannan ya saukar da sauran mutane (SAD:1957/SA:1724). Ka ji yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi. Amma a yau matsalolin da ke faruwa ga alhazzai a lokacin Aikin Hajji ba su da iyaka. Musamman na lokacin da suke gudanar da wasu ibadu. Ko idan za su bar wani wuri na ibada zuwa wani. sai ka ga ko wace jama’a na nuna son kai, da qoqarin halaka ‘yar uwarta. Duk tsarin da aka shata don cin nasarar ibadar, sai ka taras sun yi biris da shi, ko sun yi masa riqon sakainar kashi. Da ko wane alhaji zai yi qoqarin zama wani abin koyi ga sauran alhazai ‘yan uwansa ta hanyar yin kawaici, ya jinkirta da biyan buqatarsa, a lokacin da ta ci karo da wata maslaha ta sauran ‘yan uwansa alhazzai, to da musulmi sun ba duniya wani irin mamaki a fagen natsuwa, tsanaki da kyakkyawan Tsari. ii) Kula da Hidimar Mutane: Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kula da hidimar mutane ainun, ya kuma qarfafa ta a wannan lokaci. Saboda tabbatar da ita ne ya yi wa amminsa Abbas iznin zama garin makka tsawon kwanakin da ya kamata ace ya yi a Mina don ya kula da Aikinsa na shayar da mutane ruwa. (SB:1734). Kuma a lokacin da ya zo Sallallahu Alaihi Wasallama ya sami masu wannan hidima sun yi kace – kace, suna ta aiki. Don ya qara masu qwarin guiwa, sai ya ce masu: “Ku dage ku yi ta yi, haqiqa kuna kan wani aiki na gari” (SB:1636). Sai godiya ga Allah. Domin kuwa irin wannan qwazo da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya qarfafa, har yau bai gushe ba. Kullum masu sadaukar da qarfinsu da mafi yawan lokutansu ga hidimar alhazzai, da xora su a kan tafarki madaidaici, da kyautata masu, sai qara yawaita suke yi. Tattare da irin musgunawa da tsangwamar da suke haxuwa da ita wasu lokuta. Su ya kamata ayi ta fara’a da lale marhabin da su ko da yaushe. Amma duk wannan bata sa suka fasa ba. Alhamdu lillahi. Abin da ya kamaci ko wane alhaji shi ne, ya tuna faxar nan ta Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da yake cewa: “duk wanda bai gode wa mutane, to ko Allah ba ya gode wa”. Ta haka sai a gode da wannan aiki na alheri, ba tare da wata yankewa ba. Domin ko shakka babu godiyar zata qara masu kuzari da karsashi da nishaxi. iii) Tsare Haqqoqa: Haka kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi matuqar kiyayewa da tsare haqqoqan mutane a wannan lokaci, don kada su tozarta. Misalin wannan shi ne: hana ummuna Aisha Allah ya qara mata yarda yin tsaye a gina masa xaki a Mina don ya shiga. Da ta xaura niyyar yin haka sai ya ce mata: “ba sai kin wahalar da kanki ba. Ai Mina gaba dayanta masauki ce tun ga waxanda suka gabace mu” (JT:881/ MH:1/638/ SN:4/398/ ZM:2/267). Sai kuma qin kama wa masu hidimar shayar da alhazzai ruwan zamzam. Don tsoron kada haqqoqinsu su tozarta. Idan mutane suka rinjaye su. Sanadiyyar ganin har da shi Sallallahu Alaihi Wasallama cikin Aikin. Saboda kasancewar haka ya ce masu: “ba don tsoron kada mutane su takura ku ba, da na kama maku aikin nan. Har ma in xora taula a kafaxata” (SB:1636). Wannan shi ne abin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya koyar. Amma a yau, sai ga shi haqqoqan alhazzai, musamman masu xan qarfi daga cikinsu, na tozarta. Saboda buqatun wasu ‘yan tsiraru waxanda suka xauki duniya abin bauta. Haka kuwa na faruwa ne, saboda zaluntar alhazan da waxannan mutane ke yi ta fuskar rashin kula da hidimominsu, na masauki da zirga-zirgarsu; zowa da komawa. Ba irin waxannan mutane kawai ba. wasu haqqoqan ma, na wasu alhazzan a hannun wasu alhazzai ‘yan uwansu ne, waxanda ba su fatar haxuwa da alherin Allah, suke tozarta. Ba tare da la’akari da alfarmar qarshe da suke kanta ba. Saboda haka, wajibi ne a kan ko wane alhaji, ya yi qoqari iyakar zarafi, ya ga bai bi sawun waxannan mutane ba. ya yi gaggawa, matuqar yana da iko, ya kasance mai taimakon alhazai ‘yan’uwansa, ko da da kalmomin nasiha ne, da faxakarwa da bayar da agajin gaggawa. iv) Kishin Gaskiya: Duk da kasancewar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama mai tsananin jinqayi da tausaya wa mutane. Ga kuma kunya marar misali (SB:3562/SM:2316).. hakan ba ta tava hana shi gaggawar bayyana abin da yake gaskiya, da yin jan ido ba idan an tava ta. Koda kuwa hakan zata sosa ran wanda suke tare. Dalilan da ke tabbatar da jaruntakarsa da namijin qoqari da jajancewarsa Sallallahu Alaihi Wasallama a kan duk abin da ya shafi gaskiya, suna da yawa matuqa. Ga kaxan daga ciki: Xauki misalin karan tsayen da ya yi wa Falalu xan Abbas Allah ya yarda da su da hana shi ci gaba da kallon budurwar nan Bakhas’ama daya yi a kuma cikin dubu (SB:6228), wanda har hakan ta xauki hankalin amminsa Abbas Allah ya yarda da shi ya tambaye shi dalilin yin haka. Shi kuma Sallallahu Alaihi Wasallama ya karva masa da cewa: “Na ga hankalin saurayi da budurwa ne, ya kama hanyar shiga hannun shexan. Ban kuma san abin da zai faru ba (JT:885/HA:702). Misali na gaba kuma shi ne, lokacin da matarsa Sallallahu Alaihi Wasallama safiyyah ta ga wanki. Ya zaci cewa ba ta yi xawafi ba ga xaki a ranar layya, ashe ta yi. Mun gabatar da tambayar da ya yi cewa, shin Safiyyah za ta riqe mu ne? Sai kuma qin ba wa wasu sadaqa, tattare da cewa, sun roqe shi bisa dalilin cewa su majiya qarfi ne, da ke iya nema da guminsu (SAD:1633/SA:1438). Ina jin babban misali a wannan vangare, duk bai fi bijire wa mafi yawa daga cikin sahabbansa Allah ya yarda da su da ya yi ba, waxanda ba su zo da dabbobin hadaya ba, ya qi ajiye Haraminsa duk da yake hakan tafi soyuwa ga reshi don zama abin koyinsu. Ya kuma gaya masu farar gaskiya garin da garin cewa: “Ku sani ni ba zan ajiye harami ba kamar yadda na umurce ku da ajewa. Saboda ni da hadayata a hannu” (SB:7367). Saboda haka ya zama darasi ga ko wane musulmi, a gida da lokacin Aikin Hajji. Kada ya yarda son zuciyarsa ya hana shi bayanin abin da ya wajaba kansa na gaskiya da nasiha da faxakarwa, da horo da alheri da hani daga abin qi ko a gaban kowa. Domin kuwa kasa yin haka kasawa ce da rafashewa, ba kunya da kawaici ba. Domin kuwa Allah Ta’ala da kansa, ya faxi cewa ba ya jin nauyin faxar gaskiya. Saboda haka yin koyi da manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama shi ne wajibi. Ya tabbata cewa: “Ya fi amaryar da ke cikin lalle kunya” (SB:3562) amma duk da haka, zo ka ga irin yadda yake fushi da xaukar mataki idan an tava Allah. Kamar yadda Sayyida Aisha Allah ya qara mata yarda ta siffanta shi cewa: “Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bai tava xaga hannu ya bugi wani abu ba; ko matarsa ko hadiminsa. Sai fa idan an haxu ne a fagen jihadi. Haka kuma bai tava ko tunanin xaukar fansa, don an yi masa wani abu ba. Sai fa idan an yi wa wani hukunci na Allah karan tsaye. To nan kam zai yi fushi har ma ya xauki mataki, amma duk, saboda Allah maxaukakin Sarki” (SB:3560/SM:2328). v) Rashin Gallaza Ma Wanda Ya Yi Kuskure: Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ba mutum ne mai fushi da kaushin hali ba. Saboda haka ba ya gallaza wa wanda ya yi kuskure daga cikin sahabbansa Allah ya yarda da su. A maimakon haka, ya kan mayar da hankali ne, ga lurar da mutum idan ya fahimci ya jahilci abin ne ya kuma ci gaba da kula da shi har ya ga bai sake aikata kuskuren ba. haka zai zauna da shi, ko ‘yar fuska ba zai yi masa ba. Misalin wannan shi ne, qin kula da qoqarin gano sahabin nan da ya mayar masa da magana da cewa: “Yanzu sai dai mu isa Arafa da sauran ruwan janaba a jikinmu? A maimakon haka ma sai kawai ya ci gaba da qoqarin lurar da su, tare da xora su a kan abin da yake shi ne mafifici, da kuma dacewa da su a lokacin. Yana mai cewa: “kun fi kowa sanin cewa, babu wanda ya kai ni tsoron Allah, da gaskiya da biyayya gare shi. To ya kamata ku lura da cewa, ba don na zo da dabbobin hadaya waxanda ba a yanke su sai lokacinsu ba, ai babu abin da zai hana in aje haramina kamar yadda ya kamata a ce kun aje. Yanzu kuma da na fuskanci abin da na ba baya ba zan zo da su ba don inyi Umra a tare da ku. (SB:7367). Sai kuma rashin gallaza wa Falalu Allah ya yarda da shi da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi a kan waccan magana da mu ka faxa ta Bakhas’ama, da lokacin da kuma ya bi wasu ‘yan mata da ke gudu da kallo. Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a wannan lokaci bai yi wa xan’uwan nasa wata tsawa ko mugunyar magana ba. Sai dai kawai ya kama kansa a hankali Sallallahu Alaihi Wasallama ya xauke fuskarsa daga garesu. Tare kuma da ya maimaita hakan ba sau xaya ba. (SB:1513/SM:1218). Bayan wannan kuma sai rashin tozarta mutanen nan biyu da suka yi salla a gidajen su. Basu yi sallah tare da mutane ba da suka zo masallaci. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya mayar da hankali ga lurar da su, tare da xauke masu nauyi, da kuma xora su a kan abin da ya fi dacewa da su aikata (JT:219/SA:181). Wani misalin kuma mai qayatarwa shi ne, rashin musguna wa mutanen nan biyu da suka roqe shi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ba su sadaqa, alhali kuwa su majiya qarfi ne, da ke iya ci da guminsu. A maimakon ma ya tozarta su Sallallahu Alaihi Wasallama sai ya naxa su alqalai a kan matsalar. Wanda a qarshe, su da kansu suka haqura (SAD:1633/SA:1438). Ka kuwa san iyakar haquri da hikima ke nan. Wannan hali na Manzon Allah, ba ya zama xaya da na almajirai da malaman zamani. Waxanda fushi da miyagun kalamai su ne ado da kwalliyar nasiharsu, bayani kuma a wurinsu shi ne tozartawa da wofintar da mutane. Da sun harxe qafafu kuma, ko sun maqara makirifon cikin baki, ba abin da zaka ji yana fitowa bakinsu sai wautarwa da tura wa mutane haushi. Duk wannan wai da sunan karantarwa. A qarshe sai ka taras ba abin da za su qara wa mutane, illa ci gaba da aikata kurakuransu, da zama cikin vata. Kuma xaixaiku daga cikinsu, su yi ta da na sanin tambaya ko sauraren irin waxannan malamai da suka yi. Saboda sun tozarta su. To ka ga inda ma irin waxannan miyagun malamai, ba su tsoma bakinsu cikin al’amarin musulmi ba su da hakan ta fi zama alheri ga al’umma. Saboda gujewa irin wannan abu, wajibi ne duk wanda Allah Subhanahu Wa Ta’ala ya ba shi ilimin addini, da damar haxa baki da jama’a, ya yi qoqari iyakar zarafi ya yi koyi da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama . vi) Tiryan – Tiryan: Wataqila, babban abin da ya taimaka wa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ga cin nasara, a jagorancin da ya yi wa al’ummarsa a wannan lokaci na Aikin Hajji, duka bai fi kasancewar komai nasa tiryan – tairyan ya ke ba. Babu wani bayani da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama zai yi wa mutane, face ka taras da shi dalla – dalla, daki daki. Ya kan yi haka ne ta hanyar amfani da miqaqqen salo kuma sassauqa, mai armashi da kamsashi. Ta yadda jama’a ba za su qosa ba. Ko ana gabas suna yamma. Saboda haka sai gaba xayan mutanen da ke tare da shi, suka zama ala basiratin. Duk abinda suke buqata da gurin aiwatarwa ga shi ga fili sara. Kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama shi ne kawai makoma da makama, kuma shi ma ga shi gabansu ko da yaushe. Su kansu ibadodi na Aikin Hajji babu wadda aka voye masu. Ko aka kevance, sai wane da wane. Bayan kuma ga cikakken tsari kuma nagartacce, wanda akalarsa ke hannun mutum mafi nagarta da naqaltar jagoranci Sallallahu Alaihi Wasallama . Kai! Daidai da lokuta da wuraren ibadun an tantance su. Saboda haka kowa daga cikinsu ya san abin da ya kamata ya yi da wanda bai kamata ya yi ba. A kan haka kamata ya yi, a duk lokacin da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya shugabantar da mutum ga wani abu da ya shafi Aikin Hajji, ta hanyar hulxa da alhazai, to ya riqa yi masu bayanin komai dalla dalla, yadda za su gane abin da yake nufi cikin sauqi. vii) Nuna wa Mutane Qauna: Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kasance mutum mai sauqin kai, mai marhaba da mutane, tare da yi masu shimfixar fuska, mai yalwantaccen qirji. Mutum ne da ba a tava ganin xan Adamu mai xabi’ar murmushi kamarsa ba. Ko Magana yake yi da sahabbansa, zai yi ta ne cikin wani irin nishaxi da fara’a tare kuma da sa raha a cikin maganganunsa, ta yadda farin ciki zai cika zukatansu (MSH:200,205/ ANWA:180,182,207). Misalin da ke tabbatar da irin qauna da so da rahar da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya nuna wa mutane, tare da jawo su a jiki, a lokacin Aikin Hajji, shi ne abin da xan Abbas Allah ya yarda da su ya riwaito cewa: “Mun gabatar wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da ‘yan qananan yaran ‘yan gidan Abdul Muxxalabi, muna kan wasu jajayen raquma. Sai ya shiga daddafa qaqafunsu yana cewa: “Ya ku ‘yan uwana kada fa ku yi jifa sai rana ta vullo” (SIM:3025/SA:2451). Saboda haka yana da matuqar kyau, a duk lokacin da ka haxu da mutane a lokacin Aikin Hajji, ka yi masu kyakkyawar gaisuwa cikin fara’a da nashaxi, da sakin fuska. Idan kuma wata Magana ta haxa ku, to su ji kalmominka kamar farar waina a ruwan zuma. Idan wani aiki ne kuma, ka yi shi cikin tsanaki da natsuwa. Da haka sai ka sami karvuwa gare su, har su amince da kai. Ka kuma sami wata irin lada a wurin Allah, wadda ba ta misaltuwa. viii) Kamun kai da Kawaici: Kamar a ko wane lokaci na rayuwarsa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kasance mutum mai kamun kai da kawaici da kamala, da kwarjini ciki da waje a lokacin Aikin Hajjinsa. Ta yadda babu wanda ya kama qafarsa a fagen tsafta da cika fuska. Ga dai gashin kansa nan Sallallahu Alaihi Wasallama ya tsaftace shi, ya kuma shafe shi da mai, mai qamshi (SB:4398). Kamar yadda kuma bai fara Aikin na Hajji ba, sai da ya shafa wani irin turare mai qamshi (SM:1189/ SD:1801). Ya kuma yi wanka a lokacin (JT:830/ SA:664) da kuma kafin ya shiga garin Makka (SM:1259). Bayan wannan kuma, a wannan lokaci, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kasance mai kawaici da kwarjini. Ta hanyar nisantar duk wata Magana ko wani motsi, da bai dace ba (SN:3024/ SA:2827/ MA:1816). A sakamakon haka, sai mutane suka qara so da girmama shi, tare da shaya masa. Xaya daga cikin abubuwan da ke tabbatar da wannan magana, shi ne hadisin nan na harisu xan Amiru as-Sahmi Allah ya yarda da shi wanda yace: “Na ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a lokacin da yake a Mina da Arafa, mutane sun kewaye shi ta ko ina. Duk qungiyar Larabawan da ta zo ta gan shi, ba za ta wuce ba sai gaba xayansu, sun ce: “kai wannan irin fuska mai hasken albarka fa! Suna ta farin ciki da wannan annuri nasa da suka yi tozali da shi (SAD:1742/HA:1532). 2.6.1 Hannunka Mai Sanda: Saboda haka yana da matuqar kyau, musulmi ya kula da yanayin suturarsa. Kada ya yi banzar shiga. Ya kuma zama mai kamun kai daga yawaita wasa da barkwanci, tare da samun raha da nashaxi a cikin mu’amalarsa da mutane. Idan ya kiyaye waxannan, to mutane za su yi sha’awar haxa harka da shi, su kuma saurari duk abin da zai gaya masu a matsayin ilimi, har ma su kwaikwayi xabi’unsa. Kaxan kenan daga cikin abubuwa na kamala, waxanda suka bayyana ga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a lokacin Aikin Hajji, da mu’amalarsa da mutane, a matsayin jagoransu. Kuma ta hanyarsu ne ya sami nasarar huda zukatan jama’a, har suka qaunace shi, suka kuma amince da shi. A matsayin wanda komai ya umurce su da shi za su aikata cikin gaggawa, har ma da goggoriyo. Haka kuma za su yi idan ya hane su wani abu. Wannan xa’a kuma, sun yi masa ita ne, cikin daxin rai da yarda da kwaxayin lada da tsarkin niyya. To sai waxanda ke son musulmi su riqe su da hannu biyu a matsayin malamai kuma shugabanni, su auna xabi’unsu da halayensu, a kan ma’aunin waxannan xabi’u da halaye na Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama su ga irin banbanci da ke tsakani. Su kuma sani, babu yadda za’a yi wanda bai siffantu da waxannan halaye na Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ba ya samu karvuwa a farfajiyar zukatan musulmi. Domin kuwa duk maso xan kwarai to dole ne ya auri isassa.
Posted on: Tue, 22 Oct 2013 11:49:07 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015