{19} …Rayuwar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam A Lokacin - TopicsExpress



          

{19} …Rayuwar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam A Lokacin Aikin Hajji°°°°°°°° .......... 3.7 Ya Yi Masu Gargaxi Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kasance mai tsananin son ganin ya tsarkake iyalinsa daga ko wane irin savo da varna da abubuwan qi. Saboda haka yake tsaye haiqan ga yi masu gargaxi, da kuma hana su aikata laifuka, da hannunsa. Da zarar ya ga wani daga cikinsu ya kama hanyar shiga hannun shexan, nan take ne Annabi Subhanahu Wa Ta’ala zai kevo shi ya dawo da shi kan hanya. Misalin wannan shi ne abin da ya gudana tsakaninsa da falalu xan Abbas a lokacin da ya qura wa budurwar nan Bakhas’ama ido. Wadda ta zo domin ta yi fatawa ga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama. Da ganin haka kuwa sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya shiga tsakani, ya hana shi sake kallon ta, a aikace. Da kuma dai har wa yau, abin da ya faru tsakaninsa da shi Falalun Allah ya yarda da shi na hana shi da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi ci gaba da kallon wasu ‘yan mata da ke kaiwa da komowa (SM: 1218) Wani gargaxin da hani kuma, a cikin wata irin sura mai hikima da ya yi wa iyalin nasa Sallallahu Alaihi Wasallama shi ne buga misali da ya yi da su, da nufin mutane su xauki darasi daga gare su. Ya yi wannan ne a cikin wata huxuba da yayi wa mutane a filin Arafa. Inda yake cewa: “Ku saurara! Daga yau na kashe duk wata magana ta jahiliyya. Duk wani jini da ake bi bashi tun a wancan lokaci na saryar da shi. Farkon kuwa, jinin da na kashe maganarsa, shi ne jinin xan uwana xan Rabiata wanda Huzailu ta kashe, daidai lokacin da ake shayar da shi a bani Sa’ad. Kuma farkon ribar da zan saryarwa, ita ce ribarmu, ta wajen Abbas xan Abdul Muxxalabi. Daga yau ba wannan Magana, na kashe ta. Kuma ta mutu mututus”. Allahu Akbar, ka ji maza. Amma sai gashi a yau ana ji ana gani, abubuwan da suka yi hannun riga da koyarwar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama na ta faruwa a cikin iyali, babu mai cewa qala daga cikin magabatanmu. Tattare kuma da ana cikin lokacin gudanar da Aikin Hajji. Babu ruwan kowa, koda kuwa cikin waxannan abubuwan da ke faruwa akwai abin da ke iya vata Aikin Hajjin nasu, ko ya yi masa tasgaro. A gaban idon irin waxannan uwayen gidaje, mata daga cikin iyalin nasu, ke kwave-kwave irin waxanda Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya qi kamar, tsiraici da fasiqanci, da cuxanya da mazajen da ba halas a gare su ba, da sauran su. To, fa ya kamata a faxakar, Allah Subhanahu Wa Ta’ala na yin rahamarSa ne ga bawan da ya tsare kansa kamar yadda Ya wajabta masa. Ta hanyar kare iyalinsa daga faxawa tarkon shexan, ta fuskar aikata miyagun ayyuka. Ya kuma dage kai da fata a kan horonsu da aikata alheri da nisantar sharri ko wani iri ne. 3.8 Annabi Ya Tausaya Masu A wannan lokaci na Aikin Hajji, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kasance mai matuqar tausayawa iyalinsa baki xaya. Tare kuma da mayar da hankali da kusantar da masu rauni daga cikinsu. Ya kan zavar masu abu mai sauqi a duk lokacin da buqatar hakan ta kama. Tare da bayar da fifiko ga wanda buqata ta yi wa zoba, ta hanyar nema masa mafificiyar mafita. Akwai dalilai da dama da ke iya tabbatar da wannan magana. Amma ga kaxan da ga cikin su: • Zavar wa matansa Sallallahu Alaihi Wasallama yanayi mafi sauqi daya ya yi a lokacin Hajji ta hanyar umurninsu da aje Harami. Kamar yadda hadisin Sayyida Hafsatu Allah ya yarda da ita ke tabbatarwa, cewa: “Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya umurci matansa da aje Harami a lokacin Hajjin bankwana” (SDB:4398) • Sai kuma ware masu rauni daga cikin iyalin nasa da ya yi Sallallahu Alaihi Wasallama a lokacin da za a bar muzdalifa, ya turo su kafin kowa. Kamar yadda ya zo a cikin hadisin Falalu xan Abbas Allah ya yarda da su wanda ya ce: “Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya umurci masu rauni daga cikin banu Hashim da su baro tun cikin dare, kafin sauran mutane” (SM: 3034/SHA: 2340/SB: 1678). • Bayan wannan kuma sayyida Aisha Allah ya qara mata yarda ta ce: “Da muka isa muzdalifa, sai uwar muminai Saudatu Allah ya yarda da ita ta nemi iznin annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kan ta gabata kafin sauran mutane su danno. Saboda kasancewarta mace mai nauyin jiki. Sai ya bata dama Sallallahu Alaihi Wasallama ta xan riga sauran jama’a tasowa. Mu kuwa, muka jira har sai da gari ya waye. Sannan muka taso tare da shi” (SB: 1681). Sai kuma hadisin Sauban, wanda ya ce: ya shiga wurin uwar muminai Ummu Habiba Allah ya yarda da ita bayan ta qaraso, sai ta ba shi labarin cewa ai, annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya haxa ta da wasu ne suka taso tun da dare kafin sauran mutane” (SM: 1272) • Sai kuma umurcin da ya ba matarsa Sallallahu Alaihi Wasallama wato: Ummu Salama Allah ya yarda da ita a lokacin da ta koka masa cewa fa ita, tana jin jiki. Sai ya ce mata: “To ai kiyi naki xawafin nesa ga mutane kuma a kan abin hawa (SB: 464). Haka kuma ya ba amminsa Abbas xan Abdul Muxxalabi Allah ya yarda da shi izinin ci gaba da kasancewa a garin makka tsawon kwanaki da ya kamata a ce ya yi a mina. Domin hakan ta ba shi damar shayar da mutane ruwa cikin sauqi” (SB: 1634) Duk da yake alhazzan da ke tare da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a wannan lokaci, yawansu bai taka kara ya karya ba, idan aka yi la’akari da irin xinbin mutane da ke zuwa Aikin Hajji a yau, amma kuma dluk da haka su ne mafiya qarfin imani da xaukaka da natsuwa a cikin wannan al’umma. Amma kuma tattare da waxannan siffofin annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya tausaya wa iyalinsa daga cikinsu ya yi masu irin wannan sassafci. To idan kuwa har Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama zai yi haka a wancan lokaci, lalle kuwa buqatar da masu manyan shekaru da mata da qananan yara su ke da ita zuwa ga tunatarwa da sawwaqa al’amurra, a wannan zamani namu ta zarce ta waxancan. Domin matsayin ba xaya ba. Kuma ko shakka babu ya kamata a kula da su matuqa. Domin kuwa qaruwar yawan alhazzai a wannan zamani bai daxa su da komai ba, sai qaruwar jahilci, domin mafi yawansu imani da tsoron Allansu bai taka kara ya karya ba balle a yi zaton samun wani tausayi daga gare su zuwa ga takwarorinsu alhazai. Saboda haka yana da kyau matuqa mutum ya kula da iyalinsa. Ta hanyar sauqaqa masu al’amurra ko da yaushe, da zavar masu abin da ya fi dacewa da su a fagen hukunce hukuncen shari’a da a dokokinta. Domin kuwa haka shi ne mafi alheri ga mutum, da qara bunqasa rumbum ladarsa. 3.9 Sannan Ya Nuna Haquri da su Bayar da misalai waxanda za su iya tabbatar da kasancewar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama mai haquri da iyalinsa a wannan lokaci na Aikin Hajji abu ne da ba sai an kai ruwa rana ba, ko sai an wani dogon tunani ko zuzzurfan batun zuci. Dalili kuwa, ba su da wani malami kuma a lokaci xaya mai kula da al’amurransu sai shi. Ka kuwa san duk wanda irin wannan nauyi ya hau kansa dole ne ya zama damo sarkin haquri; Ko kuma a yi ba tulu ba ruwan daxi. Musamman idan aka yi la’akari da kasancewar akwai masu manyan shekaru da nauyin jimi a cikin iyalin nasa Sallallahu Alaihi Wasallama kamar uwar muminai Saudatu (SB: 1681). Akwai kuma marasa lafiya, da ke fama da laulayi kamar Dhuba’atu (SB: 5089) da kuma Salmatu (SB; 464) Akwai kuma mata da yawa kamar ‘yarsa Faximatu (SM: 1218). Ga kuma gaba xayan sauran matansa Sallallahu Alaihi Wasallama (ZM: 2./106/SN: 4/222). Ga kuma matasan ‘yan gidan Abdul Muxxalabi da ‘yan gidan Hashimu (MA: 3013). Kai ka san duk wanda bai kai gwarzo a fagen haquri ba, ba zai iya rungume wannan taron jama’a ba. Amma sai ga shi Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya iya da su ta hanyar wani irin haquri da dauriya irin waxanda ba a tava gani ba. A lokaci xaya shi ne malaminsu, jagoransu (SM: 1211/MA: 26590) Shi ne kuma inuwarsu wurin hutawa, kuma uwa mai maganin kukan xanta (SB: 4398, 1678). Shi ne mai sa ido akan su a cikin tausayawa da kyautatawa. (SB: 1788/SM: 1211) Shi ne kuma mai xebe masu kewa a cikin raha da nashaxi (SA: 2507) da kiyaye haqqoqansu daga tozarta (SB: 1636). Shi ne kuma mai qarfafa guiwarsu a kan aikata ayyukan alheri (SM: 1218). Da waxannan siffofi ne da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya haxa, ya ci nasarar jagorancin wannan tawaga ta iyalansa a cikin hikima da basira da nuna qwarewa a fagen tarbiyya da dashen zukatan alheri duk, a cikin natsuwa da kwanciyar hankali. Ba tare da da xai rana an ji wani ya koka da shi ba daga cikinsu . Wai!....ina ma dai ace tarihi zai maimaita kansa? A samu wani nagartaccen shugaba ya kwatanta irin waxannan halaye da xabi’u na Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama , waxanda ya bar mana a cikin tarihi. Waxanda kuma sai mutum mai cikakkiyar himma da tsarkin zuciya ke iya aiwatarwa. Ko shakka babu haquri da iyali wani aiki ne mai matuqar wuya da girma, da sai waxanda Allah Subhanahu Wa Ta’ala ya zava daga cikin mazaje ke iya xauka. Domin kuwa ga al’ada ido ya raina wanda yake gani kullum. Saboda haka lalle ne sai mutun ya qara dauriya da haquri, kafin ya iya gudanar da jagoranci yadda ya kamata, kwalliya ta biya kuxin sabulu. Masamman irin lokacin Aikin Hajji, wanda kamar kogi da ruwa yake keta shi sai an shirya. Saboda haka, lalle ne duk wanda ke son lada da tsira gobe qiyama, ya koya ma rayuwarsa haquri na gaske, tsakaninsa da iyalinsa da sauran makusanta. Ta haka sai ya karva sunan shugaba, kuma alkadarinsa ya xaukaka. Kamar yadda Allah Subhanahu Wata’ala Ya ce: “Kuma mun sanya shugabanni daga cikin su, suna shiyarwa da umurninmu, a lokacin da suka yi haquri kuma sun kasance suna yin yaqini da ayoyinmu (32: 24) Bayan wannan kuma, da haquri ne ake samun qauna da so daga wurin Allah har ma da agaji. Kamar yadda Subhanahu Wa Ta’ala Ya ce: “Kuma Allah Yana son masu haquri” (3: 153) A wata ayar kuma Subhanahu Wa Ta’ala Ya ce: “Lalle ne Allah na tare da masu haquri “ (2: 153) To ba a wurin Allah Subhanahu Wa Ta’ala kawai ba, duk da mutane, suna matuqar son mutum mai haquri, suna kuma yarda da jagorancinsa. 3.10 Manzon Allah Yana Rarrashin Iyalinsa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama na matuqar ji da iyalansa kamar yadda uwa ta ke ji da xan qaramin xanta, ko fiye da haka. Shi ya sa ba ya qaunar ganin abin da zai cuta masu. Ba abin da yake qoqarin yi Sallallahu Alaihi Wasallama ko da yaushe, sai ya yi abin da zai daxaxa masu rayuwa, matuqar hakan ba zai sava wa Allah Subhanahu Wa Ta’ala ba. Ya kan xauki wannan mataki ne Sallallahu Alaihi Wasallama idan abu ya wakana savanin yadda xaya daga cikin iyalan nasa ke fata. A nan sai ya sanya rarrashi da lele a matsayin wata hanya ta magance al’amarin. Haka Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kasance da iyalansa musamman a lokacin Aikin Hajji. Misalin wannan shi ne lokacin da matarsa, sayyida Aisha Allah ya qara mata yarda ta shiga wani hali na damuwa. Inda ya same ta tana kuka. Saboda an hana ta haxa haramai biyu (na Hajji da na Umra) kamar yadda sauran matansa suka yi, saboda wanki da ya kama ta. Sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ganin haka, ya shiga rarrashin ta yana cewa: haba yi haquri! Wannan ba zai cuce ki da komai ba. Abu ne da Allah Ya hukunta ga bayinsa mata, ba ke kaxai ba. Ki wadatu da Hajjinki, ya ishe ki. Sai Allah ya ba ki ladar Umra saboda niyyarki” (SB: 1788/SM: 1211). Amma ina! Aisha Allah ya yarda da ita sai ta kafe saboda quruciya, tana mai cewa: “Ya Manzon Allah, ba komai ke damu na ba, sai in na tuna ‘yan ‘uwana (tana nufin abokan zamanta, sauran matan manzon Allah) duk za su koma gida, da Hajji da Umra. Ni ko Hajji kawai zan koma da shi. Jin haka fa sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya fahimci lalle Aisha Allah ya yarda da ita ba ta xauki wannan matsala da sauqi ba. Don haka sai ya umurci yayanta Abdullahi xan Abubakar Allah ya yarda da shi da ya tafi da ita a can kan iyakar haramin Makka a wani wuri da ake kira “Tan’im” don ta sabunta haramarta da Umra. Shi kenan sai a huta” (SB: 1561/SM: 1211/SAD: 1782). A wata riwaya kuma aka ce, ce mata ya yi “Dawafin nan naki na Hajji ya haxa har da Umra” amma ta kasa fahimta. A qarshe sai ya haxa ta da yayanta don ta yo sabuwar haramar Umra” (SM: 1211) Allahu Akbar! Ka ji irin yadda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ke yi da iyalinsa. Amma mafi yawan mutane a wannan zamani ko dai ka sami sun wuce wurin. Ta yadda har iyalin nasu sun sukur-kurce. Ko kuma sun kasa, matuqar kasawa. A taqaice dai magidanta sun rabu zuwa qungiyoyi biyu: Qungiya ta farko, ita ce ta magidantan da suka fifita buqatun iyalansu a kan dokokin Allah Ta’ala. Sai aka wayi gari iyalan nasu suna keta dokokin Allah, da biyar son zuciya. Qungiya ta biyu kuwa, ita ce ta magidantan da, saboda tsananin rashin sanin girman Allah da dokokinsa, suke zamar wa iyalansu kamar dodanni. Su ne kullum xaure da fuska tanke da mara. A littafin rayuwarsu babu babin sassafci balle na ba ni gishiri in ba ka manda (Ina nufin musayar ra’ayi da neman fahimtar juna). Babu wani abu da ke sa su xan tattauna da iyalansu, balle har su xan shawarce su ko da wata rana. Ko su xan yi raha da su, ko rarrashi da lele. Babu abin da ke tsakaninsu, sai bayar da umurni ko hani, cikin kakkausar murya kamar sojoji, ba wata saurarawa ko nisawa balle karvar uzuri. Alhali kuwa addinin Allah, abu ne da ke son tsakaitawa, kada a wuce wuri kar kuma a kasa. Yana kuma matuqar kwaxaitarwa da kira zuwa ga kula da iyali da rarrashinsu a inda hakan ya cancanta. Matuqar haka ba za ta kai ga sava wa Allah Subhanahu Wa Ta’ala ba. To abu ne mai kyau, da kuma ya kamata ko wane musulmi ya tsare idan yana fatar samun tsira da babban rabo.
Posted on: Tue, 22 Oct 2013 16:48:58 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015