A CIKIN FALALAR IMANI:- Annabi (S.A.W) ya ce: Imani sani ne a - TopicsExpress



          

A CIKIN FALALAR IMANI:- Annabi (S.A.W) ya ce: Imani sani ne a zuciya, fadi ne a baki kuma Aikine da gabobi.Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Imani tsaraici yake tufafin sa tsoro Allah, Adonsa kunya, dan Itaciyarsa shi ne ilimi. Manzon Allah (S.A.W) ya ce babu Imani ga wanda babu Amana a tare da shi. Manzon Allah(S.A.W) ya ce: Dayanku bai yi Imani ba har sai ya so wa dan uwansa abinda ya ke sowa kansa. Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Imani a cikin kirjin mumini yake, kuma Imani baya cika sai da cikar farillai da sunnoni, ka nan Imani baya bacci da musanta farillai da sunnoni. Duk wanda ya tauye farillai guda daya ba tare da yana musanta ba za ayi masa azaba a kanta. Wanda ya cika farillai Aljanna ta wajaba a gareshi. Manzon Allah ( S.A.W) ya ce: Imani baya karuwa baya raguwa, amma yana da Iyaka-wato rassa Imani wanda yatauye to daga rassa ne.Amma asalinsa fadar: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. Shi kadai bashi da abokin tarayya, kuma Annabi Muhammadu Bawansa ne Manzonsa ne da tsarda salla da bada zakka da azumin Ramadan da Hajji da kuma wankan janaba ga kowana muminia. Wanda ya kara cikin iyakarsa sai kyawawan ayyukansa su karu, wanda ya tauye da cikin iyakar to a cikin rassa ya tauye. Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Imani tsagi biyu ne. Rabi yana ciki Hakuri, daya Rabin yana cikin godiya ga Allah. Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Imani shine Katanga ga barin kisa. Mumini baya kisa. Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Allah ya halicci Imani ya kawata shi, ya kuma yabe shi da rangwame da kunya. Haka ma ya halicci kafirci ya zargeshi da rowa da sabo. Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Idan yan Aljanna suka shiga Aljanna, yan wuta suka shiga wuta, Allah zai yi umarni wanda a zuciyarsa akwai gwargwaado kwayar zarra na imani ya fita Daga wuta..
Posted on: Wed, 27 Nov 2013 19:11:50 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015