A.P.C. Canji! A.P.C. Canji!! A.P.C. Canji!!! - TopicsExpress



          

A.P.C. Canji! A.P.C. Canji!! A.P.C. Canji!!! Salamu Alaikum, yan’uwana yan jamm’iyyar A. P. C. canji. TAKARDAR TSOKACI DA FADAKARWA GA SHUGABANNI DA ‘YAN JAM’IYYAR A.P.C. (CANJI) NA JAIHAR KANO DA KASA BAKI DAYA. Gabatarwa: Bayan gaisuwa da girmamawa. Ina mai farin cikin yin tsokaci da fadakarwa akan al’amuran siyasa ta demokradiyya da hanyoyin da jam’iyyar A.P.C zata samu daukaka a Jihar Kano da kasa baki daya, kuma a samu nasarar cin zabe (insha’Allah) cikin sauki da fizge mulki ta yin amfani da kuri’un mu daga hannun ‘yan jari hujja wadanda basa kishin kasa da talakawa sai kishin kansu. Wadanda suka assasa talauci, jahilci, cin hanci da rashawa da kuma tabarbarewar tattalin arziki, rashin wutar lantarki, rashin aikin yi musamman ga matasa, da tabarbarewar kiwon lafiya, da yajin aikin malaman jami’o’i da sauran manyan makarantu na kasa da likitoci a asibitocin Nijeriya. Haka kuma akwai tabarbarewa da lalacewar hanyoyi da sauran al’amuran da suka shafi gwamnati da manyan kamfanoni, wanda suke da dangantaka da muhimmanci a tattalin arzikin kasa da al’ummarta. Sanin wadannan abubuwan da muka ambata, shi ya sabbaba ‘yan Najeriya masu kishin kasa dasu samo hanya wacce zata kawo canji mai albarka domin gyara al’amuran Najeriya gaba daya, yadda ‘yan kasa zasu samu salama a rayuwarsu. Wannan shi ya haifar da kafa jami’iyyar A.P.C. mai farin jini mai albarka domin kawo canji a tafiyar da mulkin Najeriya. Saboda haka annan ya zama wajibi muyi kira ga duk yan jam’iyyar A. P. C. da muyi kokari mu fito gaba dayanmu da iyalinmu da yan’uwanmu da duk wanda zamu fadawa yaji don mu yanki rajistar jam’iyya da zarar anfara a jihar Kano da kasa baki daya. Wannan shine kadai mafita da za’a kawo canji a mulkin jihar Kano da Nijerya gaba daya. Siyasa: Siyasa tana da ma’anoni da yawa, amma mafi shahara shine tafiyar da mulkin al’ummma dangane da abinda ya shafi tattalin arziki, rayuwar yau da kullun da kuma zamantakewa tsakanin yan kasa. Kuma yana daga ma’anar Siyasa, aiwatar da abinda al’umma suke so ko suke da bukata. Siyasa tana da shika-shikai (da dangogi) guda uku;------------ 1. Tsare daraja,---- kima da mutunci da addini da dabi’u da al’adu da iyali da muhalli da sauransu 2. Bukata----- wacce ta shafi tattalin arziki, zamantakewa, dangantaka ta al’umma kamar kasa da kasa, ko gari da gari, ko kabila da kabila, zaman lafiya da sauransu 3. Cimma buri----- kamar yadda kowa ya sani, dan adam baya rabo da buri a rayuwa. Amma cimma buri a rayuwar dan adam ya dogara da damar da ya samu ta shugabanci a siyasa na yadda zai aiwatar da bukatu na al’ummar da yake shugabanta. Saboda haka ya zama wajibi ga mu ‘yan jami’yyar A.P.C. mai albarka mu tashi tsaye, mu canja yadda ake tafi da yanayin siyasar kasar nan. Ina matasa? Ina mata iyayen giji? Ya kamata ku tashi tsaye kuyi fafutuka ta yadda za’a tabbatar da zaben jam’iyyar A.P.C. ta hanyar tabbatar da yin zabe na adalci (a kasa, a tsare a raka a tabbatar da an fadi sakamako na gaskiya) a Jihar Kano da kasa baki daya. Wannan shi kadai zai tabbatar da kaucewa “jiki magayi”. Saboda ya zama wajibi a kawo canji a siyasa da tattalin arziki da zamantakewa a Jihar Kano da kasa baki daya, amma a sani wannan duka ba zai yiwu ba sai an samu hadin kai, kaunar juna, adalci, kamanta gaskiya, fahimtar juna, sadaukar da kai, kawar da son zuciya da kuma zaben shugabanni na gari acikin jam’iyyar A.P.C. wadanda zasu tabbatar da abubuwan da aka ambata a sama. Kuma duka wadannan abubuwa zasu samu ne idan aka dora komai a kan mizani na tsari, da lakanin Siyasa da kuma baiwa ‘yan jam’iyya hakki da dama na mu zabi shugabanni wadanda zasu wakilce mu a dukkanin al’amura na tafiyar da siyasar demokradiyya a kasa baki daya. Demokradiyya: Siyasar demokradiyya tsari ne wanda yake baiwa al’umma dama na su zabi shugabannin da zasu tafi da al’amuransu da kuma wakiltar su acikin tafiyar da mulkin Siyasa, tattalin arziki da zamantakewar al’umma. Kuma tsari ne wanda yake bada dama na yanda al’umma zasu sami cigaba a kasa. Tsarin demokradiyya yana da shika-shikai kimanin talatin da uku (33) wadanda suka hada da; shigar al’umma (umuman) wajen tafiyar da demokradiyya, fadin albarkacin baki, tsarin bin doka da oda, kafa jam’iyyu, kafa kungiyoyi, rubuta tsarin mulki, baiwa kowane dan kasa damar ya zaba ko a zabe shi, amfani da kudi ta hanyar da doka ta tanada, alkintawa da inganta tattalin kudi na jam’iyya, sauraron muryar marasa rinjaye ko bukatunsu, tattalin arziki, zamantakewa, kafa gawamnati, yin adawa mai ma’ana, ‘yancin dan adam, baiwa kowane dan kasa dama ta watayawa, mulkar al’umma, al’amuran al’umma, wakilci, shari’a ta adalci, dokoki, babu tilastawa ko yin amfani da karfi, gina hukumomi, mujadala, yin yarjejeniya, daidaito da sasantawa, akida da tsara manufofi, damar zabi da ‘yanci na yin addini, zabin ra’ayi na sassauci ko kuma ra’ayi na ‘yan mazan jiya, mafiya yawa da rinjaye su suke da fada a ji, kyautatawa, kuma demokradiyya tsari ne wanda shugabanni masu gogewa ta fannin ilimi da aikin gwamnati da iya tsari na shugabanci suke wucewa gaba don tafi da mulkin al’umma. Duk wadannan abubuwan da muka ambata na ginshikan demokradiyya baza su tabbata ba sai jamm’iyyar mu mai albarka ta A.P.C. ta bada dama an zabi shugabanni na gari ta hanyar yin tsarin demokradiyya a cikin Gidan jamm’iyyar A.P.C. Yin hakan zai tabbatar da nasarar jamm’iyyar A.P.C. (Insha’Allah), a Jihar Kano da kasa baki daya. Allah (SWT) ya bamu sa’a, nasara da dacewa, amin. Fadakarwa: A nan muna kira ga shugabannin mu da magoya bayan jam’iyyar A.P.C. Canji da su fadakar da al’ummar Jihar Kano da kasa baki daya, manufofi, akidu da kudurori na kawo canji mai albarka wanda za’a samu salama da aminci a rayuwar al’ummar Jihar Kano da kasa baki daya. Ma’ana manufofin jam’iyyar A.P.C. da zata aiwatar---kamar yin shugabanci na gari kuma mai inganci kuma mai cike da adalci, bada ilimi mai nagarta kyauta ga ‘yan Najeriya, tabbatar da tsayuwar wutar lantarki awa 24 a kowane sashe na Najeriya a cikin shekaru hudu zuwa takwas, kawar da cin hanci da rashawa, tabbatar da da’a da bin doka da oda a kasa, bayar da magani tare da kiwon lafia kyauta ga yara da tsofaffi da mata, inganta tattalin arzikin Najeriya da ‘yan kasa, inganta aikin gona da tsarin baiwa matasa aikin yi mai inganci da nagarta, tabbatar da tsaro a kasa da kawar da satar danyen mai da sauran sace-sace, gina hanyoyi na birane da karkara, samar da ruwan sha mai nagarta da baiwa dattawa ‘yan Najeriya (wadanda suke da bukatar tallafin gwamnatin tarayya) suka haura shekaru sittin (60) zuwa sama alawus duk wata don rage radadin rayuwa da inganta tattalin arzikin kasa a cikin gida. Kuma da dawo da kima, daraja da martabar Najeriya da ‘yan Najeriya a idon kasashen duniya. Daga karshe ina kira ga ’yan uwana ‘yan jam’iyyar A.P.C. Canji da mu zabi shugabanni na gari masu kamanta gaskiya da adalci wadanda zasu tabbatar da girma da mutunci da kima na jam’iyya da ‘yan jam’iyya. Kuma abu mafi muhimmanci shine mu dage da addu’a Allah (S.W.T) ya bamu nasara da dacewa na kawo canji mai albarka a Jihar Kano da Najeriya!. Naku, dan’uwanku, mai kaunarku, kuma mai biyayaya ga shugabanni. Hon. Abbati Bako, (mti,psc,bsis, UK) Political Strategist SAKO DAGA ABBATI BAKO ORGANIZATION ZUWA GA YAN’JAMIYYA.
Posted on: Sat, 14 Sep 2013 20:39:49 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015