A ZO KUDUS YADDA YA KAMATA IN JI SAYYID ZAKZAKY Mai karatu wannan - TopicsExpress



          

A ZO KUDUS YADDA YA KAMATA IN JI SAYYID ZAKZAKY Mai karatu wannan sakon Sayyid Ibraheem Yaqoub Zakzaky ne dangane da makircin da aka kulla kan shirin al’ummar musulmi na muzaharar Ranar Kudus da za a yi gobe a manyan biranen Kasar nan, kamar yadda za a yi kuma a sauran biranen kasashen duniya. Ya yi wannan bayanin ne a karshen Tafsir na Alkur’ani mai girma ranar Talatar da ta gabata a Husainiyya Bakiyyatullah Zariya. Ibrahim Musa ne ya rubuta daga shafin yourlisten bangaren iakilu. Jaridar ALMIZAN ta gobe ta zo da wannan bayanin ita ma. Don haka a tarbe ta. DAREN LAILATUL KADRI BAN san ranar da za mu gama tafsirin nan ba. Da na so yau mu yi wannan (Suratu Nasr), mu yi kuma Tabbat yada, gobe sai mu yi kuma Kulhuwa da Kula’uzai. Mun sauke Alkur’ani ke nan. Kuma da yake muna da sauran kwanaki a Ramadan din, sai mu faro kuma daga farko. Sai mu yi Fatiha, mu shiga Bakara. Ko ko a ajiye ne a huta kawai? A gabanmu akwai dare muhimmi, wanda ya fi kowane dare muhimmanci a cikin dararen Ramadan, daren 23, wanda ya kamata a yi ta magiya zuwa ga Allah. Ya fi kowanne daga cikin dararen. Shi aka fi kyautata zaton ya kasance daren Lailatul Kadri. Saboda haka kar a yi sake. Ayyuka ma’asurai ga su nan rututu. Baya ga raka’o’i dari da addu’o’insu, akwai kuma addu’o’i daban-daban. Akwai Jaushin, ana so a karanta. Akwai kuma wadansu addu’o’i daban-daban. In mutum ya duba Mafatihul Jinan zai ga addu’o’i daban-daban ma’asurai da kuma wannan aikin sanya Alkur’ani din nan a ka da tawassuli da Allah da Ma’asumai, alhali Alkur’ani yana kan mutum, sannan kuma dai da addu’o’i daban-daban. A TAIMAKA MANA DA ADDU’A Kuma kar a manta a taimaka mana da addu’a a kan azzalumai. Mutanen nan suna ban mamaki kwarai da gaske. Su ba su da wani tunani a zuciyarsu illa za su yi kisan kai. Shi ke nan la gairu. Na ce, to ku wadannan tunanin ya dode ne, ba wani abin da za ku iya yi ne banda ku yi kisan kai kawai? In ba a manta ba, lokaci ya wannan bara, nake mana bayanin cewa a yi addu’a don mutanen nan sun shirya in ana Kudus za su sa bama-bamai a motoci a gefen hanya ya tashi, kuma har da addade musu adadin motocin, da ma na so sai in gaya musu na su wane suka sata kuma a ina. Da suka ji wannan, sun yi taraju’i. Sai daga baya aka ba da sanarwa cewa wadanda aka sace musu motoci, to yanzu Kwastam sun kama su. Sai aka ba mutane motocinsu daga baya. Ba su ta da bom din ba. To, amma shekara hudu da suka wuce sun yi niyyan za su kawo hari a kan taron Kudus na Zariya, kuma duk mun fadi ga shi abin da suke shirin yi. Har ma aka fada a wadansu kafafen watsa labaru, tashoshin talabijin da ake kamawa a duniya daban-daban da gidajen rediyo, duk suka yada cewa ana yunkurin kai hari a taron Kudus na Zariya, za a bude musu wuta. Har ma ana gobe za a yi Kudus, muka sami tabbacin sun sami sabani a tsakanin jami’an tsaro din, har wasu suka ce ba za su taba yarda a yi wannan ba. To, amma da safe shi Kwamandansu mai baki kamar jaba, sai ya tattara wasu suka bude wuta. Shi ya dauka ran nan za a yi kisan zubargada ne, kuma daga nan ma su wuce Gyallesu. Shi ke nan Allah (T) ya tsai da abin, sun kashe mutum biyu – Abdurrahman Isa da Isa Muhammad. Kuma sun ji wa wani dan uwa Tsalha rauni wanda har yanzu bai mike ba, don sun kwantar da shi ne suka hahharbe shi a kafa, har yanzu bai sami kafar ba. SHIRINSU NA JUMA’AR FARKO YA GAZA Yanzu kuma muna da labari bayan yunkurin da suka yi a Juma’ar farko, suka tsattsara za su bude wuta a kan al’umman Tudun wadan Kaduna, su yi kisan kan mai-uwa-da-wabi, bayan sun bindige wani Shehin Tijjaniyya, wanda za su fake da cewa ana rigima ne tsakanin Shi’a da Tijjaniyya, daga nan kuma su yi barin wuta a kan al’ummar musulmi, ba tare da la’akari da ko kai dan meye ba. To, Allah (T) kuma mai rufe idanunsu, sai ya rufe musu idanunsu ba su san cewa duk mun san abin ba. Mun san shirin da wa zai yi da a ina ya tsaya. In muka so muna iya gaya muku, ina kuka ajiye rundunoninku, su wane ne, motan nawa kuka ajiye a daidai gidan mai, mota nawa kuka ajiye a gidan Alhaji Wane, mota nawa kuka aje kusa da kasuwar Barci? Duk mun san abin da kuka shirya. Mutum nawa kuka dora a kan masallaci suka kwakkwanta da bindigogi? Duk wannan bai yiwu ba da Allah (T) ya tarwatsa shirinsu. Sai suka je suka yi mitin, yanzu haushin da suka ji, sai sun fanshe hushinsu kan Kudus na Zariya. Saboda haka dabarar da za a yi shi ne za a ta da bom ne, daga nan sai a ce to ba fita. Na ce, to ai ba ku yi dabara ba ma, in kuka ce za ku ta da bom ku hana kowa zirga-zirga, ku hana Kudus. In kuka hana Kudus, duk ba ku ce komai ba, muna yin Kudus a birni 22 ne. To, in tana iya yiwuwa ku hana birni daya ko biyu, kun yi mene? In an yi a birni 20 sai me? Ko yanzu ma akwai wasu wuraren da suka aiko mana cewa saboda yanayi ba za su iya yi ba, amma idan aka yi a wurin da ya yiwu sai me? Ba dai an yi ba? Kudus ana yi a ko’ina a duniya, kuma za a yi a Nijeriya. A NUNA MUSU BA SU ISA BA Kuma lalle a nuna musu cewa ba su isa ba. A zo Kudus yadda ya kamata! Ya rage musu, wadannan mutane miyagu, hasararru, tababbun duniya da lahira. Ba ku iya komai ba sai za ku yi kisan kai. Shi ke nan abin da za ku iya. In kuna kaunar Isra’ila, da take kada ku kamar dabbobi, ku yi taron goyon bayan Isra’ila mana. Muna goyon bayan Palasdinu; to ku yi taronku na magoya bayan Isra’ila, in kun isa? Ku tattaro mutane magoya bayan Isra’ila, ku daddaga tuta ku ce Isra’ila muke goyon baya. Ba za mu ce muku ku ci kanku ba. ’Yanci ne kowa yana da nasa. Ya rage musu. Amma yanzu insha Allah wannan dare kar a manta da addu’a, Allah (T) masu nufin mu da sharri, Allah ya mai da musu da sharrinsu a kawukansu. Shi ke nan addu’ar a kullum. Ba muna cewa shi mutum za mu je mu dirar masa ba ne, a’a ya shirya sharrin, amma Allah ya sa shi zai fada ciki! Wasallallahu ala Muhammaddin wa alihid dahirin. Upload Audio, Listen and Download Music - Yourlisten YourListen an audio website where users can upload, listen, share, download, search, embed and discuss audio files which consist of podcasts, interviews, sound bites, sound effects, ringtones, audio books and music. YOURLISTEN.COM
Posted on: Thu, 01 Aug 2013 12:15:45 +0000

Trending Topics



a>
UNUDARDIM.. ( Vahid Eziz ) Oldur meni, neyniremse
His Holiness the Gyalwang Drukpa, Their Eminences Drukpa Yongdzin
Dear friends travelling via Tunis , As we are on transit in Tunis,

Recently Viewed Topics




© 2015