A karo na biyu na saurari shirin Sharia Garkuwa wanda wasu Manyan - TopicsExpress



          

A karo na biyu na saurari shirin Sharia Garkuwa wanda wasu Manyan Lauyoyi ke gabatarwa a gidan Rediyon Freedom, kuma ake yada shi kai tsaye duk ranar Jumuah. Abu biyu da suka janyo hankali a shirin da ya gabata shine irin Kama-karyar da wasu masu gabatar da kara (Prosecutors) ke yi a kotunan mu. Wata saar zaka ga shine mai juya Alkali sai abinda yake so ayi a sharia zaayi, wanda hakan nasa a daure mai gaskiya ko a sallami mai laifi. Na biyu, rashin kwarewar aiki ga wasu daga cikin Maaikatan kotuna. Hakan na haifar da nakasu a harkokin sharia. Don haka ina kira ga Shugabannin Kungiyar Maaikatan kotuna da lallai su dauki gabaren shiryawa Membobin su bitoci akai akai domin zaburar da su wajen tunkarar kalubalen da suke fuskanta. Alkalan mu kuma su rika kokarin kamanta adalci. Allah yasa mu dace.
Posted on: Sat, 09 Nov 2013 12:45:33 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015