A kullum sai kaji ‘yan’uwa musulmai muna cewa Allah kawo mana - TopicsExpress



          

A kullum sai kaji ‘yan’uwa musulmai muna cewa Allah kawo mana zaman lafiya…. Via Usman Yakasai Ali Barkun Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un. Ta yaya Allah zai sauraremu bayan munki bin dokokinsa? Shari’ar da annabi(saw) ya barmu akai mun kauce mata, Allah(swt) yace: ‘MASU TSABAWA WA UMARNIN MANZON ALLAH SUJI TSORON KADA WATA MUSIBA TA SAMESU KO AZABA MAI RADADI’ Allah yayi gaskiya gashi muna kan ganin musiba kala kala. Bala’I iri iri. Ana kashemu kaman kiyashi amma babu wadda zai tashi ya tsaya a madadinmu. Ana kama mana malami ana tsaresu amma mun kasa daukar mataki, ana kisan muminai ba laifi amma mun kasa cewa komai…. Wannan wata irin rayuwa ce? Shin ‘yan’uwa kuyi tunani. wata gudumawa kuka baiwa addinin musulunci a rayuwarku? Ku tuna fa ba’a haliccemu domin muzo muyi wasa a duniya ba. An haliccemu ne domin muzo muyi bauta wa Allah… Allah yace :’BAN HALICCE MUTUM DA ALJAN BA FACE DON SU BAUTAMIN…’. Toh mu dubi rayuwarmu a yau shin bautan Allah mukeyi da gaske ko shirme? Mun kasa tsinana komai wa kanmu ‘yan’uwa mu tuba mu koma wa Allah. Ku dubi yadda muka mai da riba ta zamto halal. Wanda Allah(swt) yace : ‘INHAR BAKU BAR CIN RIBA BA TOH KU SHIRYA YAKI DA ALLAH’ Shin meyasa bazamu hada kai mu kafa bankin musulunci ba? Bamu da masu kudi ne da zasu taimaka? Ko bamu da masu ilmi ne da zasu gudanar da harkokin bankin? Duka muna dasu. Kuje ku dubi jami’oi kuga yadda ake lalata acikinsu. Hazbunallah Yaa ku mazinata wallahi ku tuba. Yaa ku ‘yan luwadi wallahi ku tuba. Yaa ku maciya riba wallahi ku tuba. Yaa ku maciya amana wallahi ku tuba. Yaa ku ‘yan ta’adda wallahi ku tuba. Yaa ku masu bid’ah wallahi ku tuba. Yaa ku ‘yan tsubbu wallahi ku tuba. Yaa ku masu aiki da shari’ar da bata Allah ba, wallahi ku tuba. Yaa ku azzaluman shuwagabanni wallahi ku tuba. Yaa ku mashaya giya da sauran kayan maye wallahi ku tuba. Yaa ku munafukai wallahi ku tuba. Yaa ku maciya rashawa wallahi ku tuba… Wallahi babu wata lokaci da ta rage mana. Tashin Alqiyaama ta kusa, indama kun mike kafa ne, ku nade ta ku tashi kuyi wa addinin Allah aiki. Domin mu tsira tare….. Allah ya taimaki musulunci. Allah ya nuna mana gaskiya ya bamu daman binta. Ya nuna mana karya ya bamu daman kauce mata….
Posted on: Mon, 21 Oct 2013 09:04:50 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015