ABIN DA AKE SO KA AIKATA LOKACIN DA AKA ZO MAKA DA - TopicsExpress



          

ABIN DA AKE SO KA AIKATA LOKACIN DA AKA ZO MAKA DA GULMA:- Akwai Abubuwa Da Dama Da Akeso Ka Aikata Lokacin Da Wani Ya Zo Maka Da Gulma, Kadan Daga Ciki Sune:- *1. Kada Ka Gaskata Labarin Da Aka Zo Maka, Domin Wanda Ya Zo Da Labarin Ya Zama Annamimi, Fasiki, Kuma Mai Mayar Da Alheri. *2. Ka Hana Wanda Ya Kawo Maka Gulmar Cigaba Da Gulmar, Kuma Kayi Masa Nasiha Sannan Ka Kyamaci Aikata Hakan. *3. Ka Nuna Masa Kaji Haushinsa Domin ALLAH, Don ALLAH Yana Fushi Da Aikinsa, Kuma Yin Fushi Domin ALLAH Wajibi Ne. *4. Kada Kayi Mummunar Zato Dangane Ga Wanda Aka Kawo Maka Gulmarsa, Domin ALLAH(S.W.T) Yana Cewa:- KU NISANCI MAFI YAWA DAGA CIKN ZATO.. (Hujurat:12) *5. Kada Mutum Yace Zai Yi Bincike Don Gano Abinda Aka Fada Masa Karya Ce Ko Gaskiya Ne, Domin ALLAH (S.W.T) Yana Cewa:- Kuma Kada Kuyi Bincike.. (Hujurat:12). *6. Kada Mutun Ya Cigaba Da Labartarwa Da Wasu Abinda Aka Kawo Masa Na Gulma, Domin Shima Sai Ya Koma Matsayin Wanda Yazo Masa Da Gulman. YA ALLAH KA SANYAYA ZUCIYOYINMU MU ZAMA MASU JURE WAUTAR MASU WAUTA
Posted on: Fri, 29 Nov 2013 08:20:39 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015