ABIN MAMAKI DA ALAJABI..! MATASAN AREWA SUN BAWA JONATHAN - TopicsExpress



          

ABIN MAMAKI DA ALAJABI..! MATASAN AREWA SUN BAWA JONATHAN GUDUNMAWAR NAIRA MILIYAN BIYU DOMIN SIYAN FORM A 2015..! A jiya Asabar ne wata qungiya wadda take kiran kanta da Qungiyar Matasan Arewa ta gudanar da wani taro a Marhaba Sinima dake Kano, inda tayi gangamin hadawa Shugaba Mai Malafa Mijin yar lukuta kudi na siyan tikitin kuma neman takarar shugabancin qasar nan a 2015. Bello Bichi wanda shine yake kiran kansa da sunan shugaban qungiyar yabada gudunmawar kudi har naira miliyan biyu da sunan tallafin qungiyar, anasa jawabin dayake kar6ar tallafin kudin, Ministan Ilimi kuma tsohon gwamnan Kano wato Ibrahim Shekarau, yayi godiya da kuma nunajin dadinsa abisa wannan hubbasa na matasan arewar, kana yaqara da cewa, matasan su tabbata sunfito sun jajirce dan ganin Jonathan da PDP sunkai ga nasara axa6en dake gaf. Shugaban qungiyar yaqara da cewa, sundauki wannan matakin ne sbd yarda da ingancin Jonathan, da yadda salon mulkinsa yake gudana, yadda yake kula da mata da kuma matasa, dan haka xasuyi duk maiyiyuwa dan ganin jonathan din yakuma xarcewa aqasar nan! Taron dai yasamu halartar gabadayan ministoci ukun dake jahar ta kano qarqashin Ibrahim Shekarau ministan Ilimi. (Ikon Allah Kenan... Wannan fa shi ake kira HARBATA MATI..! A yan kwanakin bayan nan da suka wuce wata jarida dake qasar america ta fitar da rahotan cewa Jonathan shine shugaba na 6 ajerin shuwagabannin qasashen Africa masu kudi, kuma ana kyautata xaton idan har ya xarce to sai yakere saa, wato sai yaxamo na daya kenan, kuma ba kasuwanci yakeba, kawai da kudin qasar yake axurta kansa! Amma wai ahakan wasu suke yin gangami na tallafamasa da kudin da xai siyi form na takara, hmmmmn anbar jaki ana dukan tanki kenan..! Misali shi wannan daya kira kansa a matsayin shugaban Qungiyar Matasan Arewa, wanda kuma naga dan qaramar hukumar Bichi ne, ina da tabbacin a qaramar hukumarsa akwai Matasa masu hikima da basirar da sukeson yin karatu mai xurfi amma sbd babu dole sun haqura kuma suncire tsammani, banda talakawa mabuqata dake kwana da yunwa sbd tsananin Talauci, amma sbd son asani yahada taro yakira manema lbrai ya bada check din naira miliyan biyu abawa Mai Malafa! Oh!) Arewa da gyara... Qasarmu da gyara...! Ni dai Dan Arewa ne... Kuma xan iya shiga sahun Matasan Arewa, Dan haka ni dai bada yawuna ba gaskia... Kuma na barwa Allah... Sbd an6atamin suna! Ehee! Idan ka kama Freedom Radio yanxu - yanzu zakaji sun saka shirin. A.I.A
Posted on: Sun, 26 Oct 2014 10:41:09 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015