ABIN MAMAKI GA YAN’MATA Wani abin da ke yawan bani mamaki - TopicsExpress



          

ABIN MAMAKI GA YAN’MATA Wani abin da ke yawan bani mamaki game da yan matan wannan zamanin shine, yadda suka kware da sanin darajar rike babbar waya. Zaka ga mace rike da Blackbery Bold 5, Z10, Q10, Galaxy SII, SIII, SIIII, Iphone Phones etc, da sauran su kuma, Saboda da sanin darajar babbar wayar tasu, yasa zaka ga suna tattalata ta hanyar bata kariya sosai don gudun kar wani abu ya samu jikin wayar. Idan ka duba wayar zaka same ta cikin gidan da zai bata kariya (COVER) haka ma kan fuskar wayar lullu6e yake da wata ledar kariya (Screen Guard) hatta keypad ba a barin su haka sakaka da akwai garkuwa (Keypad Protector). Wai dukkan wadannan kariyar sunyi shine kawai don su saya wayar su kar wani abu ya same jikinta. Abin Ban Haushi, Abin takaici amma sai ka tarar da wasu daga cikin su, suna yawo kan titi kusan tsirara babu wani cikakken lullu6in da zai baiwa nasu jikin kariya. Kaga mace ta dinka dinki wanda dukkan sassan jikin ta komi waje. kaga mace tasa riga wadda rabin abinda ke a gabanta duk a waje suke, kaga mace tasa siket wanda ya matseta har kana ganin sharp din pant nata, kaga mace tasa wani dan karamin gyale sharara wata ma, ko gyalen batasawa. Kaga mace tasha wandon swager da mini shirt ta fito kan titi tana yawo. Abin tambaya shin wayoyin ku sun fi jikin na ku daraja kenan? Ko dai darajar jikin na ku a matsayin ku na Yaya matan ne baku sani ba har yanzu?? Allah (SWT) Yasa mu dace, ya kuma sa muci karfin zukatan mu, Allah kuma ya zaba mana mata na gari, suma matan ya zaba masu mazaje na gari. Via:Dandalin Auwal Yusuf Bauchi
Posted on: Mon, 04 Nov 2013 16:25:30 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015