ABIN #MAMAKIN DA YAFARU TSAKANIN WANI ARNE DA MUSULMI ALLAHU - TopicsExpress



          

ABIN #MAMAKIN DA YAFARU TSAKANIN WANI ARNE DA MUSULMI ALLAHU AKBAR Wani dan uwa musulmi ya samu aiki a cikin restaurant (gidan saida abinci) to kullum in zai shiga bandaki (bayi) sai ya nemo buta ya shiga da ita.. Akwai wani arne da suke aiki tare sai ya tambayeshi, "akan me kake shiga da buta bandaki? Sai musulmin nan yace "addinin mu ya koya mana hakan (mu wanke najasa bayan fitarta). Sai arnen nan ya sace "to me yasa ba zaka yi amfani da toilet paper ba (takardar da ake goge kashi ko fitsari kawai a fito waje)? Sai musulmin yace masa "Idan da ace wannannajasar zata taba maka hannu ba zaka goge da toilet paper ba wankewa zaka yi. Washe garin arnen nan ya dauki buta ya shiga bandaki da ita. Can sai ya fito daga bandakin yana kuka. Musulmin yace yaya haka?? Sai yace masa Ina rantse maka tunda aka haifeni ban taba jin tsafta ta samu jikina kamar wadda nayi yanzu ba. Daga nan sai ya karbi addinin Islam ya zama musulmi.. Allahu Akbar Allah ka kara daukaka addininka.
Posted on: Wed, 31 Jul 2013 18:14:03 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015