ALI (A.S) SHINE SHUGABAN DUKKAN MUMINAI A BAYANA INJI MANZON ALLAH - TopicsExpress



          

ALI (A.S) SHINE SHUGABAN DUKKAN MUMINAI A BAYANA INJI MANZON ALLAH (S) ` NA BIYU`~2~ ALLAHUMMA SALLI ALA MUHAMMAD WA ALI MUHAMMAD. A YAU ZAMUYI DUBI NE A TURA RUNDUNONI BIYU ZUWA YEMEN INDA AKA TURA ALI A MATSAYANI SHUGABANSU GABA DAYA. TABBAS WASU SUN KASANCE TAKE DA SAWUN ALI (A.S) SUNAI MASA HASSADA A MATSAYIN DA ALLAH YA BASHI, KAMAR YANDA MUKA FADA A BAYA ALI BAI TABA ZAMA KARKASHIN WANI SAHABI BA A ZUWA YAKI NE KO A WANI AIKI BA, TO DUK ALI NE KE JAGORANTARSU, SUNYI KADAN RU JAGOARANCESHI. DALILI KUWA SHINE MANZON ALLAH YACE MA : ALI NE ZAI AIKINSA IN BASHI NAN. MISALI A LOKACIN DA AKA TURA ABUBAKAR DA TAUBA ZUWA GA MUTANEN MAKA SAI JIBRIL YAZO YACE BABU MAI WANNAN AIKI SAIKAI KO WANI DAGA GAREKA DON HAKA ALI YA KASANCE MAI JIBINTAR ALAMARIN MANZON ALLAH TUN YANA RAYA, KUMA MAI JIBINTARSA BAYAN BASHI. KAR MU CIKA KU DA YAWAN MAGANA GADAI HADISIN.: أخرج أحمد من طريق الأجلح الكندي ، عن إبن بريدة ، عن أبيه قال : بعث رسول اللّه صلى الله عليه وسلم بعثين إلى اليمن علي أحدهما عليّ والآخر خالد فقال : إذا التقيتما فعلي على الناس وإن إفترقتما فكل منكم على حده فظهر المسلمون فسبوا فإصطفى عليّ إمرأة من السبي لنفسه فكتب خالد إلى النبي (ص) بذلك فلما أتيته دفعت الكتاب فقرئ عليه فرأيت الغضب في وجهه ، فقلت :يا رسول اللّه هذا مكان العائذ بك فقال : لا تقع في علي فإنه مني وأنا منه وهو وليكم بعدي ، قال : جدنا للأم الزين العراقي :الأجلح الكندي وثقه الجمهور وباقيهم رجاله رجال الصحيح. AHMAD YA RUWAITO TA HANYAR AL-AJLAH AL-KINDI DAGA IBN BURAIDAH DAGA BABANSA YACE: MANZON ALLAH (S) YA TURO RUNDUNONI BIYU ZUWA YEMEN, DAYA DAGA CIKINSU ALI DAN ABI TALIB NE JAGORA, DAYAN KUMA KHALID DAN AL-WALID. SAI YACE : IDAN SUN HADU ALI YA JAGORANCESU GABA DAYANSU (RUNDUNONIN), IDAN BAKU HADU BA TO KOWA YA JAGORANCI DAYA (TASHI) RUNDUNA. MUSULMAI SUKA SAMU NASARA AKAN MAKIYA, SAI ALI YA DAUKARMA KANSA MACE DAYA, SAI KHALID DAN AL-WALID YAYI RUBUTA ZUWA GA ANNABI (S), YANA FADA MASA WANCAN (ABINDA YA FARU). SAI ALOKACIN DA NAZO GARESHI (ANNABI (S) ), NA BASHI TAKARDAR SAI NAGA BACIN RAI A FUSKARSA (MANZON ALLAH (S) ) SAI NACE : YA MANZON ALLAH KA TURA NI DA MUTUN KA UMURCENI IN MASA DAA.MANZON ALLAH (S) YACE: KARKAYI KARYA DANGANE DA ALI (A.S) , SHI DAGA GARENI YAKE NI KUMA DAGA GARESHI NAKE, SHINE SHUGABANKU A BAYANA. ABD AL-RA`UF MUHAMMAD AL-MUNAW YACE: DAN GANE DA WANNAN HADISIN: KAKANMU NA AL-IRAQI YACE: AJLAH AL-KINDI, DUKKAN MALUMA SUNCE: THIQA NE DA SAURAN MARUWAITAN WANNAN HADISIN SAHIHAN MARUWAITANE. FAIDHUL QADIR SHARH AL-JAMI AL-SAGHIR. JUZ. 4, SHAF. 357 ALBANI YA INGANTASHI KA DUBA: SILSALAT AL-HADITH AS-SAHIHA. JUZ. 5, SHAFI, 261 -264 ALHAMDULILLAH.
Posted on: Thu, 24 Oct 2013 23:21:00 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015