ALKAKI DA RUWAN ZUMA Ingantaccen Tarihin Fiyayyen Halitta - TopicsExpress



          

ALKAKI DA RUWAN ZUMA Ingantaccen Tarihin Fiyayyen Halitta Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi Wasallam Fitowa ta 14 Alfijir Ya Keto An haifi fiyayyen halitta Muhammadu dan Abdullahi bisa ga mafi rinjayen zaton masana tarihi a ranar litinin wadda ta zo daidai da 8 ga watan Rabiul Awwal, shekara ta 13 kafin hijira, 20 kenan ga watan Afrilun shekarar 571 ta miladiyya. Amma a wani kauli an ce 2 ga watan Rabiu din ne. A wani kaulin kuma 12 ga watan. To, sai dai 2 ga wata talata ce, 12 kuma jumah. Ga shi kuwa manzon Allah (S) da kansa ya fadi cewa an haife shi ne a ranar litinin, daya daga cikin dalilan da suka sa yake azumtar wannan rana a kowane sati. Sahihu Muslim, hadisi na 1162. Haka shi ma raayin da ke cewa, an haife shi ne a cikin watan azumi shi ma ba ya da karfi sosai. Duba: Al-Mawahib Al-Ladunniya, na Qastalani (1/25) da Al-Bidaya Wan-Nihaya na Ibn Kathir (2/260) da Al-Miyar Al-Murib na Wansharishi (7/100). An haifi fiyayyen halitta ne a wani wuri kusa da Kaaba, wata 2 kacal bayan yakin giwaye da madaukakin sarki ya fada a Suratul Fil. A lokacin haifuwarsa mahaifiyarsa ta ga wani irin haske wanda ya haska ma ta benayen kasar Sham. Shakka babu! Haske ne ta haifo ma duniya wanda aka dade ana jiran sa. Duba: Al-Musnad na Imam Ahmad (5/262) da Al-Mustadrak na Imam Al-Hakim (2/600) da Majma Az-Zawaid na Haithami (8/222). Maccen da ta karbi bikin manzon Allah (S) ita ce kuyangar mahaifinsa; Ummu Aiman. Haka kuma nono na farko da ya tsotsa daga kirjin Suwaiba ne; kuyangar baffansa Abu Lahabi. Babbar alama mai nuna cewa, shi ne manzon da ya zo ya yanta bayi, ya fitar da alummar duniya daga kangin bauta. Duba: Ar-Rahmah Al-Muhdah, na Sheikh Dr. Ali Muhammad As-Sheikh, bugun Dar Maktabat Al-Iman, Tarabulus, Lebanon, na farko, 1434H/2013M, shafi na 22. Kafin mu fantsama a cikin tarihinsa daga haifuwa zuwa janaiza zai yi kyau mu tsaya mu yi nazari kyakkyawa a kan asalinsa. Domin duk wanda yake tunanin cewa, manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam fulawar juji ne; maana, shi kadai ne nagartacce ba tare da duge da asali gami da zumu ba to, ya kwana da sanin cewa ya kurba giyar gigita. Allah ya hada mu a darasi na gaba. Daga; Dr. Mansur Sokoto
Posted on: Tue, 03 Dec 2013 21:32:25 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015