ALƘUR,ANI MAI TSARKI: FALALARSA, MATSAYINSA, - TopicsExpress



          

ALƘUR,ANI MAI TSARKI: FALALARSA, MATSAYINSA, DA KASANCEWARSA TUSHEN SHARI,AR ADDININ MUSULUNCI “Alƙur,ani zancen Allah ne, Shi ne Ya fare shi ba tare da an san yadda Ya furta shi ba, kuma Ya saukar dashi ga AnnabinSa ta hanyar wahayi, kuma lalle ne tabbas Muminai sun gaskata shi, kuma sun sakankance da cewa haƙiƙa Zance ne na Allah (S.W.T.), ba halittaccen abu ba ne kamar zancen halittunsa, duk kuma wanda ya ji shi sa,an nan ya riya cewa zancen mutum ne, to, lalle ne ya kafirta....” Wanda Ya saukar da shi (S.W.T.) Ya sifanta shi, inda Yake cewa: ((kuma lalle shi, haƙiƙa, Littãfi ne mabuwãyi. Ɓarna bã zã ta je masa ba daga gaba gare shi, kuma bã zã ta zo ba daga bãya gare shi. Saukarwa ce daga Mai hikima, Godadde.)) (Suratu Fusilat:41-42). Kamar yadda Allah Mai bayyanannar Ƙudura Ya sifanta shi, Yana cewa: ((Littãfi ne an kyautata ãyoyinsa, sa,an nan an bayyana su daki-daki, daga wurin Mai hikima, Mai ƙididdigewa.)) (Suratu Hud: 1). Lalle ne: Haƙiƙa ayoyin Alƙur,ani mai tsarki suna cikin tabbataccen tsari matuƙa, da kuma cikakken bayani wanda Mai hikima Ya kyautata tsarinsu, sa,an nan Gwani Ya rarrabe su daki-daki, kuma haka wannan Littafi zai ci gaba da kasancewa gagara-koyo ta ɓangaren zurfin balaga, hukunce-hukunce, ilimi, tarihi da wasunsu, har zuwa lokacin da Allah zai gaji duniya da abin da ke cikinta, babu wani abu na canji da zai shigo masa komin ƙanƙantarsa, hakan na gaskata zancen Allah (S.W.T.): ((Lalle Mu ne, Muka saukar da Ambato (Alƙur,ãni), kuma lalle Mu, haƙiƙa, Mãsu kiyãyewa ne gare shi)). (Suratul Hijr: 9) Kuma dukan duniya ba ta taɓa samun wani littafi wanda ya tattara dukan alheri, kuma mafi shiryarwa ga hanya madaidaiciya, kuma mafi samar da abin daɗaɗawa ga mutane, kamar wannan Alƙur,ani Mai girma ba, wanda Ya faɗi a cikinsa cewa: ((Lalle ne wannan Alƙur,ãni yanã shiryarwa ga (hãlayen) waɗanda suke mafi daidaita, kuma yana bãyar da bushãra ga muminai waɗanda suke aikata ayyuka na ƙwarai (cewa) Lalle ne sunã da wata ijãra mai girma)). (Suratul Isra,:9) Wannan Alƙur,anin Mai tsarki, Allah Ya saukar da shi ne ga ManzonSa Muhammad (S.A.W.); domin ya fitar da mutane daga cikin duhunhuna zuwa haske, Allah (S.W.T.) Ya ce: ((Littãfi ne, Mun saukar da shi zuwa gare ka d‘min ka fitar da mutãne daga duhunhuna zuwa ga haske, da iznin Ubangijinsu, zuwa ga tafarkin Mabuwãyi, Abin g‘dewa)). (Suratu Ibrahim: 9). Allah Ya buɗe makafin idanuwa, da kuramen kunnuwa, da rufaffun zukata, kuma ya bai wa Musulmai tabbacin samun jin daɗi da walwala a duniyarsu da lahirarsu, idan har suka lazimci karanta shi gaskiyar karantawa, tare da fahimtar surorinsa da ayoyinsa, kuma suka fahimci jumloli da kalmominsa, kuma suka tsaya a kan iyakokinsa, sannan suka bi abin da ya umurce su da shi, kuma suka hanu daga abin da ya hane su, kuma suka ƙawatu da abin da ya shar,anta, kuma suka aiwatar da abin da yake karantarwa, da abin da yake kira zuwa gare shi, tare da lazimtar halaye nagari da kyawawan ɗabi,u da yake kira zuwa gare su, a kan kawunansu, da iyalansu, da al,ummr da suke rayuwa a cikinta. Allah (S.W.T.) Ya ce: ((Waɗanda Muka bai wa Littãfi suna karatunsa a kan hakkin karãtunsa, waɗannan suna imãni da shi.)) (Suratul Baƙara: 121) . Ibn Abbas ya ce: ,Suna biyayya gare shi haƙƙin biyayya,, suna halatta abubuwan da ya halatta kuma suna haramta abubuwan da ya haramta, kuma ba su canza shi daga yadda yake., Ƙatada kuma ya ce: ,Waɗannan su ne Sahabban Muhammad (S.A.W.) sun yi imani da Littãfin Allah tare da gaskata shi, sun halatta abubuwan da ya halatta, kuma sun haramta abubuwan da ya haramta, kuma sun yi aiki da abubuwan dake cikinsa. Lalle ne, haƙiƙa lokacin da aljannu suka saurare shi ya rasta zukatansu, kuma zukatansu sun cika da ƙaunarsa tare da girmama shi, sa,an nan suka gaggauta kiran al,ummarsu zuwa ga binsa, kamar yadda Allah ke cewa: ((Sai suka ce, ,Lalle ne mu, mun ji wani abin karantãwa (Alƙur,ani), mai ban mãmãki. ,Yana nuni zuwa ga hanyar ƙwarai, sab‘da haka mun yi imãni da shi, bã zã mu sãke bautã wa Ubangijinmu tãre da k‘wa ba. ,Kuma lalle ne shi, girman Ubangijinmu, Ya ɗaukaka, bai riƙi mãta ba, kuma bai riƙi ɗã ba”). (Suratul Jinn: 1-3) Kuma lalle Allah Ya bada labarinsu a cikin Alƙur,ani cewa: ((Suka ce, Ya mutãnenmu! Lalle mu, mun ji wani Littãfi an saukar da shi a bãyãn Musã, mai gaskatãwa ga abin da ke a gaba da shi, yanã shiryarwa ga gaskiya da kuma zuwa ga hanya madaidaiciya. Yã mutãnenmu! Ku karɓa wa mai kiran Allah, kuma ku yi imãni da Shi, Ya gãfarta muku daga zunubanku, kuma Ya tserar da ku daga azãba mai raɗaɗi)). (Suratul Ahƙãf: 30-31). Saboda waɗannan abubuwa duka, shi wannan Littafi Mai albarka Ya ɗaukaka a kan Littafan sama da suka gabace shi, kuma ya kasance mafifici a kansu wajen matsayi, Allah (S.W.T.) Yace: ((Kuma lalle shi, a cikin uwar littãfi, a wurinMu, haƙiƙa, maɗaukaki ne, bayyananne)). Suratu Zukhruf: 4. Sa,an nan Allah (S.W.T.) ya ce: ((Kuma Mun saukar da Littãfi zuwa gare ka da gaskiya, yana mai gaskatãwa ga abin da yake gaba gare shi daga Littãfi (Taurata da Injila), kuma mai halartãwa a kansa)). (Suratul Ma,ida: 48.) Malaman tafsiri sun ce: “Ɗaukakar Alƙur,ani bisa sauran Littafan Allah duk kuwa da cewa dukansu sun zo ne daga gare Shi, da wasu al,amura: daga cikinsu, akwai cewa shi ya fi su ta hanyar yawan surorinsa. Ya zo a cikin Hadisi cewa, lalle keɓanta Annabinmu Muhammad (S.A.W.) da Suratul Fatiha, da ƙarshen Suratul Baƙara, haka kuma a cikin littafi mai suna (Musnadud Darami) an samo Hadisi daga Abdullahi bn Mas,ud (R.A.) ya ce: Lalle surori guda bakwai masu tsawo kamar Attaura suke, kuma surori masu ayoyi ɗari kamar Linjila suke, kuma gajerun surori kamar Zabura suke, kuma sauran Alƙur,ani bayan wannan falala ce daga Allah). Kuma an samo daga Imam Ahmad da Ɗabarani daga Wãsila bn Al-Asƙa, cewa, lalle Annabi (S.A.W.) ya ce: (An ba ni surori bakwai masu tsawo a matsayin Attaura, kuma aka bani surori masu ayoyi ɗari a matsayin Zabura, kuma aka bani gajerun surori a matsayin Linjila, sa,an nan aka fifitani da surorin (mufassal), wato gajerun surori). Musnadul Imam Ahmad (2/107). Kuma surorin bakwai masu tsawo sun fara ne daga farkon Suratul Baƙara har zuwa ƙarshen Suratul A,araf, waɗannan surori shida kenan, amma sun samu saɓani a kan ta bakwai ɗin, shin Suratul Anfal ce haɗe da Bara,a tare, sadoda rashin raba tsakaninsu da Bisimilla, ta yadda za a sanya Anfal da Bara,a a matsayin sura guda, ko kuwa itace Suratu Yunus. Amma surorin da ake cewa (ma,un), sune waɗanda ayoyinsu suka wuce ɗari ko kuma suka yi kusa da hakan. Su kuma (Mathani), sune surorin dake biye da surori masu ayoyi ɗari, wajen yawan ayoyin, ko kuwa sune surorin da yawan ayoyinsu suka gaza ayoyi ɗari; saboda sun keɓanta da cewa ba a yawan maimaita abubuwa a cikinsu, kamar yadda ake yi a cikin surori masu tsawo da kuma masu ayoyi ɗari. Amma surori waɗanda ake cewa (Mufassal), watau masu yawan bayanin hukunci, sune waɗanda ke bin gajerun Surori, amma an samu saɓani bisa farkosu, an ce: sun fara ne daga farkon Suratus Saffat, kuma an ce: Daga farkon Suratul Fathi, kuma aka ce daga farkon Suratul Hujrat, sannan aka ce: Daga farkon Suratu Ƙ,- Wannan shi ne abin da Ibn Kathir da Ibn Hujur suka rinjayar - Kuma an ce: wasunsu ne, sai dai sun haɗu a kan cewa ƙarshen Mufassal shi ne ƙarshen Alƙur,ani Mai tsarki. Daga cikinsu: akwai cewa Allah Ya sanya salonsa ya zama mu,jiza, duk kuwa da cewa sauran Littafan Allah (S.W.T.) suna ɗauke da mu,ujiza a cikinsu, ta wajen bayar da labaran abubuwan gaibu tare da bayyanar da hukunce- hukunce, sai dai babu wani salo da ya saɓa wa al,ada a cikinsu, don haka Alƙur,ani ya ɗaukaka a kansu da irin waɗannan ma,anonin da ire-iren su, wannan ne abinda aya ke nunawa, inda Allah (S.W.T.) ke cewa: ((Kuma lalle shi, a cikin uwar Littãfi, a wurinMu, haƙiƙa, maɗaukaki ne bayyananne)). (Suratuz Zukhruf: 4). Haka kuma daga abin da ke nuni ga haka akwai faɗin Allah (S.W.T.): ((Kun kasance mafi alherin al,umma wadda aka fitar ga mutane)). (Suratu Ãl ,imrana: 110). Hafiz Ibn Kasthir ya ce, a cikin littafi mai suna (Fada,ilul-Ƙur,an) , shafi na 102-103: (Lalle haƙiƙa, sun sami wannan ɗaukaka ne da albarkacin Alƙur,ani Mai girma, wanda Allah Ya fifita a kan dukan Littafan da Ya saukar, Ya kuma sanya shi ya mamaye sauran Littafan, kuma ya kasance Mai shafe hukuncinsu, kuma Ya sanya shi ya kasance Littafin ƙarshe, domin kuwa dukan Littafan da suka gabata, an saukar dasu ne lokaci guda, amma shi Alƙur,ani ya sauka ne kashi-kashi, gwargwadon aukuwar abubuwa, saboda tsananin kula da shi, da kuma tsananin kulawa da wanda aka saukar dashi a gare shi, a kowane lokaci yakan sauka sau guda ne kamar saukar Littafi daga cikin Littafan da suka gabata). Kuma wannan Littafi Mai albarka Ya tabbatar da gaskiyar ilmomin duniya masu yawa, waɗanda ke bijirarwa tare da nuni da cewa akwai Allah, kuma da nuni ga girman ƘudurarSa, da kaɗaituwarSa, Allah (S.W.T.) Ya ce: ((Kuma Muka sanya dukan kome mai rai daga ruwa? Shin, bã zã su yi imãni ba? )). (Suratu Ambiya,i: 30). Kuma Ya kwaɗaitar zuwa ga amfana da dukan abinda idanuwan mu ke iya gani na rayuwa wanda Allah Ya halitta, Allah (S.W.T.) Ya ce: ((Ka ce, Ku dubi abin da yake cikin sammai da ƙasa)). (Suratu Yunus: 101). Allah (S.W.T.) Ya ce: ((Kuma Ya h‘re muku abin da ke cikin smmai da abin da ke cikin ƙasa, gabã ɗaya daga gare Shi yake. Lalle ne, a cikin wancan, haƙiƙa, akwai ãy‘yi ga mutãne waɗanda ke yin tunãni)). (Suratul Jathiya: 13). Don haka, ya zama tilas ga musulmi su nemi sanin ilmomin kimiyya na duniya kada su haramta wa kawunan su amfanin dake tattare da irin waɗannan abubuwa masu girma da daraja waɗanda Allah Ya taskace a cikin sammanSa da ƙasarSa. Lalle, haƙiƙa zance a kan Alƙur,ani mai tsarki alherinsa ba ya ƙarewa, domin shine ke sanya musulmi son yin adalci da kuma yin shawara a tsakanin su, kuma ya hana su aikata zalunci da kuma danniya, taken mabiyansa shi ne ƙarfin imani, rashin so da fifita kai, kuma suna tausayawa junan su. Don haka, sai mu rayu tare da Alƙur,ani muna masu karantawa, da aiki da shi tare da natsuwa da shi, da kuma haddace shi, saboda rayuwa bisa shaƙuwa da Alƙur,ani domin ayyukan da muminai suka sifantu da su ne Allah (S.W.T.) Ya ce: ((Lalle, waɗanda ke karãtun Littãfin Allah kuma suka tsayar da salla, kuma suka ciyar daga abin da Muka arzuta su da shi, a asirce da a bayyane, sunã fãtan (sãmun) wani fatauci ne wanda bã ya yin tasgaro. D‘min Allah zai cika musu sakamakonsu, kuma Ya ƙara musu daga falalarSa. Lalle Shi Mai gãfara ne, Mai g‘diya.)) (Suratul Faɗir: 29-30). Allah (S.W.T.) Yana yabawa masu yawan karanta Littafinsa a cikin waɗannan ayoyi guda biyu, karatu mai tare da natsuwa wanda ke iya kaiwa ga fahimta da kuma ratsa zukata, yana daga cikin abin da babu kokanto a kansa cewa, lalle ne karatun da ya ratsa zuciya, to, tabbas ne yana kaiwa ga aiki da abin da ake karantawa. Saboda haka Allah (S.W.T.) Ya sanya a bayan karatun Alƙur,ani, a tsayar da salla, kuma a ciyar a ɓoye da kuma a bayyane daga falalar Allah, sannan da ƙaunar masu karatun cewa suna kasuwanci ne da wanda babu asara a cikinsa, domin sun sani cewa Abin da ke wajen Allah Shi ne mafi alheri daga abin da su suke ciyarwa, kuma suna yin kasuwanci wanda zai kai ga cika musu ladarsu da yi musu ƙari daga falalar Allah, domin Shi (Allah) Mai gafara ne kuma Godadde, Yana yafe wa wanda ya taƙaita, Ya kuma gode wa wanda ya yi aiki. Don haka, ya zama tilas a riƙa karanta Alƙur,ani karatu tare da natsuwa da fahimta, wanda zai sanya a fahimci jumlolin Alƙur,ani, cikakkiyar fahimta, idan wani abu na ma,ana ya wuyata ga mai karatu, to, sai ya tambayi ma,abuta sani, Allah (S.W.T.) Yace: ((Sai ku tambayi mutãnen Ambato idan kun kasance ba ku sani ba)). (Suratun Nahali: 43). Kuma karatun Alƙur,ani cikin jama,a abu ne da ake so koyaushe, a cikin Hadisin da Abu Huraira (R.A.) ya ruwaito ya ce, Manzon Allah (S.A.W.) ya ce: “Mutane ba su gushe ba suna taruwa a cikin wani Ɗaki daga Ɗakunan Allah suna karanta Littafin Allah kuma suna koyar da shi ga juna, face natsuwa ta sauka gare su, kuma rahama ta lulluɓe su, kuma Mala,iku su yi musu laima, kuma Allah Ya ambace su daga cikin waɗanda ke gare Shi, kuma duk wanda aikinsa bai cece shi ba, to, danginsa ba za su cece shi ba.” (Sahih Muslim: 2699). Kuma faɗin Manzon Allah (S.A.W.) a cikin wannan Hadisi mai daraja (Mutane ba su gushe ba suna taruwa a sikin wani Ɗaki daga Ɗakunan Allah) ba wai an taƙaita bisa masallaci ne ba kawai; domin akwai wata ruwayar ta Muslim dake cewa: “Mutane ba su gushe ba su na ambaton sunan Alllah (S.W.T.), face Mala,iku sun yi musu laima...,” to, idan suka taru a wani wurin da ba masallaci ba, to, suna samun irin wannan ladar, don haka ke nan, keɓanta Ɗakin Allah da ambato a nan ya zo ne a matsayin abu mafi rinjaye ba hakan ake nufi ba, don haka, taruwa domin karatu da karantar da Alƙur,ani da nufin neman fahimtar ayoyin Allah da abin da suke nunawa na hukunci da abin lura, ko a wane wuri ne kuwa, to za a samu wannan falalar, ammam idan taruwr domin karatu da karantar da Alƙur,ani a cikin masallaci ne, to, ya fi taruwa a wani wurin na daban, saboda abin da masallaci ya keɓanta da shi wanda babu a wani wurin daban. Kuma an samo Hadisi daga Abdullahi bn Mas,ud (R.A.) ya ce, Manzon Allah (S.A.W.) ya ce: “Duk wanda ya karanta harafi daga Littafin Allah yana da lada guda, kuma kowane lada ɗaya za a ninka shi har sau goma, amma lalle ni ba zan ce A.L.M. harafi ne ba, sai dai (A.) harafi ne, (L.) harafi ne, kuma (M.) harafi ne.”) Tirmidhi (Hadisi na 3075). Kuma an samo Hadisi daga Usman bn Affan (R.A.) daga Annabi (S.A.W.) ya ce: “Mafi alheri daga cikinku shi ne wanda ya san Alƙur,ani kuma ya koyar da shi.” Sahih Al-Bukhari, (Hadisi na 4739). Wannan yana nuni ga bayanin muhimmancin sanin Alƙur,ani, da kuma kwaɗaitarwa zuwa gare shi, lalle an tambayi Sufyan Ath-Thauri cewa shin a ganinka, mutum ya halarci yaƙi shi ne mafi alheri ko kuwa ya karanta Alƙur,ani? Sai ya ce: Ya karanta Alƙur,ani shi ne mafi kyau, domin Manzon Allah (S.A.W.) ya ce: “Mafi alheri daga cikin ku shi ne wanda ya koyi Alƙur,ani kuma ya koyar da shi”. Imam Abu Abdur Rahaman As-Salmi ya kasance yana koyar da Alƙur,ani har tsawon shekaru arba,in, saboda jin wannan hadisin, kuma ya kasance a duk lokacin da ya bada ruwayar wannan Hadisin ya kan ce, wannan shi ne ya zaunar da ni a mazauni na wannan. Hafiz Ibn Kathir ya ce a cikin littafi mai suna (Fada,ilul Ƙur,an) shafi na 126-127: Manufar abin da Manzon Allah (S.A.W.) ke cewa: Mafi alheri daga cikin ku shi ne wanda ya san Alƙur,ani kuma ya sanar da shi, wannan shi ne sifofin muminai mabiya Manzanni, kuma suna masu cika kyawawan ayyuka ga kawunansu, kuma suna cikawa ga wasunsu, kuma hakan ya ƙunshi taƙaitaccen amfani da kuma mai ɗorewa, saɓanin sifofin manyan kafirai waɗanda ba su da amfani, kuma ba su barin wani ya amfana, kamar yadda Allah (S.W.T.) Ya ce: ((Waɗanda suka kãfirta, kuma suka kange daga hanyar Allah, Mun ƙara musu wata azãba bisa ga azãbar)). (Suratun Nahl: 88) Kamar kuma yadda Ya ce: ((Kuma sunã hanãwa daga gare shi, kuma sunã nisanta daga gare shi,)). (Suratul An,am: 26). Bisa batutuwa biyu mafiya inganci na malaman tafsiri game da wannan, shi ne lalle su (kafirai) suna hana mutane bin Alƙur,ani, tare kuma da ƙara nisantarsu daga gare shi su ma, sai suka haɗa tsakanin ƙaryatawa da kangewa, kamar yadda Allah (S.W.T.) Ya ce: ((To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙaryata ãy‘yin Allah, kuma ya hinjire daga barinsu?)). (Suratul An,am: 157). Wannan shi ne halayen mafiya sharrin kafirai kamar yadda sha,anin zaɓaɓɓun mutane masu yin biyayya ga Ubangijinsu yake, suna masu ƙoƙarin cika ayyuka na ƙwarai ga kawunan su, suna masu ƙoƙarin cika kyawawan ayyuka ga wasunsu, kamar yadda ya zo a cikin wannan Hadisin, kuma kamar yadda Allah (S.W.T.) Ya ce: ((Kuma wãne ne mafi kyau ga magana daga wanda ya yi kira zuwa ga Allah, kuma ya aikata aiki na ƙwarai, kuma ya ce, ni, inã daga mãsu sallamãwar al,amari zuwa ga Allah?)). (Suratu Fusulat: 33). Sai aka haɗa tsakanin kira zuwa ga Allah, (S.W.T.) ta hanyar kiran salla, ko kuwa ta waninsa, daga nau,o,in kira zuwa ga Allah, kamar koyar da Alƙur,ani da Hadisi da Fiƙihu da wasunsu daga ayyukan da ake yi domin neman yardar Allah, da kuma wani aiki da yake nagari ne, ko zance nagari, to, babu wani mutum zai sami kansa a cikin wani yanayi mai kyau da ya wuce wannan. Kuma kamar yadda rahamar Allah (S.W.T.) ta ƙunshi masu karanata LittafinSa, kuma masu tsayawa ga iyakokinsa, haka kuma ta ƙunshi masu sauraren karatunsa, Allah (S.W.T.) Ya ce: ((Abin sani kawai, muminai su ne waɗanda idan an ambaci Allah, sai zukãtansu su firgita, kuma idan an karanta ãyoyinSa a kansu, sai su ƙãrã musu wani imãni, kuma ga Ubangijinsu suke d‘gara; Waɗanda suke tsayar da salla, kuma daga abin da Muka arzutã su sunã ciyarwa. Waɗannan su ne muminai da gaskiya. Sunã da daraj‘ji a wurin Ubangijinsu, da wata gãfara da arziki na karimci)). (Suratul Anfal: 2-4). Kuma an samo Hadisi daga Abdullahi bn Mas,ud(R.A.) ya ce, Manzon Allah (S.A.W.) ya ce mini: “Ka karanta mini Alƙur,ani,” sai na ce: Ya Manzon Allah, shin zan karanta maka gashi kuwa a gare ka aka saukar da shi? Ya ce: “Na,am, lalle ni ina son na saurare shi daga wanina,” sai na karanta Suratun Nisa,i har zuwa wannan ayar ((To, yãyã, idan Mun zo da shaidu daga dukan al,umma, kuma Muka zo da kai a kan waɗannan, kana mai shaida!)) Sai ya ce: “Ya isa haka,” sai na dube shi sai na ga hawaye na zuba daga idonsa. (Bukhari: 4582 Muslim: 800Abu Dauda:3668). Imam An-Nawawi ya ce: (Akwai fa,idodi masu yawa a cikin wannan Hadisin, daga cikinsu akwai kwaɗaitarwa zuwa ga sauraren karatun Alƙur,ani, da himmatuwa wajen saurarensa, tare da yin kuka a lokacin da ake karanta shi, da kuma natsuwa ga karatun, da kuma bukatuwar mutum da a riƙa karanta masa Alƙur,ani domin ya saurara, shi ne mafi shiga zuciya da kuma fahimta fiye da karantawarsa da kansa). Don haka, ya zama tilas ga dukan Musulmi ya san Alƙur,ani, haƙƙin saninsa, ya kuma kiyaye tsarkinsa, kuma ya lazimci iyakokin addini a lokacin da yake sauraren ayoyin Alƙur,ani Mai tsarki, kuma ya yi koyi da abubuwan da Salihan magabata suka gadar mana, game da karatun Alƙur,ani Mai tsarki da kuma saurarensa, lalle sun kasance kamar rana mai haske suke, ana yin koyi da su wajen cikar imani da tsoron Allah da natsuwar zuciya, suna masu imani da zancen Allah (S.W.T.): ((Kuma lalle Shi (Alƙur,ani), haƙiƙa, saukarawar Ubangijin halittu ne. Ruhi amintacce ne ya sauka da shi. A kan zuciyarka, d‘min ka kasance daga mãsu gargaɗi. Da harshe na Larabci mai bayãni)). (Suratush Shu,ara,: 192-195). Tabbas, lalle ne Alƙur,ani Mai tsarki, tare da lafazozinsa da ma,anoninsa zancen Allah ne, shi ne tsarin rayuwa daga sama ga mutane da kuma dukan halittu baki ɗaya, sa,an nan shi ne madogara na farko ga al,amuran musulmai, sa,an nan kuma tushen hukuncin da suke komawa gare shi, kuma shi ne makomar dukkan hukunce-hukunce na shari,a, sa,an nan kuma hukunce-hukuncen dake cikin Alƙur,ani Mai tsarki ba a saukar da su a lokaci guda ba, sai-dai an saukar da su ne daki-daki, a tsawon zamanin manzanci, wasu hukunce-hukuncen an saukar da su ne domin tabbatarwa da kuma ƙarfafa zuciyar Annanbi, (S.A.W.)- wasu kuwa sun sauƙa ne domin tarbiyyantar da wannan al,ummar mai tasowa da ilimi da kuma aiki, wasu kuwa sun sauka ne a lokacin aukuwar abubuwan ga Musulmi a cikin rayuwar su ta yau da kullun a cikin lokuta da zamuna daban-daban, don haka a duk lokacin da wani abu ya faru sai wani abu daga Alƙur,ani da ya dace da wannan abu ya sauka, kuma ya bayyana hukunci Allah a cikin irin wannan, akwai shari,o,i da kuma abubuwan dake aukuwa a cikin al,ummar Musulmi a zaminin saukar wahayi, sai mutane su bukaci sanin hukuncinsu, daga nan sai ayoyi su sauka suna masu bayani bisa hukuncin nasu, kamar haramcin shan giya. Lalle ne, Imam Ahmad ya ruwaito daga Abu Huraira (R.A.) ya ce: Annabi (S.A.W.) ya zo Madina alhali suna shan giya, suna kuma cin dukiyar caca, sai suka tambayi Manzon Allah (S.A.W.) game da waɗannan abubuwa sai Allah Ya saukar da: ((Suna tambayar ka game da giya da cãcã. Ka ce: A cikinsu akwai zunubi mai girma da wasu amfãn‘ni ga mutãne, kuma zunubinsu ne mafi girma daga amfaninsu)), (Suratul Baƙara: 219). Sai mutane suka ce, bai haramta mana ba sai dai kawai ya ce: A cikinsu akwai zunubi mai girma, sun kasance suna shan giya har wata rana wani mutum daga Muhajirina yana limanci ga wasu abokansa a Sallar Magariba, sai ya rikice a cikin karatunsa, sai Allah ya saukar da wata ayar mafi tsanani: ((Ya ku waɗanda suka yi imani! Kada ku kusanci salla alhali kuwa kuna masu maye, sai kun san abin da kuke faɗa)). (Suratun Nisa’i: 43). Dukan mutane sun kasance suna shan giyar har ɗayansu kan zo yin salla a cikin halin maye, sai aka saukar da wata ayar mafi tsanani: ((Ya ku waɗanda suka yi imani! Abin sani kawai, giya da ceca da refu da kiban ƙuri,a, ƙazanta ne daga aikin Shaiɗan, sai ku nisance shi, wa la,alla ku ci nasara)). (Suratul Ma’ida: 90). Suka ce mun hanu, Ya Ubangijinmu, sai mutane suka ce: Ya Manzon Allah, mutane sun mutu a wurin ɗaukaka kalmar Allah, ko a kan shimfiɗunsu (gidajensu), alhali suna shan giya, kuma suna cin dukiyar caca, kuma haƙiƙa Allah Ya sanya shi ƙazanta daga aikin Shaiɗan, sai Allah Ya saukar da: ((Babu laifi a kan waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, a cikin abin da suka ci, idan sun yi taƙawa kuma suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sa,an nan suka yi taƙawa kuma suka yi imani, sa,an nan kuma suka yi taƙawa kuma suka kyautata. Kuma Allah Yana son masu kyautatawa)). (Suratul Ma’ida: 93). Sai Annabi (S.A.W.) ya ce: “da an haramta musu, to, da sun hanu kamar yadda kuka hanu.” (Musnad Imam Ahmad, 2/351-352). Sahihul Bukhari (Hadisi na 4620). An samo daga Anas bn Malik (R.A.) ya ce: Na kasance ina shayar da mutane giya a gidan Abu Ɗalha, sai aka saukar da haramcin shan giya, sai aka umarci wani mai yekuwa ya yi yekuwa, sai Abu Ɗalha ya ce: Fita ka duba mene ne wannan muryar ke cewa? Sai na fita, kuma na ce: Wannan wani mai yekuwa ne yana cewa: Ashe lalle ba a haramta shan giya ba? Sai ya ce mini: "Tafi ka zubar da ita, har ta gudana a kan hanyoyin Madina." Ya ce: Giyar tasu a wannan lokacin ita ce (Fadih), watau giyar da ake yinta da ,ya,yan dabino; wasu jama,a suka ce: An kashe wasu mutane alhalin wannan giyar tana cikin cikinsu, Ya ce: Sai aka saukar da wannan ayar: ((Babu laifi a kan waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, a cikin abin da suka ci)). Daga abin da ya gabata za mu iya sanin cewa, lalle haramcin giya ya sauka ne bisa matakai uku: Lokacin da aka saukar da ayar Suratul Baƙara: ((Suna tambayar ka game da giya da cãcã. Ka ce: A cikinsu akwai zunubi mai girma da wasu amfãn‘ni ga mutãne, kuma zunubinsu ne mafi girma daga amfaninsu)). Hakan ya ƙunshi hani wanda ba shi da ƙarfi, sai mutane masu tsananin imani suka bar shan giya, sai Umar (R.A.) ya ce: Ya Allah Ka bayyana mana game da giya bayyanawa mai warakarwa, sannan aka saukar da ayar Suratun Nisa,i: ((Ya ku waɗanda suka yi imani! Kada ku kusanci salla alhali kuwa kuna masu maye, sai kun san abin da kuke faɗa)), sai Musulmi suka nisanci shanta a cikin lokacin da suke zaton maye zai iya kai su har zuwa lokacin salla, sai Umar (R.A.) ya ce: Ya Allah Ka bayyana mana game da giya bayyanawa mai warakarwa. Sai ayar Suratul Ma,ida ta sauka: ((Ya ku waɗanda suka yi imani! Abin sani kawai, giya da caca da refu da kiban ƙuri,a, ƙazanta ne daga aikin Shaiɗan, sai ku nisance shi, wa la,alla ku ci nasara)). A wannan lokacin da aka kira Umar (R.A.), aka karanta masa sai ya ce: “Mun hanu”. Haka hukunci ya yi ta sauka bisa matakai sannu- sannu, domin Allah (S.W.T.) Ya tsarkake al,ummar musulmi daga al,adun da suka saɓa wa hanyar Allah, Ya kuma cika musu da falalarSa da ta ƙunshi rangwame da haƙuri, da kuma ba da kyawawan misalai da nuna soyayya da riƙon amana tare da kiyaye hakkin maƙwabtaka, da kuma adalci da dai wasun waɗannan da dama na daga halaye nagari. Allah (S.W.T.) Shi kaɗai ne Mai saukar da hukunci ga bayinSa. Allah (S.W.T.) Ya ce: ((Ka ce: Lalle ne inã kan hujja daga Ubangjina, kuma kun ƙaryata (ni) game da Shi; abin da kuke neman gaugãwarsa, bã ya wurina, hukunci kuwa bai zama ba fãce, ga Allah, Yanã bãyar da lãbãrin gaskiya, kuma shi ne mafi alherin mãsu rarrabewa.)) (Suratul An,am: 57). Allah ba Ya saukar da wani hukunci ga mutane face abin da yake alheri ne da daɗaɗawa gare su, duk ɗaya ne, sun fahimci hikimar dake tattare da shi ko a,a? Alƙur,ani mai tsarki sh ine tushe na farko ga hukuncin Shari,a. Amma Sunnar Annabi (S.A.W.) ita ce tushe na biyu game da hukunci, babu saɓani a tsakanin malaman fiƙihu bisa cewa lalle ita sunna, hujja ce mai ƙarfi da za a dogara da ita bayan Alƙur,ani mai tsarki, Allah (S.W.T.) Ya ce: ((Yã ku waɗanda suka yi imani! Ku yi ɗã’a ga Allah, kuma ku yi ɗã’a ga ManzonSa, da ma’abuta al’amari daga cikinku. Idan kun yi jãyayya a cikin wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah da ManzonSa idan kun kasance kunã imãni da Allah da Rãnar Lãhira. wannan ne mafi alheri, kuma mafi kyau ga fassara)). (Suratun Nisa,: 59). Kuma Allah (S.W.T.) Ya ce: ((Kuma Mun saukar da Ambato zuwa gare ka, d‘min ka bayyana wa mutãne abin da aka sassaukar zuwa gare su)). (Suratun Nahl:44). Kuma Allah (S.W.T) Ya ce: ((kuma abin da Manzo ya bã ku, to, ku kama shi, kuma abin da ya hane ku, to, ku bar shi. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle, Al1ah, Mai tsananin uƙuba ne)). (Suratul Hashr:7). Imam Ibn Alƙayyim Al- Jauziyya ya yi bayani kan matsayin Sunna dangane da Alƙur,ani a cikin littafinsa mai suna (I,ilamul Muƙi,ina An Rabbil Alamin) Hadisi na 2, shafi na:263, inda yake cewa: “Sunna da Alƙur,ani suna da halaye uku: Na farko: Shi ne ta yi daidai da shi ga hukunci ta kowace fuska, ta yadda Sunna da Alƙur,ani za su daidaita a kan hukunci guda ta hanyar kawo dalilai masu gamsarwa. Na biyu: ta kasance bayani ce ga manufar Alƙur,ani da kuma tafsiri a gare shi. Na uku: ta kasance ta na wajabta wani hukunci da Alƙur,ani ya yi shiru bai zartar da wani hukunci ba a kai, ko kuwa ta haramta abinda ya yi shiru bai haramta ba, ba ta wuce waɗannan abubuwa uku, kuma ba ta saɓa wa Alƙur,ani da kome ba ta kowace fuska”. Don haka, Sunna tana tabbatar da abubuwan da suka zo a cikin Alƙur,ani mai tsarki ne na hukunce- hukunce, ta kan fassara abubuwan da nassi ya kawo, ko kuma ta yi bayani ga hukunce- hukuncen da aka kawo a dunƙule, kuma ta kan kawo hukunci game da wasu halayen da wani nassi bai sauka ba a cikin Littafi, amma duk da haka ba a komawa ga Sunna a matsayin dalili ga hukunce-hukunce, sai idan nassin Alƙur,ani bai warware hukuncin ba, domin sunna ita ta bayyana mana -mu musulmi- cewa salloli farillai biyar ne a rana da dare, kuma ita ce ta bayyana mana yawan raka,o,insu da rukunansu, kuma ita ce ta bayyana mana haƙiƙanin zakka, da kuma ga wane ne take wajaba, da kuma yadda ake rabonta, sa,an nan kuma ta bayyana mana yadda ake aikin Hajji da Umra, da kuma cewa Hajji ba ya wajaba sai sau guda ne a tsawon rayuwa, ta kuma bayyana mana miƙatocinsa da adadin ɗawafinsa. Don haka, ya zama wajibi ga duk wanda yake da,awar cewa shi mai riƙo ne da Alƙur,ani, sannan kuma ya ƙauracewa Sunna ya gaggauta sabunta imaninsa, tare da komawa ga Allah, (S.W.T.) Allah Ya ce: ((Kuma lalle Ni haƙiƙa Mai gãfara ne ga wanda ya tuba kuma ya yi imãni, kuma ya aikata aikin ƙwarai, sa’an nan kuma ya nemi shiryuwa)). (Suratu Ɗ.H.: 82). Don haka, Alƙur,ani da Sunna masu tsarki, dukansu wahayi ne daga Allah zuwa ga ManzonSa Muhammad (S.A.W.), kuma tushe ne na hukunce- hukuncen Shari,ar Musulunci, waɗanda suka mayar da mutum ga halin da Ubangiji Ya halice shi a kai, Ya kuma sanya shi mutumin da ya san hanyarsa zuwa ga rayuwa ta ƙwarai, yana mai nanata faɗin Allah (S.W.T.) : (( G‘diya ta tabbata ga Allah, wanda Ya shiryar da mu ga wannan. Kuma ba mu kasance munã iya shiryuwa ba, bã d‘min Allah Ya shiryar da mu ba.)). (Suratul A,raf: 43). Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabinmu Muhammad (S.A.W.) da ,yan gidansa da Sahabbansa.
Posted on: Tue, 16 Jul 2013 20:16:28 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015