ANYA WADANNAN ZINDIKAN MUTANEN BA SU DA TABUWAN HANKALI - TopicsExpress



          

ANYA WADANNAN ZINDIKAN MUTANEN BA SU DA TABUWAN HANKALI KUWA!!! Ku ji maganar da wani Muridin Shehu ya kuma fada a kan Status da nai Sharing daren jiya daga page din Darus-sahabah, akan tattaunawar da akai da Shaikh Alhassan Saeed, wanda ya bada amsa cikin ilimi da basira ba son zuciya ba. Ga comments din da Jahilin muridin Shehi Usmaniyyah Dagauda: Usmaniyya Dagauda wanda yazagi shehi tabbas zai iya zina da uwarsa koshi waye Yesterday at 10:59pm • Like Usmaniyya Daguda Wallahhi duk mai neman rahama wajen Allah bazai zagi masoyin Annabiba. Zagin shehi sai la.ananne dan wuta 11 hours ago • Like Ga dai maganganun, na Shaikh Alhassan Saeed wanda na dauko daga Darul Sahabbah: WANAN SHINE MATSAYAR-MU. -Sheikh Alhassan Sa’eed Aminiya ta tuntubi daya daga cikin malaman kungiyar Izala da aka gudanar da taron hadin kai da shi a kasar Saudiyya domin jin ta bakinsa game da bayanin da Sheikh dahiru Bauchi ya yi: Aminiya: Me za ka ce kan bayanin da Sheikh dahiru Usman Bauchi ya yi cewa taron da kuka yi na hada kan musulmi a Makkah siyasa ce da yaudara, domin duk lokacin da kuka yi irin wannan taro da zarar kun dawo Nijeriya sai kowa ya kama gabansa ku cigaba da sukar juna? Sheikh Alhassan Sa’eed. To, abu biyu zan fada ko uku, na farko, kila shekaru sun fara yi wa Malam yawa, na biyu shi ne ko kuma yana da wata damuwa ta musamman, na uku ko kuma yana da wata bukata ta musamman. Amma mutum ya dubi wannan haduwa ya ce yaudara ce ina yi masa tsoron haduwarsa da Ubangiji. Saboda haka ni a wurina wannan yunkuri da ake yi na hada kan musulmin Nijeriya gaskiya ne. Idan ya ce yaudara ce to a wurinsa ne yaudara. Aminiya: To, me zaka kan bayanin da Malam ya yi cewa ba za su taba haduwa da ‘yan izala ba har sai sun daina kafirta su sun dawo suna binsu sallah? Sheikh Alhassan Sa’eed: Ban gane kafirci ba, idan an ce wanda ya ce yana da wani abu da ya wuce Alkura’ani ba musulmi ba ne, ko wanda ya ce yana da wani matsayi da ya fi na Annabi ba musulmi ba ne, ina jin wannan ba zagi ba ne. Kuma wannan kira ne na cewa a dawo a tafi abu guda daya, mu yarda cewa Annabi Muhammad (SAW) shi ne yafi kowa a cikin halittar Allah, kuma Allah Shi ne mahalicin kowa, saboda haka wannan shi ne abin da za mu fada. Idan wadannan abubuwa da muke fadi shi ne ake cewa kafirtawa ne, to ba za mu daina wannan ba. Domin ba mu yarda akwai wanda ya fi Annabi ba, ba mu yarda gashin kan wani ya fi sahaban Annabi ba, ba mu yarda wani yana da abin da ya fi Alkura’ani ba, ba mu yarda wani yana wani abin da ya fi saukar Alkura’ani har sau dubu 6 ba. Kuma ba mu yarda wani ya auri mata a bai wa wani a ce ya cire mata gashin minkiri ba, ba mu yarda a ce wani ya ce zai shiga Aljannah tun daga nan duniya ba, saboda haka ba ma kafirta kowa. Za mu bi sallah ga dukkan wanda bai yarda da wadannan muyagun abubuwa, amma wanda ya yarda da su ba za mu bi shi sallah ba, sai idan ya bar wadannan abubuwa ya dawo ya tsaya kan Alkura’ani da hadisan Manzon Allah (SAW), bai yarda a ce akwai abin da ya fi Annabi ba, bai yarda a ce wani ya fi sahaban Manzon Allah ba, bai yarda akwai abin da ya fi Alkura’ani ba, bai yarda a ce za a sayar wa da mutum Aljannah ba, za mu bi shi sallah. Aminiya: Wadannan hanyoyi ne kake ganin za a bi hada kan musulman Nijeriya? Sheikh Alhassan Sa’eed: Hanyar da za a hada kan musulman Nijeriya shi ne mu dawo mu rike Alkura’ani da hadisan Manzon (SAW), idan muka dawo muka bi wannan hanya al’ummar musulman Nijeriya za mu hade, mu dunkule mu zamo daya. Amma ni a ganina ai musulman Nijeriya sun riga sun dunkule, don a yanzu wadansu masu irin wannan ra’ayi na Malam su ma a zuciyarsu ba su yarda akwai abin da ya fi Alkura’ani ko Annabi ko sahaban Manzon Allah ba. Ni tambayata anan, shin ina abin magana don an fadi gaskiya?
Posted on: Tue, 05 Nov 2013 10:26:03 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015