AURE Bautar Ubangiji - taskar Lamido MALAM BUKATA NA SHINE A KASHE - TopicsExpress



          

AURE Bautar Ubangiji - taskar Lamido MALAM BUKATA NA SHINE A KASHE MANI UWAR MIJI NA To bakomai hajia Nabila amma ina son naji tarihin zaman ku da ita bayan hajia Nabila ta karasa labarin da malam ya bukata da cewa wannan bakar tsohuwar ta addabi rayuwa ta kuma ni ina son Dan ta bana iya rabuwa da shi wannan shine dalili na da yasa nake son a kashe ta na huta.sai malam yace to hajia nabila ba damuwa karbi wannan maganin kiyi amfani da shi zata mutu cikin sauki ba tare da an zarge ki ba amma abinda nake son dake sai kin bi sharadin da zan gaya maki yanzu ina son daga yau zuwa kwana arba,in nan gaba ki rika kyautatawa wannan tsohuwar kamar haka ki rika yimata wankin tufafin ta da gyaura mata dakin ta kullum safiya ki kuma rika yimata kirgi abinci mai dadi sai ki rika saka wannan garin maganin a ciki sannu ahankari zai rika cin jikinta har ta mutum amma kuma duk abinda zata yima ki tsawon wannan lokacin kadakiyi rigima da ita ki rika lalabata sannun a hankali kina bata hankuri haka kuma duk abinda mijin ki ya kawo maki na kayam marmari ki rika diba kina bata kyautatawa dai sosai daga nan hajia Nabila tayi sallama da malam ta wuce taje tayi ta kokarin yin abinda malam ya gayamata kwana arba,in basu cika ba sai ga hajia Nabila a gidan malam tana kuka malam ya tambayi hajia lafiya hajia tacewa malam malam don Allahka taimaka mani da abinda zai hana wannan tsohuwa mutuwa domin yanzu a duniya ba wadda yake so na kamar ta sai malam ya cewa hajia Nabila ba wani abin yi dole sai wannan tsohuwar ta mutu hajia nabila tayi ta rusa kuka a gidan malam tun safe har marance malam yayi banza da ita daga karshe hajia nabila tacewa malam wallahi indo wannan tsohuwa ta mutum ba makawa ni ma zan kashe kai na na bita domin na tabbatar duniyar nan ba mai sona fiye da wannan tsohuwasai malam yacewa hajia nabila akwaiwani abin yi sai dai yana bukatar dukiya da sauri hajia ta fadi gaban malam tace wallahi malam in ma zan rasa duk abinda na mallaka har tufafin jikina wannan na yarda sai malam ya cewa hajia nabila zauna wannan tsohuwar bazata mutu ba hasalima maganin da kike saka mata a abinci karamata lafiya yake.Domin tun farkon bayanin ki akan wannan tsohuwa na gano kece da matsala ba ita ba domin na fahinci ba kyautatawa a tsakanin ku kuma kinaauren dan ta ba magana mai dadi ba kuma ganin girman ta alhalin wadda yake dauke da nauyin ki a duniya baki daya ita ce tayi dawainiya da rayuwar sa har kika samu a yanzu sa,anan ita a nata zamani ba haka tayiwa tata uwar mijin ba amma ke gashi kina yimata ya za,ayi ta so ki saboda haka zaman ki lafiya shine kyautatawa gare ta domin na tabbatar bazakiyi sha,awar dan uwan ki namiji ya auro wadda zata wallakata uwar ku ba saboda haka a kiyayi hajia Nabila tayi godiya ta tafi suka zauna lafiya to yan matan zamani ga darasi fa sai
Posted on: Thu, 08 Aug 2013 21:47:18 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015