AZUMIN TASUA DA ASHURA! Bismillahir-Rahmanir-Rahim.... A duk - TopicsExpress



          

AZUMIN TASUA DA ASHURA! Bismillahir-Rahmanir-Rahim.... A duk lokacin da wani umurni ya zo daga Allah da Manzonsa (Sallallahu Alaihi Wasallam)! Ko wata kwadaitarwa ta ibada, inma wata Sallar nafila ce, Ko kuwa sadaka ce, ko ko Azumi ne, ko dai wani aikin Daa wanda zai kusanta bawa ga Allah! To, lallai duk mumini na Qwarai ya kan zama mai Qoqari da himma gami da jajircewa tare da himmatuwa wajen ganin ya aikata wannan aiki. Mumini yana Qoqarin yawaita ayyukan alkhairi ne saboda tabbatarwar shi da sakamakon da zai tarar a wurin Allah. Ya kanyi wadannan alamura ne ba don farantawa wani abin halitta raiba, haka kuma ba wai don ya yaba wani haushi ba, Aa yana yi ne da Ikhlasi domin samun shiga wajen Allah (Taala). Sanin kowannen mu ne cewa a ranakun 9 da 10 ga watan Al-Muharram Sunnah ta tabbatar da Azumin nafila. Kamar yadda ya zo a Hadithin da Imam Muslim ya ruwaito: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yace: ....Azumin ranar Ashura (10 ga watan Muharram) yakan (sanya Allah ya) kankare wa bawa zunubin shekara guda wacce ta wuce. Kamar yadda Annabi yayi Azumin Ashura kuma yayi umurni da Azumtarsa. Sai kuma yace: Idan Allah ya kaimu badI In shaa Allahu zamu Azumci tara ga watan Muharram. Saboda haka wannan itace matsayar mu: Azumtar 9 da 10 ga watan Muharram. Ba zamu Qara wani abu ba bayan wannan, ba kuma zamu rage ba, munanan inda Annabi ya tsaya. Kuma wannan shine tafarki madaidaici. Da wannan ne nake nasiha ga kaina da sauran yanuwa da muji tsoron Allah! Mu dinga yin komai domin Allah. Kar muyi wannan Azumin wasu zindiqai suna sanya baqaqen tufafi suna nuna baqin ciki da dai wasu ayyuka na shirme! Muce to bari mu muyi Azumi domin mu basu haushi, koda kuwa su suna tsokanar mu, suna takalarmu, suna neman mu da mu tanka musu! Aa mu Qyale su. Kawai mu cigaba da Ibadodinmu kamar yadda muka saba ba don muba wani haushi ba. Mu karatu ne a gabanmu yanzu! Muna Qoqarin sanin addinin ne tukunna, su kuma basu san addinin ba, basu kuma neman su sani, sai dai shirme da hauragiya. Da kurin Jihadi Jihadi, kurin baza da wofi. Saboda haka kar mu biye musu duk abinda zasuyi matuqar yar nesa ce, sai dai idan suka shiga huruminmu! Nan kam ba daga Qafa. Allah ya karvi ibadunmu ya kuma Qara mana juriya da haquri, gami da jajircewa tare da juriya da Qarin Qaimi da tabbatuwa akan tafarkin Sunnah, ya kuma ganar da wadanda basu gane ba. (Ameen) *************************** BA-GIRIN-GIRIN-BA dai.......
Posted on: Mon, 11 Nov 2013 21:54:56 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015