Abdullahi a Dakin Tiyata! Hakika na dade ban zubad da hawaye ba, - TopicsExpress



          

Abdullahi a Dakin Tiyata! Hakika na dade ban zubad da hawaye ba, har ma rayuwata ta canza sosai har na koma ina irin cikin yanayi na zullumi da tunani dangane da yadda na shiga a yammacin jiya Larba, sakamakon ganin irin yadda Abdullahi ya galabaita har yake cikin faman ciwo na hadiye fensir da yayi, wanda yazo ya tsaya masa a makwagoronsa. Na tausaya masa ainun, kasancewarsa yaro karami, kuma bai san abin da ake kira zafin ciwo ba, ga yadda ya shiga, har dai lokacin da naga ya kwashe awa ukku zuwa hudu babu wani taimakon daga Likitoci domin rage radadin ciwo da kuma yawan kakin da yake faman damunsa. Baya ga amai har da jini, ba shakka Abdullahi ya fuskanci galabaita mai yawa ta tausayi ganin yadda baki daya yanayinsa ya canza sosai, tamkar dai ba Abdullahi wanda a ranar Talata ya rugo ya tarbe ni da dare domin karbar Yar tsarabar da nayi musu da shi da Yan uwansa ba. Ba shakka maganarsa lokacin da ya farfado ta tayar man da hankali da kuma tausayi mai yawa inda yace man; Baba, Don Allah ka sanya a cire man shi Watau in nemi Likitoci dasu cire masa wannan fensir. Haka kuwa, ai nan da nan hawaye suka zubo a fuskata, yayin da na kau da kaina kada Lema Binanci da M A Faruk dake kusa da ni su gane abin da nake ciki. Kai ciwo, balai ne! Yanzu ma da nake rubuta wannan sakon, hawaye nake sharaf! Haka na rabu da Abdullahi kamin a shiga Tiyata da shi a yanzu, muna yi masa fatan samun nasarar aikin. Allah Ya saka muku da alheri dangane da adduoinku na neman sauki garesa, hakika adduar tayi amfani. Nagode! Nagode! Nagode!!!
Posted on: Thu, 07 Nov 2013 10:54:55 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015