Abokina Madu Iro ya rubuta wannan sharhin: YARIMA, YARIMA, - TopicsExpress



          

Abokina Madu Iro ya rubuta wannan sharhin: YARIMA, YARIMA, YARIMA, ALLAH YA SAUWAQE! Kada mai karatu ya yi mamakin irin wannan kan-batu, ba komai ba ne face fallasa tadin zuci irin na wannan marubuci. Kan-batun yana bayyana yadda zuciya take takaicin dabi’un Sanata Ahmad Sani wanda aka fi sani da Yariman Bakura ne. Me ya sa wannan zuciya take takaicin dabi’un wannan mashahurin dan siyasa? Qila tambaya makamanciyar wannan ta darsu a zukatan wasu, musamman irin wadannan da ke da kusanci da shi, ko dai saboda abarkacin abin hannunsa, ko kuma saboda rashin fahimtar haqiqaninsa. Ko ma dai mene ne zai iya zama dalilin tambayar, amsar tana ga dabi’arsa ce ta wasa da addinin Musulunci. Ya maida addini tamkar katin karta, yana jujjuya shi da dukkan wayonsa don yin galaba a kan abokin hamayya. Akwai wani labari da ake yawan bayarwa game da shi, wanda ake jingina wa Marigayi Abubakar Rimi cewa wai wata rana ya hadu da Yarima a wurin wani taro, sai Yarima ya daga hannu yana mai jinjina wa Rimi a matsayin manyan ’yan siyasa. Sai Rimi ya ce, haba Yarima, ai ku ne manyan ’yan siyasa, saboda ka ga mu mutane kawai muke yaudara, amma ku kuwa har Allah ma kuna yaudararsa. Gaskiya ne ko qarya, abin sani dai shi ne, ana yawan bayar da labarin a tsakanin jama’a. Kuma jama’ar tana jin dadin labarin tare da ganin daidaitonsa a kan wanda ake danganta shi da shi. Idan ma hakan ba gaskiya ba ne, jama’a da dama suna ganin yadda ya gudanar da shari’arsa (bazamfariya), hujja ce da ke gabatar da shi a matsayin dan siyasan da ke amfani da addini domin tarawa kansa magoya baya. Irin haka ne wai kawai a makon jiya sai aka ji Yarima ya kwashi wasu malamai ya kai wa Shugaba Jonathan don su yi addu’ar zaman lafiya a fadar Aso Rock. Wace irin addu’a ce wannan da sai an je fadar shugaban qasa za a yi ta? Shugaban nan ba musulmi ba ne, kirista ne, duk da haka ba a ji wani dan siyasa kirista ya kwashi fada-fada na coci sun je yin irin wannan addu’a a fadar shugaban ba. Amma kamar gilmawar tauraruwa mai wutsiya sai aka ji gogan naku ya kwashi malaman da aka sani da yin wa’azozin Musulunci a kafafen yada labarai. Don Allah wace irin siffa Yarima yake so ya ba wa wannan addini na Allah? Idan da ma a ce shugaban ya yi wani abin a zo a gani ne game da sha’anin gudanar da mulki a qasar, da sai a samu wurin fakewa game da aikin na Yarima, amma abin takaici, shugaban bai yi komai ba kuma babu alamun zai yi komai ko da kuwa nan da shekara 100 ne, amma wai sai ga Yarima, a matsayinsa na dan jam’iyyar adawa, ya kwashi malamai, ba ma ’yan siyasa irinsa ba, sun je yin addu’a, ba kuma a filin sallar Idi ko Jumu’a ba, a’a, a fadar Aso Rock, to fisabilillahi dan uwa da wane irin ido ke nan za a kalli Musulunci? Kada fa a manta Yarima wata alqibla ce (duk da cewa ba haka yake ba a tsakanin musulmin Nijeriya) a idon akasarin ’yan Nijeriya wadanda ba musulmi ba. Suna kallonsa a matsayin wani jagora ko wani masani a addini, musamman saboda bazamfariyar shari’ar da ya qirqira a jiharsa ta Zamfara shekaru 13 da suka gabata tare da yadda ake jinsa a wasu lokuta yana magana da sunan addini (kamar batun aurar da yarinya qarama da a yanzu ake tattaunawa a Majalisar Dattawa). Wadannan dalilai sun sa da dama cikin wadanda ba musulmi ba suna kallon gogan a matsayin wanda yake da ruwa da tsaki a lamarin addini. Wani abin qarin takaicin kuma shi ne, sai ya kasance akwai malamai wadanda suka fi kama da abin da Mujaddadi Shehu Usmanu ya kira da ‘malaman fada,’ suke biye masa. Kamar dama jiransa suke yi, a duk lokacin da ya fige su, sai su samu kansu suna binsa kamar bindi, zuwa duk wata mayanka da zai gigirawa addinin Allah wuqar da ke hannunsa na dama. Kai tir da wannan aiki. Kamata ya yi ya zama cewa irin wadannan malamai su ne a gaba-gaba wurin sanyawa irin wannan dan siyasa birki, amma sai suka zama a gaba-gaba wurin qara giya ga wadannan muradu nasa na siyasa wadanda shi da kansa bai san mafuskantarsu ba bare ranar qarewarsu. An zarge shi da neman kujerar mataimakin shugaban qasa ne, tunda wai, yana ganin shi mataimakin da ke kai, bai da wata martaba da yake qara wa tafiyar shugaban gaba daya. Don haka sai Yarima ya ga cewa, to ai shi yana da irin tasa martabar da zai bayar. Don haka ya kwashi wadannan malamai ya garzaya da su can. Amma shi Yariman ya musa wannan zance da cewa gayyatarsa shugaban qasan ya yi, wai ya kawo masa malamai har fada don su yi addu’ar samun zaman lafiya ga qasa. Tambayar da ake yi a kan wannan musawa ta Yarima ita ce, idan har haka ne, me ya sa shi shugaban qasan bai buqaci malaman su zo fadar da kansa ba? A matsayinsa na shugaban qasa kamar Nijeriya, shin Yarima ya fi shi kusanci da malaman ne ko kuwa ya fi shi sanin hanyoyin da zai gayyace su ne su zo fadarsa? Ashe Yarima ba dan jam’iyyar adawa ne ba? To kuma me ya hada shi da dan wata jam’iyyar game da neman mafita ga qasa? A duk cikin ilahirin ’ya’yan PDP da ke tare da shugaban qasa, shin babu musulmin da zai iya kai wa Shugaba Jonathan malamai ne sai an tsallaka an dauko Yarima? Yayin da makamantan wadannan tambayoyi suke tabbatar da wancan zargi na farko a kan Yarima, haka nan a lokaci guda kuma suna nuni ne da cewa dole fa APC ta yi hankali da ’yan siyasa irin su Yarima wadanda a kullum alamu ke nuna cewa babu wani abu da yake da qima a rayuwarsu face dai burinsu na mulki da tara abin duniya wanda baida ranar qarewa. Idan kuma tabbas haka irinsu suke, to fa ya zama faralin ainihi ga APC ta yi wa kanta karatun ta-natsu. Ta daina yarda ana ganin gig-gilmawar ’yan siyasa irin su Yarima a cikin tafiyarta saboda dalilai biyu qwarara. Na farko, a kowane lokaci zai iya sakinta ya koma inda ya fi maiqo, ta wayi gari fanko idan har ta dogara da shi ne. Na biyu tana iya rasa mutunci a wurin ’yan Nijeriya saboda ganin haqiqanin ’yan jari hujjar siyasa a tare da ita. Ke nan kasuwancin cin riba kawai za a yi da PDP, ba ceto talakawa daga halin ni-’ya su ba. Jam’iyyar da take so ta hau doron mutunci da daraja tare da neman ’yanci ga talakawa, musamman raunana irin ’yan Nijeriya, lalle dole ne a gareta ta nemo rariyar tace tsakuwa daga tsakin da za ta tuqa don wadannan talakawa su ci. A ra’ayin Alqiblata, ya kamata malaman Musulunci da ke Nijeriya su yi gangami na hana Yarima magana da yawun addini tunda tattalin arziqi ya karanta a jami’a ba malantar addini mai girma irin Musulunci ba. Rashin yin haka da za su yi, cutar da addinin ne, yayin da yin hakan kuma taimako ne ga addinin. Shin don Allah ya kyautu ga malamai, wadanda hadisi ya martaba da matsayi irin na ‘Magada Annabawa’ su zura ido dan siyasa irin Yarima ya riqa wasan kura da mutuncin addinin da Allah da kansa ya kira “kammalalle” sannan kuma nazarin hankali a kullum yake qara tabbatar kammalar tasa? Kalla! Bai kyautu su yi haka ba!!
Posted on: Mon, 29 Jul 2013 13:00:25 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015