Allah wadaran Matsoraci. Sahabin nan KHALID bin WALID - TopicsExpress



          

Allah wadaran Matsoraci. Sahabin nan KHALID bin WALID (R.A) {Takobi daga takubban Allah} duk wani yaki da akayi lokacin Manzon Allah (S.A.W), Abubakar (R.A) da Umar (R.A) kuma yayi gwagwarmaya sosai, tsakanin saran Takubba da tabo sun kai kusan dari a jikin sa, amma duk da haka Allah bai nufa zai mutu a wajen yaki ba, sai akan gado acikin dakin sa, da yazo mutuwa yace Allah wadaran matsoraci/ rago. Maana yadda ya shiga cikin abokan gaba kuma ya fita ba tare da ya mutu ba, saboda lokacin mutuwar sa bai yi ba. Amma masu mulki, yan kaauwa, yan siyasa da Saraku na sun kasa cewa komai akan jinin mutanen da kullum ake kashe wa a yankin Barno, Yobe, Adamawa da sauran jahohin Najeriyya saboda tsoron mutuwa. To ga dai abinda Khalid ya fada. Ya kamata ku fito ku yi magana akan abinda yake faruwa don Wallahi mutuwa dole ce ko kun shirya mata ko baku shirya mata ba sai tazo. To kaga gwarama ka mutu akan fadin gaskiya da kamutu kana mai haintar Alumarka.
Posted on: Thu, 06 Mar 2014 21:10:21 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015