Almizan Hausa Wayne Rooney zai rika samun Naira miliyan 90 duk - TopicsExpress



          

Almizan Hausa Wayne Rooney zai rika samun Naira miliyan 90 duk mako Wayne Rooney ya faranta wa daukacin magoya bayan kungiyar Manchester United rai bayan da ya sanya hannu a wani sabon kwantiragin shekaru hudu tare da kungiyar da ke kasar Birtaniya, wanda zai kai shi ga kwasan albashi na zunzurutun kudi har Fam dubu dari uku (N90,000,000) a kowane mako. A baya dai ba a san makomar dan wasan ba sakamakon wata yarjejeniya da aka kulla da kungiyar Chelsea, wadda ita ma ke kasar ta Ingila a baran,sannan kuma saura watanni 18 a ragowar kwantaraginsa da Man U, ga shi kuma wasu manyan kungiyoyin kwallon kafar Nahiyar Turai suka shiga zawarcinsa, to amma a ranar Jumaar da ta gabata sai Wayne Rooney ya sanya hannu tare da Man U, inda zai ci gaba da taka mata leda har zuwa karshen Kakar 2018/19. Manajan kungiyar ta Manchester United, David Moyes ya bayyana wa manema labarai farin cikinsa da yadda tauraron dan wasan na kasar Birtaniya ya zabi ci gaba da kasancewa a a kungiyar, duk kuwa da cewa hamshakan kungiyoyin zakarun Turai na farautarsa. YAN WASAN SUNSHINE SUN YI HADARI A ranar Juma’a ne tawagar yan wasan kungiyar kwallon kafa ta nan gida Nijeriya, wato Sunshine suka yi wani mummunan hatsarin mota akan hanyarsu ta komawa gida bayan da suka kammala horo a sansanin da suka yi a Ijabu Ode da nufin shirye-shiryen tunkarar gasar Premier League na wannan shekara, wanda kungiyar za ta bude da fara wasa da kungiyar Enyimba. Bayanan da ALMIZAN ta samu na cewa hatsarin ya auku ne a garin Ore da ke kusa da garin Ondo, wanda ya kai ga kwantar da yan wasa shida a asibiti sakamaon munanan raunukan da suka ji, yayin da manyan jamian kngiyar hudu suka ji raunukan da ba mai tsanani ba. NEW ZEALAND TA TSALLAKA GASAR DUNIYA Kasar New Zealand ta sami tikitin shiga gasar cin kofin duniya na FIFA na mata yan kasa da shekaru 20 biyo bayan doke kasar Papua New Guinea da ci 3-0 a wasan karshe da suka kara na DFC a birnin Auckland. Kasashen biyu dai da suka fafata sun taka muhimmiyar rawa bayan da suka yamutsa kasashen Vanuatu da Tonga, nasarar da ya kai New Zealand zuwa gasar duniya. BERCELONA TA BIYA TARAR FAM MILIYAN 11 KAN CINIKIN NEYMARA A ranar Talatar nan ce kungiyar Barcelona FC da ke Sipaniya ta biya fam miliyan 11.2 ga Hukumomin kasar don kaucewa karar da aka shigar a kan ta ranar Larabar makon jiya a birnin Madrid sakamakon tuhumarta da aka yi kan badakalar kin biyan kudin haraji na sayen dan wasan kasar Brazil mai suna Neymar da kungiyar ta yi. Mai shigar da kara a gaban kotun dai ya ce ya yi amanna cewa kungiyar Barca ta ki biyan kudin haraji, wanda jimillar sa ya kai kudin Yuro miliyan 9.1 wato Dala miliyan 12.5, kokuma Fam miliyan 7.5 a bisa yarjejeniya biyu da aka kulla na shekarar 2011 da niyyar cewa kungiyar za ta sanya hannu tare da dan wasan, to amma daga bisani ta saba doka ta hanyar kin biya. A nata bangaren, kungiyar ta Bercelona ta ce ita kam ba ta karya wata doka game da kin biyan haraji ba, kuma za ta dauki dukkan mataki domin gyara sunanta da aka bata. A watan da ya gabata ne dai Shugaban Kungiyar ta Barca da ke Spain mai suna Sandro Rosell yayi murabus sakamakon likin da ya fito ne cewa kungiyar ta ki biyan kudin haraji. MESSI NE ZAI KAFA TARIHIN DOKE KOWA Kochin kungiyar Bercelona Gerado Martino ya ce dan wasansa Lionel Messi mai shekaru 26 a duniya zai doke karya duk wani tarihin zura kwallo a raga a kundin tarihin gasar cin kofin Laliga. A yayin fafatawar su da Rayo Vallesa Messi ya jefa kwallaye biyu a raga wanda wannan nasara ta sa yayi kan-kan-kan da tsohon dan wasan Real Madrid wato Raul Gonzalez wanda ya zura kwallaye 228 a gasar La liga. Yanzu dai kwallaye 228 da Messi ya jefa a raga a wasanni 263 da yayi ya wuce na tsohon dan wasan Real Madrid Alfredo De Stefano wanda ya jefa kwallaye 227 a wasanni 359 da ya buga a zamaninsa. Wadanda ke gaban Messi a yanzu sun hada da Telmo Zarra mai kwallaye 251 da Hugo Sanchez mai yawan kwallaye 234.
Posted on: Sun, 02 Mar 2014 15:42:52 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015