An karbo daga Abdullahi dan Busur, (R.A) yace wani mutum (mazaunin - TopicsExpress



          

An karbo daga Abdullahi dan Busur, (R.A) yace wani mutum (mazaunin karkara ) yazo wurin Annabi yace ya Manzon Allah shari’oi sun yi mana yawa a bamu wani babi gamamme da zamu rike. “ Sai Annabi yace kada harshenka ya bushe wajen Ambaton Allah Ahmad ne ya rawaito shi (188, 190). SHARHI; Wannan hadisin yana nuna cewa, wani mutum mazaunin karkara yazo wurin manzon Allah yace dashi ya manzon Allah shari’oi sun yi mana yawa an ce kaza’ ka bar kaza ka bar kaza kayi kaza don haka a fadi wani guda daya wand azamurike wanda ba gudu b ja d aya sai anyi shi ko ana cikin me, Sai Annabi yace, kada harshenka ya bushe wajen Ambaton Allah in dai kana son abin da zaka rike ba wahala kayi komai kudinka komai talaucinka zak iyayi ko kan da mukami ko baka dashi kana kwance, a gadon asibiti ko a gida kake matukar kana d arai zaka iya yi yace, to ga zikirin Allah abin da ake nufi ka zamanto mai ambaton Allah a tsaye Allah yana cewa, ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻳﺬ ﻛﺮﻭ ﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻗﻴﻤﺎ ﻭﻗﻌﻮﺩﺍ ﻭ ﻋﻠﻰ ﺟﻨﻮ ﺑﻬﻢ ﻭ ﻳﺘﻔﻜﺮﻭ ﻥ ﻓﻰ ﺧﻠﻖ ﺍﻟﺴﻤﻮﻟﺖ ﻭﻻﺭﺽ ( ﺍﻝ ﻋﻤﺮﺍﻥ . (Wadanda suke ambaton Allah atsaye da zaune, da in suna kwance kuma suna tunani akan halittar sammar da kassai) (Ali Imran 191) Wannan shi ne cikon hadisi na hamsin idan an kara guda takwas wadanda Ibnu Rajab Alhambali ya kara kenan, kuma wannan shi ne karshen wannan fassarar llittafi mai albarka na Arba’una Hadis abin da duk muka fada na daidai Allah ya bamu lada a kai, wanda mukai kuskure, to Allah ya yafe mana.
Posted on: Tue, 08 Oct 2013 06:40:09 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015