An tona asirin mace mai cikin tsumma a Zamfara Category: Manyan - TopicsExpress



          

An tona asirin mace mai cikin tsumma a Zamfara Category: Manyan Labarai Published on Friday, 24 May 2013 00:00 Written by Shu’aibu Ibrahim, a Gusau Hits: 2485 Wata matar aure wadda ba ta wuce shekara 16 da haihuwa ba, ta yaudari mijinta, inda ta boye tsummokara a cikinta da nufin cewa cikin haihuwa ne. Asirinta ya tonu ne a makon jiya, inda aka kai ta asibiti domin gano musabbabin rashin haihuwarta, duk kuwa da cewa lokacin da ya kamata a ce ta haihu ya wuce. Yadda abin ya faru kuwa shi ne, ita dai wannan mata mai suna Suwaiba, wadda ke zaune a kauyen Mayanci na karamar Hukumar Maru, Jihar Zamfara, mijinta Malam Aminu ne ya aure ta sama da shekara hudu, inda a tsakanin shekarun Allah bai taba ba ta haihuwa ba sai a wannan lokaci ta sami ciki. A lokacin da mijin ya fahimci tana da ciki sai ya tura ta ga wani likita mai suna Malam Yahaya, wanda ya gwada ta kuma ya tabbatar cewa tana da ciki dan wata hudu. Binciken Aminiya ya gano cewa sun taba samun sabani da mijin, inda ta tafi gidansu na tsawon kwana 21, inda bayan an samu sasanci ta dawo dakin aurenta. Mijinta da ’yan uwanshi suka fahimci cewa lokacin da ya kamata Suwaiba ta haihu ya wuce, don haka sai aka fara tunanin akwai matsala; wannan ya sanya aka sake tunanin a tafi a sake gwada ta ko cikin kwanciya yayi. Da yake bayyana wa wakilinmu yadda abin ya faru, mijin Suwaiba ya ce ya sake tura ta wajen wani likita amma ta ki amincewa a sake gwada ta don gano halin da take ciki. Bayan abin ya yi kamari ne sai aka tafi da ita Babban Asibitin Maru, inda aka tafi za a yi gwaji, amma ta ki amincewa da haka. Kan haka ne bincike ya tsananta har aka gano cewa tsumma ne ta cusa a cikinta, ya turo kamar cikin haihuwa. Mijin Suwaiba ya shaida wa Aminiya cewa yana zargin mahaifiyarta da hada wannan yaudara, domin a cewarsa ya dade yana fuskantar matsala daga wurinta, wanda haka ya sanya suke yawan samun sabani da matarsa. Zargin da surukar tasa ta musa, ta ce ita ba ta ma taba sanin lokacin da ’yarta ta samu ciki ba. Ita kuwa Suwaiba, ta shaida wa wakilinmu cewa a karon farko da aka gwada ta, ta san tana da ciki, amma ya zube. Sai dai ta kasa yin bayanin dalilin da ya sanya ta yaudari mijinta da cikin tsumma. Ta nemi mijinta da iyayenta da su yafe mata, haka ba zai sake faruwa ba. Da wakilinmu ya tambayi mijin ko me zai iya cewa a yanzu, sai ya ce ba shi da abin da zai ce sai dai kawai ya bar wa Allah. “Abin da nake bukata kawai shi ne a maida mini da mata dakinta na aure.”
Posted on: Tue, 02 Jul 2013 11:31:51 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015