Aslm. Abubuwan da akeso ayi a ranar IDI. - TopicsExpress



          

Aslm. Abubuwan da akeso ayi a ranar IDI. 1) Gaggauta Tafiya Idi da sauraran Kudubah. 2) Fesa Turare mai Kamshi yayin tafiya idi, ga maza kawai. 3) An so sanya sabon Tufafi, ko wanda ranka yafiso acikin kayanka base fariba anfison kala, 4) Yanka Dabba bayan An dawo daga Idi, shi ne Sunnah. 5) An so ana Tafiya ana kabar bari. ﺮﺒﻛﺍ ﻪﻠﻟﺍ ﺮﺒﻛﺍ ﻪﻠﻟﺍ ﻪﻟﺍ ﻻ ﻻﺍ ﻪﻠﻟﺍ ﻪﻠﻟﺍﻭ ﻪﻠﻟﺍ ﻪﻠﻟﻭ ﺮﺒﻛﺍ ﺪﻤﺤﻟﺍ. Ana yinsu ne zuwa da dawowa, da kuma Bayan ko wacce sallah ta farilla, har sai an kai 3 Ga zul hajji. 6) Sallar idi sunnace me karfi, bisa zance mafi karfi da inganci, har yara Yan mata, da masu Al,ada duka suna fita idi a Sunnah. 7) A kiyaye mummunar shiga, da baiyana Tsiraici , musamman yara Yan mata. An sunnanta Raba Abinci da sadakar Nama da kyauta ga Abokan Arziki. 9) Ziyarce Ziyarce abu ne mai kyau a Shariah ta zaburar ayi musanman a ranar idin. 10) Kada mu manta da yafewa junan mu da Afuwa da sakin fuska, da gaida Manya. ﻞﺒﻘﺗ ﺎﻨﻣ ﻪﻠﻟﺍ ﻢﻜﻨﻣﻭ ﻝﺎﻤﻋﻻﺍ ﺢﻟﺎﺻ ALHERIN ALLAH YA TABBATA GARE MU! TAQABBALALLAHU MINNA WA MINKUM.
Posted on: Tue, 15 Oct 2013 06:35:37 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015