Assalamu Alaikum Sunana A. Sadiq Marubucin Nishadi na wannan - TopicsExpress



          

Assalamu Alaikum Sunana A. Sadiq Marubucin Nishadi na wannan Dandali mai farin jini Ina yiwa daukacin masoya labari na Barka da Shan ruwa da fatar Allah ya karbi Ibadar mu gaba daya amin. Muna godiya ga Allah daya nuna mana wannan wannan Sallah karama lafiya da fatar Allah ya nuna mana ta shekaru masu zuwa amin. Kasancewar watan ramadan ya wuce zamu cigaba da labarinmu na JINI DA TSOKA a inda muka tsaya. Dama mun saurara ne domin samun damar gabatar da Ibadun dake cikin wannan wata mai Albarka. kamin nan zamu dan dawo baya domin mai karatu ya tuna inda labarin namu ya kwana. …….JINI DA TSOKA Kashi na 1 - 4 “ “ Dr. Bashir cikin mamaki ya kara duba “result” din da ya fito daga “lab”. A cikin murya mai karfi yayi kiran sunan Haj. Hafsat. Acan cikin jirin matan dake zaune a bakin “ward” na bangaren mata masu juna biyu, Haj. Hafsat take amsawa cikin fargabar dalilin da yasa likitan yayi irin wannan kira mai tayar da hankali. Tayi tsam ta mike tsaye, acikin rawar jiki ta shiga dakin na likita, ta same shi cikin yanayi na farin cikin abinda ya ke karantawa a takardar dake hannunsa, ga dukkan alamu akwai wani abun alkhairi acikin wannan takarda. Likita ya juya kallonsa zuwa gareta tare da cewa Haj. Hafsat ciki ne dake, ya fada acikin murya mai karfin gaske wanda duk matan dake zaune wajen layin sai da suka ji sautin zancen nasa. Haj. Hafsat a tsaye kawai take ta kasa zama domin ji take ajikinta sam kamar mafarki ne take yi. Haj. Ki zauna mana, a tsaye kawai take hankalin nata sam baya tare da ita. Ita kanta batasan abunda take tunani ba. Don Allah Haj. Hafsat ki zauna mana, godiya a wurin Allah shine mataki na farko da zaki fara yanzu, kamin komai. Magana yake amma sam Haj. Hafsat ba jinsa take ba, sai hawayen dadi ke fita a Idanuwanta. Dr. Bashir ya dake tubur da karfi, a lokacin Haj. Hafsat tayi firgigit ta dawo da hankalin nata a wurinsa. Dr. ya cigaba da cewa a tunani Haj. Godiya zaki fara yima Ubangiji a irin wannan karama da kika samu na ganin Allah ya karbi addu’ar mu. Likita wallahi bazan iya cewa ga ta inda zan fara ba, tana fada acikin alamun kuka, wanda idan farin ciki mai yawa ya samu akan dan Adam yake zuwa amadadin dariya ko makamancinta. Likita Yau bana tunanin zan iya yin barci, Likita yau bana tunani mahaifiyata zata iyayin barci, likita yau bana tunanin mijina Alh. Mukhtar zai iya yin barci. A sakamkon wannan kyautar ta ubangiji da ya bamu, wadda kudi bazasu iya saya ba. Haj. Muyi addu’a ga ubangiji Allah, akan ya tsare mana wannan kyauta tasa, ya nuna mana kin sauka lafiya. Likita na gode matuka da irin hidimarka tare da gudumawar shawarwari da karfin guiwa da kake taimaka muna da shi, da fatar Allah ya biyaka da Aljanna. Domin da kudi zasu iyasa in nuna adadin godiyata akan kokarin da kakeyi akan wannan al’amari, to da ko dukkanin abinda na mallaka zan hannunta shi a warinka bazai isa ya wadatar da irin farin cikin da nake ciki a yanzu ba. Dr. Bashir ya karba da cewa Haj. Ai Allah ne abin godiya, kuma karki manta wannan duk acikin abunda aikin namu ya kunsa kenan, bada shawara da taimako ta kowace irin hanya da zamu iya taimakawa. Yanzu sai ki zabi ta hanyar da kika ga ta dace domin yin Albishir ga Alh. Muhktar domin wanna zance kamata yayi ya fito daga gareki ki kadai. Alhamdulilah, godiya ta tabbata ga Ubangiji mai kowa mai komai. Likita Idan kayi sallah ka tayani godiya da Allah. Cikin zumudi ta fara sallama da likita, saboda matsuwa ta koma gida domin shedawa mijin nata wannan Albishir da babu wani abu mafi girma da ya fishi a wurinta. To Haj. Akwai ababe da ya kammata ki kiyaye a yanzu, amma zan barki ki tafi gida domin na tabbatar da cewa ba komai zai shiga kan naki ba a yanzu. Don haka idan hankali ya kwanta sai ki dawo ranar laraba domin jin matakin da zaki fara dashi. Haj. Hafsat ta sa hannu acikin jaka ta fito da Naira Dubu dari biyu, ta ajiye akan “table” na likita. Wannan tukuicin albishir ne, nawa kamin kasamu sakon na mai gidana na gode. Dr. Bashir Haj. Kuma wannnan bai kamata ya zama kullun ba. Dawainiyar tayi yawa, kuma wannan ina gudanar da aiki nane kawai. Ai tukuici na ce ba wani abu ba. ****** Haj. Hafsat ta fito dakin likita tayi kiran direban nata, cikin hanzari yayi saurin juwo da motar, Haj. Hafsat ta shiga direban ya ja mota suka nufi gida. Tafe suke Haj Hafsat sai tunani kawai take, sai tayi yunkurin ta kira waya ta sanar da mahaifiyarta da sauran ‘Yan uwa da abokan arziki, sai kuma ta sake shawara domin a nata tunanin mai gidan nata kadai ya kamata ya fara jin wannan labari mai cike da Farin ciki. Cikin kankanin lokaci suka isa Unguwar tasu. Basu karasa bakin gidan nasu ba suka tarar da taron jama’a da dama a bakin gidan nasu, tare da ma’aikatar tsaro da kuma ma’aikatan kula da hanya, sai kuma wata zungureriyar motar Asibiti ta “Emargency unit” acikin jerin motocin da ke bakin gidan. Lafiya kuwa driver!! naga bakin gidan namu cike da jama’a. Haj. Wallahi ban da labarin abinda ke faruwa domin koda muka fita ba kowa a bakin gidan namu……………. “ “ Subhanallah driver tabbas akwai abunda ke faruwa a gidan nan maras dadi! Cikin faduwar gaba Haj. Hafsat da driver suka isa bakin gidan, basu ko sami wurin parking acikin harabar gidan nasu ba, sakamakon yawan jama’ar dake wurin. Driver yayi parking daga waje, tun kamin ya karasa tsayawa, Haj. Hafsat ta bude murfin motar ta sako kafarta a waje. Cikin rawar jiki da faduwar gaba ta kutsa kai cikin gidan nata, tambaya take lafiya? Amma takasa samun amsar abunda ke faruwa har sai da ta shiga cikin babban falon sauke baki na fara isa acikin gidan a bangaren Alh. Muhktar. Shigarta keda wuya ta tarar da dangin mijin nata a cikin wani hali mai tayar da hankali a gefe daya likitan maigidan ne keta fafutukar ceton ran Alh. Muhktar wanda yake kwance cikin jini face-face a sakamakon mummunan hatsarin motar da ya faru dashi acikin hanyarsa ta zuwa office a yau da safen nan. Haj. Hafsat a cikin gigita da firgita ta durkusa kusa da mijin nata tana tambayar likitan ya akayi hakan ta faru??? Likita ya amsa da cewa Haj. Kiyi hakuri Alh. ya samu hatsarin mota ne, akan hanyarsa ta zuwa office da safen nan, amma in Allah ya yarda zai samu sauki. Yanzu abunda nake gani zaifi, duk da cewa a cikin Abulance da muka zo da ita akwai ababen da muke bukata, to amma zaifi dacewa mu koma dashi Asibiti domin samun cikkaken taimako daga abukanan aikina, domin kamar rauni ya taba wuyan nasa. Amma da yardar Allah zaisamu sauki. Haj. Hafsat acikin Kuka take amsawa likita mu tafi mana me ake jira ne, ta juya a wajen mahaifiyar mai gidan nata Haj. Kulu tana cewa Umma kome kika gani. Haj. Kulu ta amsa da tabbas zuwa Asibitin zaifi Alfanu. A take Manyan Kannen Alh. Muhktar da yaran gidan nasa suka kama aka kwashi mai gidan nasu, suka dunguma zuwa Babbar Asibiti garin na Gusau. Jerin motoci na Iyalan gidansu Alh. Muhktar da na makwabta, kai kace wani dan siyasa ne aka dauko. Wannan bai zai rasa nasaba da irin Alhairan da taimakon mai gidan na Haj. Hafsat ba. Shigarsu Asibitin ke da wuya aka shiga da Alh. Muhktar Operation room take likitan nasa ya kira wasu ayarin likitoci suka dunguma a dakin domin ceton ransa. Shigarsu Asibitin bai wuce Minti talatin ba amma daukacin mutanen da suka halarci Asibitin kai kace Taron kaddamar da wani sashe na Asibitin ne ake gudanarwa. Duk inda labari yakai a cikin garin na abunda ya faru akan Alh. Muhktar sai kaga daukacin Jama’a na tururuwa zuwa Asibitin. Alh. Muhktar Allah ya yi shi mutum mai son taimako da jin tausayin na kasa da shi, wanda yakai a garin na Gusau sunansa yayi fice akan hakan. A duk lokacin da neman taimako ya taso kama da bada gudumawa wajen harkar Addini da aikin sa kai na anguwanni duk Alh. Muhktar na iya kacin kokarin ganin ya taimaka gaya. A unguwar da yake zaune Makwabtansa masu karamin karfi da yaran unguwar babu wanda yake fatar wani mummunan abu ya faru da Alh. Muktar. Sakamakon kusan duk dawauniyarsu da iyalansu tana wuyansa. Wannan yasa Samun labarin na halin da Alh. Muhktar ya shiga tayi mummunan razana mazauna unguwar da zuri’ar gidan nasu. Wanda da za’ace ana neman wani taimako da zai Iya saka Alh. Muhktar ya dawo cikin koshin lafiyarsa da za’a rasa masoka tsintsiya a sakamakon daukin da mafi yawan mutane zasu kawo akan hakan. Majinyatan dake jinya a Asibitin a ranar sunyi tunanin cewa wani babban ma’aikacin lafiya ne ya kawo ziyara a Asibitin tasu. Acikin harabar Asibitin addu’oi kawai ka keji daga bakunan mutane na neman Allah ya bashi lafiya. Haj Hafsat wadda tuni ta fara fita daga kamanninta domin ganin irin halin da mai gidan nata yake ciki. Kimanin Awa daya da rabi daukacin likitotan dake fafutukar ceto rayuwar tasa suka dauka wajen kokarin sun shawo kan raunin da Wuyan na Alh. Muhtar yasamu, amma abun yaci tura. A lokacin ne likitocin suka rika ficewa daga dakin na Operation daya bayan daya, batare da wani cikakken bayani ga Ilahirin Iyalan gidan Alh. Muhktar ba dake bakin dakin, suna jiran sakamakon aikin ba. Wannan ya sa hankalin duk wanda ya lura da abunda ke faruwa a wurin ya fara tashi. Alh. Yusuf wanda shine babban kane a wurin mai gidan, ya kasa jure abunda yake gani, yayi farat ya bude kofar dakin na Operation ya kutsa kansa aciki, inda ya tarar da Likitan maigidan wanda shi kadai ya rage acikin dakin, ya saka goshinsa akan babban gadon da Alh. Muhktar yake kwance hawaye ne, ke kwarara a idanuwansa. Da ganin haka Alh. Yusuf ya tabbatar da cewa babu rayuwar Alh. Muhktar, yayi yuf ya kware dogon zanen da suka rufe shi dashi, ya tabbatar da abunda yake zargi. Gawar Alh. Muhktar ce a kwance!! Furta kalmar Shahada da karfi da Alh. Yusuf yayi, ya janyo hankalin daukacin Jama’ar dake bakin dakin tare da fahimtar cewa tabbas akwai matsala Babba. Subhallahi!! Fitowarsa a dakin tare da lura da hawayen dake kwarara a fuskar tasa ya fahimtar da duk wanda ke wurin cewa Alh. Muhktar ya rigamu gidan gaskiya. Tabbas duk daukacin jama’ar dake wurin hankalinsu ya tashi da jin zancen mutuwar tasa amma duk fadin taron wurin babu wanda yakai dimaucewa da fitar hankali na Haj. Hafsat, dai dai da mahaifiyarsa bata tsinci kanta a irin halin da Haj. Hafsat ta shiga ba. Haj. Hasfat tayi suma fiye da sau biyar domin jin wannan mummunan labari da bata tunanin akwai abu mafi muni da ya fishi. Haj. Hafsat ta tabbatarwa kanta cewa rasuwar mijin nata batare da sanin cewa tana dauke da juna biyu ba. Wannan wata babbar barazanace a tare da ita………………. “ “ “ Daukacin Iyalan gidan Alh. Muhktar da yaransa sun tsinci kansu cikin wani mummunan halin da baza su iya kwatantashi da duk wani rashi ba. Makwabta da sauran Al’ummar gari da suke da masaniyar irin amfanin Alh. Muhktar a cikin wannan gari, sun ji wannan babban rashi a matsayin wata babbar hasara. Haka aka dauki gawar Alh. Muhktar zuwa gidan sa domin yi masa sutura daga nan a kai shi gidansa na dindin-din (Kabarinsa). Haj. Hafsat kuwa a lokacin da aka kwashe ta zuwa gida, bata cikin hankalinta kwata-kwata. “ “ “ Alh. Muhtar matashi ne mai kimanin shekara talatin da takwas (38). Allah yayi masa arziki na dukiya mai dama tun yana da kimanin shekara Ashirin da biyar, a sakamakon kula da dukiyar mahaifinsa wanda yake shahararren dan kasuwa ne a garin. Alh. Muhktar mutum ne mai kwazo da dagewa a kowane bangare na aikinsa ta wannan ne yayi kokarin hada dan taura biyu, ta hanyar gudanar da karatunsa na jami’a tare da amfani da sauran lokacinsa domin kula da dukiyar mahaifinsa. Bayan kammala karatunsa na bangaren sha’anin kudi (Accounting) da shekara biyu, a lokacin yana da shekara Ashirin da hudu (24) a duniya. Allah yayi wa mahaifinsa rasuwa. Wannan ya kara jefa Alh. Muhktar cikin rashin hutu ta hanyar takalihu da dawauniya da dukiyar mahaifinsa, sakamakon sauran kannensa maza guda biyu duka karfinsu bai kaiba a lokacin wato Alh. Yusuf da Ahmad wadanda dukkaninsu suna karatu ne a makarantar gaba da primary a lokacin. Daga wannan lokaci Alh. Muhktar ya koma a matsayin Uba a wannan gida nasu. Mahaifiyarsu ita kadai ce mahaifin nasu ya aura, Alh. Muhktar shi ne babban Dan sa, sai kuma sauran Kannen nasa guda biyu. Alh. Muhktar ya jajirce matuka wajen ganin ya kula da kannensa da kuma dukiyar da mahaifinsu ya bar masu har zuwa lokacin da suka gama mallakar hankulansu, sa’annan ya mallaka masu kasun gadon mahaifinsu ta hanyar buda masu tasu masana’antar tare da saka ido da shawarwari akan yadda zasu tafiyar da harkokin nasu ba tare da wata matsala ba. Alh. Yusuf da kaninsa Ahmad sun dauki Alh. Muhktar a matsayin Uba ta hanyar bashi dukkanin giramamawa da kulawa, wannan bazai rasa nasaba da yadda suka lura da irin dawauniyar da yake yi dasu ba. A lokacin da Alh. Mansir ya cika shekara Talatin (30) a rayuwarsa, ya samu matsi matuka daga mahaifiyarsa akan maganar aure, wanda shi kansa ya gama kammala shawarar yin hakan ta hanyar lura da babu wani uzuri a tare da shi, wanda zai gabatar a madadin hakan. Mahaifiyarsa Allah bai bata haihuwar ‘Ya macce ba, wannan yana daya daga burinta na ganin yayi aure ko zata samu Jika mace daga wurinsa. Acikin wannan hali ne Allah ya hada Alh. Muhktar da Haj. Hafsat a wani bukin yaye dalibai da aka gudanar a makarantar Islamiyyar tasu Haj. Hafsat inda aka gayyaci Alh. Muhktar a matsayin Babban bako a taron. A wannan buki na yaye dalibai an gudanar da bada kyautuka ga dalibai masu hazaka, inda Haj. Hafsat ta karbi kyauta daga hannun babban bako wato Alh. Mukhtar, akan dalibar da tafi natsuwa da tsafta a jerin daliban da za’a yaye. Daga wannan lokaci ne Alh. Muhktar ya ji yana sha’awar Hafsat la’akari da yadda kamalar ta da natsuwar ta take. Iyayen Hafsat ba masu karfi bani, ma’ana talakawa ne, “kadaran kadahan” ta hanyar arziki, wannan yasa Haj. Hafsat bata samu damar yin karatu boko ba a makaranta mafi ingaci ba. Domin kuwa a wannan lokaci ta kammala karutun ta na secondary amma sakamakon jarabawar bai fito da kyau ba. Don haka suka yanke shawarar yi mata aure idan ta samu miji. Duk da cewa akwai mata ‘Yayan masu hali, da kan nuna kulawarsu akan Alh. Muhktar amma shi bai bada karfi akan hakan ba, domin yakan yi la’akari da yadda wasu daga cikin abokanansa kan yi aure daga manyan gidaje amma daga baya su kasa tafiyar da saitin gidan nasu, domin matan nasu na tinkaho da dukiyar mahaifan nasu, don haka babu isasshen ‘control’ a irin wadannan gidaje. Wannan ita ce babbar hujjarsa tare da yanke shawarar neman aurensa a gidajen masu karamin karfi Idan har yayi dace da ‘Ya mai tarbiya wadda ta kwanta masa a rayuwa. Acikin wannan ne suka hadu da Hafsat. Bayan kammala wannan buki na yaye dalibai, Alh. Muhktar ya nemi gidan mahaifan Hafsat daga shugaban makarantar, inda daga bisani, ya aika magabatansa da a nema masa iznin neman aure Hafsat. A lokacin da mahaifin Hafsat ya samu labarin cewa Alh. Muhktar ne ke neman iznin neman auren ‘Yarsa. Bai yi wata wata ba yace a mayar masa da sakon cewa ya bashi auren Hafsat, ba ma takan maganar neman izni ba. Wannan ba zai rasa nasaba da sunan da Alh. Muhktar yayi wajen Alhairai da taimako akan al’ummar wannnan gari na Gusau ba. Ita kanta Hafsat bata tsaya wani Ja’inja ba wajen amincewa da wannan tayi na Alh. Muhktar ba, wanda take ganin kamar wata baiwace Allah ya aiko mata ba. “ “ Alh. Muhktar bai bata lokaci wajen neman auren Hafsat ba ganin yadda ta nuna masa kauna matuka, tare da la’akari da yadda Mahaifiyarsa ke kara hura masa wuta akan zancen. Haka aka sha buki acikin ban sha’awa. Iyayen Hafsat sun samu baki a harabar gidansu a lokacin daurin aure wanda a rayuwarsu basu taba tunanin manyan mutane zasu halarta a bakin gidannasu ba kamar haka. Mahaifin Hafsat yayi farin cikin da bazai iya misaltawa ba a wannan rana ta auren Hafsat da Alh. Muhktar. Tun daga dawauniyar buki da kayan dakin Amarya duk Alh. Muhktar ya dauki nauyi tare da Jarin kudi na Naira Miliyan biyu ga Mahaifin Hafsa bayan an kare buki. Hafsat bata san ta wace hanya zata bi domin ta tabbatar da godiyarta akan Alh. Muhktar ba. Domin fada a fatar baki ba zata wadatar ba. Daga karshe ta yanke shawarar irin kalar zaman da zata yi da mijin nata shi zai tabbatar da godiyarta akan wadannan ababen Alhairi da yayi mata. Haka kuwa akayi domin sai da Alh. Muhkatar ya canja wa Hafsat suna daga Hafsat zuwa ‘Yar Aljannan sakamakon kololuwar kyautatawa da biyayya da Hafsat ki yiwa mijin nata. Alh. Mukhtar ya kai matsayin da baya muradin ganin abunda zai bata wa matarsa rai a rin wannan dawainiya da biyayya da take yi akansa da Yan uwansa. Wannan ya kara girman kimar Iyayen Hafsat a Idanun Alh. Muhktar ta hanyar gamsuwa da irin tarbiyar da suka bata. Haka suka cigaba da zamansu cikin jin dadi da anashuwa, babu wanda ya taba jin korafin wata rashin jituwa a tsakaninsu. A lokacin da auren Alh. Muhktar da Hafsat ya kai shekara biyu amma babu ko batan wata a tare da Hafsat, hankalin ta ya fara tashi domin tana da masaniyar bukatuwar Mahaifiyar Mijin nata na samun jika, wanda a duk lokacin da ta tafi gidan nata babu wata hira face magana daya, ta idan macce ce suna kaza za’a saka mata, idan namiji ne kaza za’a saka masa. Haj. Hafsat ta nemi mijin nata da su tafi Assibiti domin gano ko akwai wata matsala a tare da su akan hakan. Ba tare da musu ba, Alh. Muhktar ya kira likitansa a waya ya sanar da shi bukatarsu, shi kuma ya hadasu da likita mai kula da bangaren Juna biyu da Haihuwa. Bayan kammala gwaje gwaje, sakamakon dukkanin bincike ya fito da nuna cewa dukkaninsu suna cikin koshin lafiya da kuma Iya samun juna biyu a kowane lokaci. Alh. Muhktar yayi matukar farin ciki da jin wannan zance, domin baya son ganin damuwar matarsa ko kadan, bare a yi maganar kara wani aure atare da shi. Wanda sam a tunanin shi har mutuwarsa baya da bukatar hakan. Wannan ba zai rasa nasaba da jin dadi da kwanciyar hankali da yake samu ba, daga uwar gidan tasa ba. Duk da jin wannan labari daga bakin Mijin nata na cewa suna cikin koshin lafiya ta iya samun karuwa, amma Hafsat tana jin damuwar a zuciyarta, tare da dukufa da addu’a akan Allah ya bata haihuwa, wanda a yanzu take ganin bata rasa komai a duniya ba face ita kadai. “ “ “ A kwana a tashi Alh. Muhktar da Hafsat suka kwashe shekara biyar (5) babu ciki babu labarinsa. A wannan lokaci duk wani farin ciki da Hafsat ke samu daga wajen Mahaifiyar mijin nata ta sauya kama, abubuwa suka jagule, duk da kokarin Alh. Muhktar na ganin ya kwantar mata da hankali amma ina Haj. Hafsat tuni Al’amurah suka dameta akan wannan zance. Alh. Muhktar ya sha matukar wahala a yukurinsa na ganar da mahaifiyarsa cewa rashin samun haihuwarsa da matarsa ba laifin ta bane kuma ba laifin kowa bane, lokaci ne kawai baiyi ba daga wurin Ubangiji. Amma Mahaifiyar tasa ta dage akan sai ya kara aure domin ta tabbatar da hakan. Daga karshe Alh. Muhktar ya yanke hukuncin fita a kasar Germany domin ganawa da kwararrun likitoci akan wannan matsala. Bayan sun samu cikakken bincike dashi da matarsa amma kuma suka samu sakamako dai-dai da wanda suka samu a Asibitin gida da suka baro. Daga karshe Alh. Muhktar ya yanke hukunci dawowa gida, batare da kara wahalar da kansa akan zuwa wani Assibitin daban ba. Bayan sun dawo gida, Alh. Muhktar ya kira ‘Yan uwansa Alh. Yusuf da Ahmed ya shida masu halin da yake ciki tare da nuna masu irin tayar da hankalin da Mahaifiyar tasu ta nuna akan lamarin da zancen cewa lallai sai ya kara aure. Yusuf da Ahmad suka dauki nauyin cewa zasu sami mahaifiyar tasu su kwantar mata da hankali tare da baiwa Alh. Muhktar tabbacin zasu shawo kan matsalar. Suka yi sallama suka fita. Bayan fitowarsu daga gidan Yayan nasu, tare da la’akarin yadda hankalin Alh. Muhktar ya tashi akan zancen na mahaifiyarsu, Alh. Yusuf da Ahmad suka zauna a mota suna shawarar yadda zasu bullowa mahaifiyar tasu. Tabbas dukkaninsu basasan gani bacin ran Yayan nasu ko alama, domin ganin irin fadi tashi da yake yi domin ganin nasu farin cikin. Alh. Ahmad ya zo da wata shawara da yake gani ita kadaice zata kawo waraka a wannan yanayi, Alh. Yusuf ya ce Ina saurarenka. Ahmad ya ce zamu tafi mu sheda mata cewa sakamakon binciken da suka samu a Asibitin da suka tafi, an gano cewa Matsalar daga wurin Alh. Muhktar take, ta wannan ne kadai zata saurara akan korafin nata. Take Alh. Yusuf ya aminta da wannan shawara ganin cewa babu wata hanya da zasu bi wajen shawo kan mahaifiyar tasu. Haka kuwa akayi, Alh. Yusuf da Ahmad suka dunguma suka nufi gida wurin mahaifiyar tasu suka sheda mata wannan zance tare da nuna mata hankalin Alh. Muhktar ya tashi akan wannan zance, tare da jawo hankalinta akan cewa cigaba da nanata zance a gabansa zai iya jifa shi cikin wani hali na cuta, domin da zarar an tada zance abun yakan dawo sabo a zuciyarsa. Yanzu ma da kyar suka shawo kansa suka bashi hakuri, daga karshe suka nemi da kada mahaifiyar tasu ta tada zancen a garesa idan bashi ne yazo da zancen ba. Har ga Allah Alh. Yusuf da Ahmad sunyi haka ne domin kwantarwa mahaifiyartasu da hankali da kuma kudirin kada ta sake tayar da maganar a gaba, batare da hasashen abunda hakan zai iya bijirowa ba. Mahaifiyar tasu hankalinta ya tashi matuka da jin wannan magana tare da aminta da abunda suka fada mata, kasancewar basu taba zuwa mata da zancen karya ba. Duk wannan abun da ake Alh. Muhktar bai samu takamammen labarin abunda ‘Yan uwan nasa suka shedawa mahaifiyar tasu ba, face ya ga canji matuka a wurin mahaifiyar tasu tare da kara nuna kulawa a wajen matar tasa. Alh. Muhktar yayi farin ciki matuka da samun dawowar soyuwar mahaifiyarsa akan matar tasa, yayi godiya matuka akan ‘Yan uwan nasa na shawo kan matsalar da suka yi ba, tare da yin wani dogon bincike ba akan hanyar da suka bi, wajen shawo kan matsalarba. “ “ “ Mai karatu muhadu a cigaban labarin JINI DA TSOKA Kashi na 5 Domin jin yadda zata kasance. A. Sadiq 07035309199 sadiqcontacts@gmail
Posted on: Fri, 09 Aug 2013 11:57:05 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015