BABBAN LABARI: Karairayi Biyar Daga Bakin Jonathan Daga Idris - TopicsExpress



          

BABBAN LABARI: Karairayi Biyar Daga Bakin Jonathan Daga Idris Aliyu Daudawa da Bashir Ahmad Duk da irin kokarin da Shugaba Goodluck ya yi domin bayyana gaskiya lokacin tattaunawarsa da wasu ‘yan jaridu mai taken Media Chart karo na biyar, wanda aka yi a fadar shugaban kasa a ranar Lahadin da ta gabata, sai da jaridar P.M. ta gano karairayi guda biyar da suka ce shugaban ya gilla. Ga karyayyakin #RARIYA ta tattaro muku su. Kamar yadda shugaban ya bayyana cewa sai a lokacin da PDP ta kafa mulki a 1999 ne aka samar da wayar salula, gaskiyar magana kamar yadda P.M. ta bayyana ta ce an samar da wayar salula tun a shekarar 1993, wanda kamfanin NITEL ya fara samarwa da wani karamin kamfani mai suna MTS a jihar Legas. Kamfanonin biyu da suka samar da masu amfani da su 12,500, sun samar da sabis na E-TACS wanda ya yadu a jihohin Lagos, Enugu da Abuja. Haka, a 1995, MTS da kusa fara ayyuka, sai dai kasa biyan haraji ga NITEL ya dakatar da ita. M-Tel daga baya ya zama layin waya na kamfanin NITEL. Inda ta samar da 090, wannan layuka sun fito da tsadar gaske, wanda hakan ya sa mutane ’yan kalilan ne suka samu damar rikewa. Karin akan hakan, Multi-Links kamfanin ’yan kasuwa ya fara aiki a Nijeriya a 1994. Wanda da farko aka bawa kamfanin lasisin shekaru 10 da damar sake karin shekaru biyar domin kara nisan zangon ayyukan kamfanin. Tun kafin kamfanin ya kara nisan zangon ayyukansa, sai da ya samar da hanyoyin sadarwa akan 01-775 da ya fitar da shi kasuwa. Shugaba Jonathan ya kuma kara cewa tun daga samuwar mulkin PDP, kasa ta shaida samuwar ci gaba na harkokin rayuwa. Abin mamaki ko kuma yana kokarin rufe kasawar da jam’iyyarsa ta yi ne a matakin kasa, ya manta da cewa da yawa daga cikin binciken da yake fitowa duk shekara bai yi daidai da yadda ya bayyana halin da kasar ke ciki ba. Shekarar da ta gabata a misali, kungiyar bincike ta NBS ta yi gargadin karuwar talauci a kasa, rahoton wani mai bincike kan hauhawar talauci, Yemi Kale ya bayyana cewa talauci ya karu daga kaso 54% a 2004 zuwa 69% a 2010 a cikin ‘yan Nijeriya sama da miliyan 112, adadin yayi matukar hauhawa idan aka kwatanta da yawan ‘yan Nijeriya da suka karu cikin wan¬nan shekaru zuwa miliyan 163 a 2010. Rahoton Kale ya kara da cewa adadin zai iya karuwa a 2011, wanda a yanzu kuma da muke 2013 ba a san ya adadin yake ba. Mjalisar DinkinDuniya ta bayyana cewa adadin ‘yan Nijeriya masu cutar HIV shekarar da ta gabata, kasar ita ce tafi kowace kasa yawan masu wannan cuta a duniya. Jonathan ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya ce kadai ke taima-kon malaman jami’o’in kasar nan da ke yajin aiki ta bangaren biyan kudin ariyas, kamar yadda ya ce jami’o’in a ka’ida za su rinka samun kudin su ne daga kudin da suke samarwa kawunansu. Sai dai P.M. ta gano cewa wannan batu na shugaban zuki-ta-malle ce, sa-boda ba ya kunshe cikin yarjejeniya 2009 da kungiyar ASUU ta cimma da gwamnatin tarayya. Da yawa daga cikin ‘yan Nijeriya sun yi mamaki da suka ji Shugaba Jonathan ya ce yajin aikin ASUU siyasa ta shiga ciki. Su kansu malaman jami’o’in sun bayyana jawabin shugaban da rashin kwarewa da suke ganin bai kamata a ce shugaba ne ya yi shi ba. Haka, wata karyar da shugaban ya shirga, ita ce ya bayyana wa ‘yan Ni-jeriya cewa har yanzu bai bayyana burinsa na tsayawa takara a zaben 2015 ba. Ya kuma karyata ganin allon tallan takararsa, wanda ya ce hakan ya saba wa doka ga bayyana takara tunda hukumar zabe ba ta bada damar hakan ba. ’Yan Nijeriya ba su manta da kamfen din kwanan nan da Dam Patience, uwargidansa ta yi ba, a jihar Rivers da Abuja wanda ya hada dubban matan jam’iyyar PDP. Baya ga haka, wasu makusantan shugaban sun dade suna tabbatar da yin takarar shugaban a 2015. Kuma bincike ya tabbatar da cewa rikicin da ya barke a PDP ya samo asali ne sakamakon burin sake tsayawar takarar shugaban. Yayin da shugaban kasa Goodluck Jonathan ke ta wasiwasin ko ya sanar da niyyar da ya ke ta sake tsayawa takara karo na biyu,a wannan hali da ake ciki ko kuma sai nan gaba, sai ga shi jam’iyyar PDP ta kammala shirye shiryen da suka kamata na yin wani taro, wanda za’a yi shi a Abuja ranar 19 ga watan Oktoba na wannan shekara, wanda aka sa ma taken, zanga zagar nuna goyon baya ta mutum milyan biyar, wadda aka shirya musamman domin shugaban kasa Goodluck Jonathan ya bayyana aniyar sa ta sake tsayawa takara a karo na biyu. Wannan zanga zangar nuna goyon baya za ta samu kawa ta mutum milyan biyu a ko wanne sashe cikin sassa shida na kasa, da kuma ta mutum milyan uku a wasu birane da aka kebe. Jaridar Thisday ta ruwaito cewar shi wannan taro akwai wanda ke kulawa da shi wani jami’i daga fadar shugaban kasa, mai suna Chief Obi Oguocha. Akwai kuma ta mutane milyan 20 wadda aka sa ma taken ta ‘Nuna goyon baya ta kasa’ fadar shugaban kasa ce ta shirya tare da jam’iyyar PDP saboda a sanarwa mutane cigaban da shugaban kasa ya yi, tun ranar 9 ga watan Fabrairu na 2010 lokacin da ya fara hawa karagar mulkin kasa a matsayin mai rikon mukamin, ta hanyar wani kuduri da majalisar kasa ta zartar. Ya zama cikakken shugaban kasa bayan an rantsar da shi 6 ga Mayu na shekara ta 2010. Sai kuma 29 ga watan Mayu 2011 da aka rantsar da shi bayan an kammal a zabe. Kamar yadda wata majiya daga fadar shugaban kasa ta bayyani shi wan-nan taro na zanga zangar nuna goyon baya, wani abu ne na farko da zai nuna babu shakka shugaban kasa zai nuna aniyar sa ta sake tsayawa takara karo na biyu, a zaben shekara ta 2015. Shi taron na nuna goyon bayan an shirya shi ne da manufar sanar da ’yan Nijeriya nasarorin da shugaban ya samu, musamman ta bangaren bunk-asa kasa, da kuma nemar ma sa goyon baya tun daga mutanen karkara. Tarukkan goyon bayan da za’ayi a Abuja, sassan kasa guda shida, da na wasu wurare na musamman su ne zasu bada sauki ga Jonathan wajen samun dama ta bayyana sha’awar sat a sake tsayawa takara. Hakanan wannan taro na nuna goyon baya ana son a nuna wa jama’ar Nijeriya cewar da akwai hadin kai a jam’iyyar PDP. Bugu da kari kuma ya nuna cewar tana bayan shugaban kasa Jonathan akan aniyar sat a sake tsayawa takara. Majiyar ta nuna cewar dukkan masu fada a ji na jam’iyyar da suka hada da fadar shugaban kasa, ana sa ran za su halarci shi taron na nuna goyon baya. Dukkan gwamnonin PDP, ministoci, manyan jami’ai na jam’iyyar na kasa, mjalisun jihohi, ’yan majalisu na kasa da jihohi da kuma shugabannin jam’iyyar na kananan hukumomi, na daga cikin wadanda ake sa ran za su halarci taron. Shugaba Jonathan ya bayyana cewa gwamnatinsa ta yaki cin hanci, kuma ma cin hancin ba shi ne babbar matsalar Nijeriya ba, sai da ’yan Ni-jeriya da sauran kasashen duniya koda yaushe na kuka da karuwar cin hancin, musamman a kwana-kwanan nan. Akwai kuma kukan yawaitar barayin man fetur bai taba kaiwa batacce kamar wannan lokaci ba, wanda har ya sa shugaban kafa kwamitin kula da hanyoyin da barayin ke bi suna fita da man. A karshen lissafi, Transparency International ya bayyana Nijeriya a matsayin kasa ta 8 a duniya wadda ta fi cin hanci da rashawa. Hakan ya fito ne a watan Yuli na wannan shekara, lokacin da aka fitar da jerin kas ashen da suka fi cin hanci a duniya, Nijeriya, Zambia, Paraguay, Venezuela, Mexico, Russia, Zimbabwe, Liberia da Mongolia sun kasance a sahun gaba.
Posted on: Sat, 05 Oct 2013 20:38:55 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015