BARKANKU DA SALLAH 1.Assalamu alaikum yanuwa, Na hada muku tare - TopicsExpress



          

BARKANKU DA SALLAH 1.Assalamu alaikum yanuwa, Na hada muku tare da gaisuwa, allah sa kun sallah lafiya. 2.Duniyar marubuta gaisuwa, Dandalin marubuta yanuwa, Sani Yusuf nai muku godiya. 3.Ragaya har burin zuciya, Sai fitattun Mata na biya, Barkanku da sallah bai kulliya. 4.Barista,AG,na yaba, PrP,ban manta ka ba, Aikawa,nai maka godiya. 5.Sani Dala abokin gaskiya, Takwara kullum nai godiya, Allah zumuncin gaskiya. 6.Umar S.A. Ga jinjina, Allah kara zumunci koina, Allah ba mu zama lau lafiya. 7.Baka noma ban barka ba, Danuwa na ne bai sanni ba, Jeka nan a Ayagi ka tambaya. 8.Wanda duk ban sa sunansa ba, Yai min uziri ban ki shi ba, Ni da shi da akwai son gaskiya. 9.Marubuta mata ku kuma, Allah sassaka,Allahumma, Ya tsare mana sharrin kishiya 10Yanuwa Allah mai-maita mana, Rabbana,Allah gafarta mana, Allah sa mu cikin firdausiya.
Posted on: Wed, 16 Oct 2013 07:24:18 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015