BATATTUN AURATAYYA GUDA7 Daga cikin batattun Auratayya wacce - TopicsExpress



          

BATATTUN AURATAYYA GUDA7 Daga cikin batattun Auratayya wacce Annabi s.a.w: 1. AURAN MUTUA:- Shine aure xuwa wani lokaci ambatacce {sananne} ana nesa kona kusa,kamar dai kace mutum ya auri mace akan wani lokaci bayyananne,kama r a wata ko a shekara misali. Haramcin kuwa yaxo a hadisin da aka karbo daga Aliyu bn Abi-talib Allah ya yarda dashi yake cewa lallai manzon Allah s.a.w ya hana auran mutua ya hana cin naman jakin gida a lokacin yakin khaibar Ahmad da Nasai suka ruwaito 2. AUREN MUSANYA {daukewa}:- Shine waliyyi ya aurar ma da wani mutum yarsa,shima wannan mutumin ya aurar masa da yarsa,{exchang e kenan} kuma a tsakaninsu babu sadaki. Saboda annabi s.a.w yace Babu auren bayeyeniya {musanya ko exchange} a musulumci Muslim da Tirmidzi suka ruwaito 3. AURAN WANDA YA DAURA HARAMI:- Shine mutum yayi aure alhalin yayi harama da hajji ko umurah kafin ya sauke harami. Fadinsa s.a.w cewa Wanda ya daura harami baya bada aure kuma baa aura masa 4. AUREN KASHE WUTA:- Shine a saki mace saki uku,da wannan sakin ta haramta ga mijinta tabbas,amma sai ta auri wani mutum daban da manufarcewa ya halartawa wancan mijin nata na farko ita,abin nufi su dau xauna na wani lokaci ya sake ta ta koma gidan mijinta na farko,wannan auren bataccene qadtan. An karbo hadisi daga Abdullahi dan masud Allah ya yarda dashi yace Manzon Allah s.a.w ya laanci wanda ya halatta ko wanda aka halatta masa irin wannan auren kenan wanda bayani akansa ya gabata. Tirmidzi,Abu dawud,Bn majah da Ahmad suka ruwaito 5. AURE CIKIN IDDA:- Shine mutum ya auri mace mai idda ko ya kasance na takaba ko kuwa na saki. Allah madaukakin sarki yace Kada kuce zaku kulla igiyar aure tsakaninku da mata a yayin da suke takaba,har sai littafi ya kai ajalinsa abinda ake nufi da littafi anan shine har sai hukuncin da Allah ya zartas a littafi yazo. Hukuncin kuwa shine sai sun kai wata hudu da kwana goma,anan ne xaa iya daura aure. Malamai suka ce matukar bata gama idda ba sukayi aure har ya sadu da ita taci sadaki,kuma ta haramta gareshi har abada koda kuwa ta gama iddarta ne. 6. AURE BA TARE DA WALIYYI BA:- Shine mutum ya auri maci ba tare da iznin waliyyinta ba. Saboda fadin annabi s.a.w Babu dukkanin wata aure face da waliyyi Malamai sukace idan har hakan ta faru babu waliyyi to matar taci sadakin matukar ya shafeta {abin nufi ya sadu da ita},kuma yana halatta ya aureta bayan tayi istibrai. 7. AURAN KAFIRI KO KAFIRA BA MAABOTA LITTAFI BA {christians}:- An haramtawa musulmi auran kafira,kamar yadda baa halattawa musulma aurar kafiri ba. Allah madaukakin sarki yace La hunna hilla lahum,wa laa hum yuhilluna la hunna
Posted on: Tue, 05 Nov 2013 21:04:43 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015