BAYANI A KAN ILIMIN ALKUR’ANI (Mu’ujizarsa, Saukarsa, Yadda - TopicsExpress



          

BAYANI A KAN ILIMIN ALKUR’ANI (Mu’ujizarsa, Saukarsa, Yadda Aka Tattara Shi Da Falalar Karatunsa) Wallafar: Shaikh Aliyu Muhammad Sa’id Gamawa *** Darasi Na Uku (3) *** ================================== MU’UJIZAR ALKUR’ANI (1) Manzannin da ALLAH (S.W.T) Ya aiko tun daga Annabi Nuhu (A.S) zuwa kan Annabinmu Muhammad (S.A.W) kowa da irin baiwar da ALLAH kan zaba ya kebance shi da ita, don ya zamo darasi da kuma nuni ga mutanensa cewa daga ALLAH Yake. Amma kowane Manzo mu’ujizarsa tana shudewa ya zamo sai labarinta, amma banda Alkur’ani, wadda tana cikin mu’ujizozin Annabi Muhammad (S.A.W). Ga misali kamar haka : (1) ANNABI SULAIMAN (A.S): Yana da mu’ujizozi masu yawa a ciki ya yi magana da tsuntsu kuma yaji tururuwa kamar yadda ya zo a cikin Alkur’ani a Suratul Namli : "وحشر لسليمان جنوده من الجن والإنس والطير فهم يوزعون. حتى إذا أتوا على واد النمل قالت نملة يا أيها النمل ادخلو مساكنكم لا يحطمنكم سليمان وجنوده وهم لا يشعرون. فتبسم ضاحكا من قولها وقال رب أوزعني أن أشكر نعمتك التي أنعمت علي وعلى والدي وأن أعمل صالحا ترضاه وأدخلني برحمتك في عبادك الصاليحن" «Kuma aka tattaro wa Sulaiman rundunoninsa daga aljanu da mutane da tsuntsaye, kuma aka kange su cikin ayari; har aka iso kan rafin tururuwa, sai wata tururuwa ta ce, “Ya ku jama’ar tururuwa, ku shiga gidajenku kada Sulaiman da rundunoninsa su tattaka ku, alhali ba su sani ba.” Sai ya yi murmushi yana mai dariya daga maganarta, kuma ya ce, Ya Ubangijina Ka cusa mini godiya da ni’imarKa wadda ka ni’imta gare ni…» (27 : 17-19). Haka kuma Annabi Sulaiman ya yi magana da Alhuda-huda (wato daya daga cikin tsuntsayen da ke cikin ayarinsa) kamar haka : "فمكث غير بعيد فقال أحطت بما لم تحط به وجئتك من سبإ بنبإ يقين" «Sai ya zauna ba da dadewa ba (wato Alhuda-hudan) sannan ya ce, “Na san abin da ba ka sani ba, kuma na zo maka daga Saba’i da wani labari tabbatacce”» (27 : 22). Bayan Annabi Sulaiman ya saurare shi sai ya ce, "قال سننظر أصدقت أم كنت من الكاذبين. اذهب بكتابي هذا فألقه إليهم ....." « Za mu duba, shin ka yi gaskiya ne ko kuwa ka kasance daga makaryata, ka tafi da takardata wannan, sannan kuma ka jefa ta zuwa gare su….. » (27 : 27-28). (2) ANNABI MUSA (A.S): Cikin mu’ujizozinsa yakan jefa sandarsa ta zamo macijiya, ko ya saka tafin hannunsa a hammata ya fitar da shi yana haske. Cikin Suratul Shu’ara’i, Allah Ya ce: "فألقى عصاه فإذا هي ثعبان مبين. ونزع يده فإذا هي بيضاء للنظرين" «Sai ya jefa sandarsa, sai ga ta ta zama kumurci bayyananne, kuma ya fitar da hannunsa sai ga shi ya zama fari ga masu kallo.» (26: 32-33). (3) ANNABI ISA (A.S): Cikin tasa mu’ujizar yakan rayar da matattu, yana warkar da makaho, da mai albaras da sauransu. Tabbatacin hakan kuwa ya zo alal misali a cikin Suratul Ali Imrana kamar haka: "ورسولا إلى بني إسرائيل أني قد جنتكم بأية من ربكم أني أخلق لكم من الطين كهيئة الطير فأنفخ فيه فيكون طيرا بإذن الله وأبرىء الأكهيئة الطير فأنفخ فيه فيكون طيرا بإذن الله وأبرىء الأكمه والأبرص وأحي الموتى بإذن الله وأنبئكم بما تأكلون وما تدخرون في بيوتكم إن في ذلك لأية لكم إن كنتم مؤمنين" «Kuma (Ya saka shi) manzo zuwa bani Isra’ila (yana mai cewa) Lalle ne hakika na zo musu da wata aya daga Ubanjinku, lalle ne ina halitta muku daga laka kamar siffar tsuntsu, sannan in yi hura a cikinsa, sai ya kasance tsuntsu da izinin ALLAH, kuma ina warkar da wanda aka haifa makaho, da kuturu, kuma ina rayar da matattu, da izinin ALLAH. Kuma ina fada muku abin da kuke ci da abin da kuke ajiyewa a cikin gidajenku. Lalle ne a cikin wannan akwai aya a gare ku, idan kun kasance masu yin imani» (3 : 49). (4) ANNNABI MUHAMMAD (S.A.W): Duk wadannan kadan ke nan daga cikin Mu’ujizozin da ALLAH Ya yi wa wasu daga cikin bayinSa. Sai dai wadannan Manzanni littafin da aka aiko su da shi ba shi ne mu’ujizarsu ba, amma Annabinmu Muhammad (S.A.W), Littafin da aka aiko shi da shi da shi zuwa gare mu shi ne Mu’ujizarsa. Abin da yake cikin Alkur’ani ba ya tsufa, ko a ce yayinsa ya wuce, ko zamani ya bijiro da wani sabon abu da babu a cikin Alkur’ani. Mu saurari cigaba insha Allah.
Posted on: Mon, 30 Sep 2013 10:54:50 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015