BAZAZZAGE MAI CIN-CIN Watarana BAZAZZAGE. ya kai ziyaran gaisuwa - TopicsExpress



          

BAZAZZAGE MAI CIN-CIN Watarana BAZAZZAGE. ya kai ziyaran gaisuwa gidansu Budurwarshi, bayan an kaishi falo sun gaisa da sirikan shi, da yan uwan budurwar tashi, sai aka kawo masa cin~cin da drinks. Akace da shi Bismillah. Anan BAZAZZAGEN naku yayi Fulaku, yaki sha akayi juyin duniya dashi danya ci, cin~cin din nan amma yaki ci. Sai iyayen yarinyar da yan uwanta suka futa tsakar gida suka barshi suka ce "kila kunyarsu ya keji shi yasa yaki ci" itama yarinyar tace bari inbaka guri kaci tunda nima yau kunya ta kake. BAZAZZAGE yace; mata haka zaki ce ko? Tace Eh! Tasa kai tana murmushin kauna ta fita. Ai fitarta ke da wuya sai ya dauki kwanon cin~cin din ya juye rabi a cikin hularshi, ya mai da murfin ya rufe. Ya kifa hularsa akai kamar bashi ba, Yana muzurai. Bayan wani dan lokaci Budurwar tashi ta dawo, suka dan taba hira yace mata zai tafi tace kadai ki cin komai yace, mata na koshi ne shiyasa sweety nah. Me zai faru ya fito tsakar gida suna bankwana da iyayenta, kawai sai yaci karo da igiyar shanya aikuwa nan hula ta fado sai ga cin~cin yana zubowa sai BAZAZZAGEN naku ya karkace yace "IKON ALLAH YAU KUMA RUWAN CIN~CIN AKE YI?? #Moh’d Shamaa
Posted on: Fri, 13 Sep 2013 19:49:38 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015