BIKIN MAULIDI AKAN MIZANIN SHARIA. SHIN AKWAI DANGANTAKA TSAKANIN - TopicsExpress



          

BIKIN MAULIDI AKAN MIZANIN SHARIA. SHIN AKWAI DANGANTAKA TSAKANIN BIKIN MAULIDI DA KIRSIMETI? HUKUNCIN MIKEWA TSAYE LOKACIN GUDANAR DA BIKIN MAULIDI. A game da zancen hukuncin mikewa tsaye lokacin gudanar da Bikin Maulidi kuwa ga jerin wasu Hadisai daga Bakin wanda akace wai ana mikewa tsaye ne domin girmamashi,wato Annabi muhammad (saw) inda yake cewa Mikewa tsaye ga wani shugaba aiki ne irin na sarakunan maguzawa na kasar Rume kamar yadda yake a cikin littafin Sahihul muslim da Sunanu Abu Dauda: Hadisi na 413 Annabi (saw) ya gayawa Sahabbansa cewa, Da zunnan kukayi irin aikin mutanen Farisa da mutanen Romawa domin kuwa Talakawansu sukan rika mikewa tsaye lokacin da shugabanninsu suke zaune: Haka kuma Imam Abu Dauda da Imam Majah sun ruwaito cewa. Manzon Allah (saw) ya gargadi sahabbansa cewa kada su rika yi masa abinda mutanen farisa suke yiwa shugabanninsu(wato sukan rika mikewa tsaye lokacin da suka hango su) Haka kuma Imam Ahmad ya ruwaito cewa Annabi (saw) yace: Duk mutumin dake shaawar mutane su rika mikewa tsaye domin girmamashi to wannan mutum ya shirya gurin zamansa acikin wuta. Wannan Hadisi ingantacce ne kuma Imamu Ahmad ne ya ruwaito shi. Sai Hadisin Anas Ibn Malik inda yake cewa: Babu wani mutumin da sahabbai suke sonsa kamar manzon Allah (saw) amma duk da wannan soyayya mai tsanani idan su sahabbai suka hango Annabi (saw) na zuwa gurin su basa mikewa tsaye domin girmamashi saboda sun san manzon Allah (saw) baya bukatar mutane su mike tsaye don girmama shi. Wannan Hadisin ingantacce ne. Imam Tirmizi ya ruwaito shi. Snn33
Posted on: Wed, 04 Dec 2013 08:49:35 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015