BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM Tsira da amincin Allah su tabbata ga - TopicsExpress



          

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM Tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzon tsira Annabinmu Muhammadu da iyalan gidansa da Sahabbansa. Insha Allahu zamu dora ne daga wajen da muka tsaya acikin tarihin SARKIN MUMINAI (SAYYIDUNA UMAR BN ALKHATTAB) Allah shi Qara masa yarda. Sayyiduna Umar (ra) ya auri mataye bakwai ne arayuwarsa. Gasu nan dalla-dalla kamar haka: 1. ZAINAB BINTU MAZUN (yar uwar Sayyiduna Uthman bn Mazun r.a.) ita ta haifa masa yaya guda 3. Abdullahi, Abdurrahman Al-Akbar, da kuma Hafsaru (uwar muminai). 2. MULAIKATU BINTU JARWAL: ita ta haifa masa UBAYDULLAHI (ra). 3. QURAIBATU BINTU ABI- UMAYYAH ALMAKHZUMY : ita ya saketa. basu haifu da ita ba. 4. UMMU-HAKEEM BNTUL HARITH BN HISHAM: ita ta haifa masa FATIMAH. 5. JAMILATU BINTU ASIM BN THABIT (RA): ita ma basu haifu dashi ba. 6. AATIKATU BNT ZAID BN AMRU BN NUFAYL : Ita ta haifa masa dansa mai suna Iyadh. 7. UMMU KULTHUM BINTU ALIY BN ABI TALIB (RA) : ita ta haifa masa ZAIDU da RUQAYYAH. SAI KUMA KUYANGINSA: ★ LUHYATU (mutuniyar Yemen) ta haifa masa ABDURRAHMANUL ASGHAR. ★ FUKAIHATU : ta haifa masa ZAINABU. Gaba dayan yayansa 12 ne. Gasu kamar haka: 1. ZAIDUL AKBAR bn Umar (ra). 2. ZAIDUL ASGHAR bn Umar (ra). 3. AASIM bn Umar (ra) 4. ABDULLAHI bn Umar (ra). 5. ABDURRAHMAN AL-AKBAR bn Umar (ra). 6. ABDURRAHMAN AL-AUSAT bn Umar (ra). 7. ABDURRAHMAN AL-ASGHAR bn Umar (ra). 8. UBAIDULLAHI bn Umar (ra). 9. IYADH bn Umar (ra). 10. HAFSATU bintu Umar (ra). 11. RUQAYYATU bintu Umar (ra). 12. ZAINABU bintu Umar (ra). Abin lura anan shine duk yawancin yayan nasa ya sanya musu irin sunayen yayan Manzon Allah (saww). Ina nufin kamar Abdullahi, Zainab, Ruqayyah, Fatimah (rasuwa tayi). Sannan Sayyiduna Umar (ra) ya auri JIKAR MANZON ALLAH (SAWW) wato UMMU KULTHUM yar Sayyiduna Aliy da Sayyidah Fatimah (ra). Yayi hakan ne domin neman Albarkar dangantaka da Maaiki (saww). Saboda yaji Manzon Allah (saww) yana cewa: KOWACCE NASABA KO DANGANTAKA TANA QAREWA NE ANAN DUNIYA, AMMA BANDA NASABATA DA DANGANTAKA TA. Sannan yayi kokarin auren UMMU KULTHUM YAR SAYYIDUNA ABUBAKR (RA). sai ta Qishi saboda shi mutum ne wanda ba ya son jin dadi arayuwarsa! Ya Allah ka Qara yardarka ga Sayyiduna Umar dan Khattabi ka saka masa da alkhairi abisa hdimar da yayima ANNABINKA da ADDININKA. Anan zamu tsaya sai gobe kuma insha Allahu.
Posted on: Mon, 17 Feb 2014 10:07:43 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015