Baban Manar Alqasim ALLAH YA ISA BAN YAFE BA! 34 Sani ya yi - TopicsExpress



          

Baban Manar Alqasim ALLAH YA ISA BAN YAFE BA! 34 Sani ya yi kuskuren dukan Mari a wani wurin da bai dace ba, don kuwa nan take ta watse qasa sai mimmiqewa take yi tana wani numfarfashi sama-sama, ga wani abu kamar kumfa yana gangaro ma ta daga baki, idanun sai suka juya suka yi sama, a daidai lokacin wasu maqwabta sun ji ihunta har sun kutso dakin domin kawo mata gudummuwa, sai ya zama Sani ya sake shiga tasku, yanzu kam ba shi da wata mafita don ya yi kisan kai, ba in da ba ya rawa a jikinsa sai qoqari yake ya kusance ta don ya tabbatar da cewa tana da sauran rai ko ta cika, amma mutane sun shiga tsakani, sun hana shi kusantar ta, kafin a fitar da ita Malam Salisu da ya shigo cikin hanzari yake cewa ba ta kai ga rasuwa ba a yi maza a kai ta asibi, sani kuwa ko ta kansa ba wanda ya bi, don kuwa an san komai na sa a unguwar, yar kadarar da yake togo da ita ba zai iya barinta ya qara mai ba, ko ma ya yi qoqarin yin hakan yanzu idanun kowa a kansa yake, malam Salisu ya rantse ya qara kan cewa in fa Sani ya yi niyyar guduwa to zai shiga quliya manta sabo, wace a can ne zai qarisa rayuwarsa. Ita kuwa Mari ta farfado tun safiyar Lahadi, wato tun shekaran jiya kenan, yau Talata kuma ba a barin ma su ziyara sai bayan sallar Laasar, shi ma din na saoI Biyu ne kacal, yan mutanen da ke tare da ita qalilan ne, su ne kadai suke da damar shiga wurinta, ko su din sai sun tambayi wata Nas mai koren kaya da ta 6ata rai a gefen babbar mashigar da kowa sai ya bi ta wurinta kafin ya isa dakin da yake so, ko magana ba ta son ta yi da kowa, dan abu kadan ta fara masifa, yanzu ma ta hana hira ta ce za a dami majinyata ne, Sani dai yana gefe guda ya yi tagumi ko me yake tunani Allahu Aalam, Tala kuma ta mayar da Fatu gida qarfi da yaji ta amshi jiyyar domin sanin haqiqanin abin da yake faruwa, Fatu ma ta san za a yi haka shi ya sa ta turje sai da mutane suka sha qarfinta sannan ta fita tana kuka, ana dai ganin kamar halin da Mari ta shiga ne ya rikita ta, amma a zahiri ba ta qaunar kowa ya san sirrin da suka dade ne suna binnewa, tun da kuwa lamarin ya kai ga asibiti tilas sai dai ta yi haquri. Me kike so? In ji Tala, Mari ba ta ce komai ba sai hawaye yake ta gangaro ma ta kamar ruwa, ba dai kasa magana ta yi ba don an ji ta tana rade-radi da mahaifiyarta kafin ta koma gida, Tala ta sake tambayarta, sai ta bude baki da qyar Ba komai...ina Sani yake Tala ta harare shi ba ta ce kanzil ba, ganin haka sai ya matso kusa da Mari jikinsa yana rawa, har da Tala ta fita sai Nas din ta dawo da ita ta ce ta tsaya kar wani abu ya faru, don in ba ya son ganinta yana iya qarisa ta ba a sani ba, sai ta sami wata kujera a gefe ta rashe, duk da cewa ba ta ji dadin abin da Mari da uwarta suka yi ba, tausayin Marin na nade a cikin zuciyarta, dan lokaci kadan za ka ga tana kallonta, don dazu ma suka gama kuka da Fatu sai da aka yi ta ba su haquri, shi kuwa malam Salisu kasa zaman asibitin ya yi ya koma gida Sani ka cuce ni, ka gama da rayuwata, ka zubar min da mutunci a gaban kowa, ka rabani da iyayena, ka haramta min rayuwar qwarai da mutanen kirki, ALLAH YA ISA BAN YAFE BA. Sani yanzu yana cikin farin ciki ne tun da ya fahimci Mari ba mutuwa za ta yi ba, yan sandan da suka sa hannu aka kar6e ta a wannan asibitin sun yi alwashin cewa matuqar ta mutu to shi ma rayuwarsa tana cikin hatsari, sabo da an rubuta cewa ya yi qoqarin yin kisan kai ne Haba Mari ya za a yi mutum ya durqusar da masoyinsa? Don Allah ki yi haquri kuskure ne ya zo ya zauna a gefen gado kusa da ita, Tala ta wani 6ata baki ta ce Mhn! Ta kawar da kai, ba abin da take yi sai harararsa, tun da ta shigo asibitin ba ta yi magana da shi ba Amma ba alkawarin aure muka yi ba Sani, yanzu me kake so na ce wa mamanmu, na ce da ma ina da aure ko yanzu nake so a daura? Kana so ne na ce zina da ma nake yi da kai yanzu a daura mana aure ko da ma ina da aurena shikenan saura tarewa? Wannan maganar ta ba Tala mamaki, sai gwalo ido ta yi tana kallonsu baki bude, shi kuwa Sani ya marairaice ya saukar da murya Mari tsautsayi dai kin san bai da makawa Allah ya riga ya rubuta, kin san an ce waman qaddaral Lahu, yanzu dai ki sami lafiya tukunna albashi duk abin da kika ce shi za a yi ya dan jawo mayafin da ta rufa da shi yana share mata hawaye, jim kadan aka shigo mata da abinci, Sani ya miqe a hankali ya fita, ita kuwa Tala ta matso tana ta zub da hawaye sabo da ganin irin halin da Mari ta tsinci kanta a ciki, duk ta rame ta kwande ta lalace, dama tuni dan kyawun da yake fuskarta ya fara dushewa tun kwanciyar asibitin fari da wasu Nas-nas suka fadi cewa an yi qoqarin zubar mata da ciki ne, a qarshe ma ya zo da matsala, ga shi da murmurewarta wani cikin ya sake shiga, suka ce ba don saar da aka ci ba da shi ma ya sake fita, amma a yi wa mijinta fada in ba haka ba zai sabauta ta, su Tala ba su ta6a jin wannan ba sai wannan karon, Fatu ta ba da izinin a fitar da wannan ma, Sani ma ya goyi baya, yanzu dai ga ta nan Tala tana ba ta abinci tana qin ci tana tura ma tare da fada.
Posted on: Fri, 01 Nov 2013 00:46:37 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015