Bala Muhammad Makosa KASHI NA 2 MUTANE BA SU SAN ITRA BA SUN DAUKA - TopicsExpress



          

Bala Muhammad Makosa KASHI NA 2 MUTANE BA SU SAN ITRA BA SUN DAUKA IN AN CE AHLIL BAIT, SHARIFAI NE AKE CEWA AHLIL BAIT. SUN DAUKA DUK SHARIFI SHI NE AHLIL BAIT IN JI SAYYID ZAKZAKY KO KA SAMI ZUWA ZARIA A JIYA, KA JI JAWABIN SAYYID ZAKZAKY NA RUFE TAFSIRIN KUR’ANI KAI TSAYE?................. TO, SAYYID ZAKZAKY YAYI JAWABI NA TSAWON MINTI 23, DA SEKON 31, NA RUFE TAFSIRIN KUR’ANI, JAWABI MAI MUHIMMANCIN GASKE GA DUKKANIN ‘YAN UWA. DON HAKA, ABIN DA ZA KU KARANTA A KASA, KASHI NA 2 NE, NA JAWABIN SAYYID ZAKZAKY NE, KAI TSAYE, DAGA KALMOMINSA MASU ALBARKA, DA YAYI A JIYAN, CIKIN HUSSAINIYYA BAQIYATULLAH, A GABAN DUBBAN ‘YAN UWA MAZA DA MATA…GA JAWABIN KAMAR HAKA: Na ce, to aiko Sharifai, yanzu ba mu san ko miliyan nawa bane. Wani ma ya bugi kirji ya ce ‘ya’yan Fatima a yanzu sun kai miliyan dari da shirin a doron kasa. Allahu A’alamu, ban san inda ya samu wannan maganar ba. Ba su ne ake nufi ba; ba ‘ya’yan Hassan da Hussaini ba, ba kuma Sayyidodi ba. Mu a wurinmu ba ‘ya’yan Hassan da Hussaini bane kawai Sayyidodi ba. Sayyidodi dukkanin jinin Abdulmudallib, sune Sayyidodi, sune dangin Annabi (SAWA). Na’am, Allah (T) yayi musu wata daraja ta daban; na cewa ya kebance su da haramta musu zakka, wanda yake kazantotin mutane ne. Ya kebance su da khumusi; kuma, wannan don girmamawa ga wannan gida na Annabi (SAWA). Wanda suke ‘ya’yan gidan, suka kiyaye martaban gidan, da kiyaye mutuncinsu, sai su zama kawa ga wannan gida. Wanda suka kuma lalata kansu, su sun tozarta kansu ne, amma gidan yana nan. Kuma Alhamdulillahi, wannan gida, gida ne da Allah ya albarkata da wadanda suka tsaya da kiyaye addini din. Amma, Itra din da ake nufi, wasu kayyadaddun mutane ne guda goma sha biyu; sune aka daidaita su da Alkur’ani. Da su da Alkur’ani dai-dai wa-dai-da ne. Duk inda Alkur’ani yake nan suke, ba za su rabu da Alkur’ani ba, har sai sun cimma Manzon Allah a koramar sa. Ya ce kuma zai tambayesu. Tunda an gwama su, ba ka daukar Itra; Itratil Dhahira, A’immatu Ahlil Bait; ba ka daukar su ba tare da Alkur’ani ba. In ka dauke su ba Alkur’ani ka bace, ba kuma ka daukar Alkur’ani ba su; inka dauke Alkur’ani ba su, shi ma ka bace. Shiriya shi ne, ka gwama su kamar yadda shi ne nasihan wasiyyan Annabi (SAWA). Kuma muna fata, Insha Allahu In Allah ya ba mu dama, karo na uku za mu karanta wannan Alkur’ani… Na’am, kodayake na ce uku; lallai tun shekarar 1400 dai-dai-wa-dai-da, muka fara Tafsiri, kuma har yanzu akwai wasu suna da ‘yan kasusuwan haka. Muka dauko shi tiryan-tiryan. Kodayake an rika samun interval (katsewa), wani lokaci akan tafi wadansu makarantu; akwai wanda aka nausa, aka yi wajen shekara uku, aka dawo aka dora, kama-kama, tsakanin zuwa kurkuku da fitowa, ainihin ya dade bai kammala ba. Wannan ban sa shi a lissafi ba. Akwai kuma wanda aka yi a kurkuku, aka tattara ‘yan uwa da yawa muka taru a kurkukun Kaduna; muka dauko tun daga Baqara, da yake muna yi kullu-yaumin ne. To, shi ma sai da muka kai har cikin Mufassar. Gab da za mu karasa, sai kuma aka rarraba mu. To, duk ba su a cikin lissafi. Da kuma wanda muka yi Ta’alimil Khas, shi ma daban daban; shekara talatin da hudu dindin zuwa yau, daban daban, duk dai ba mu sa su a lissafi ba. Amma Alhamdulillahi, kuma wasu suka ce ya kamata a sami wani lokaci da za a fassara ma mutane Alkur’ani, su ji fassara daga nazarin Ahlil Bait. Sai muka fara da Madhal; na yi amfani da tafsirori guda uku; da Addusi-at-tibyan, wanda yake mujalladi goma ne, wanda ina iya bugun kirji in ce na karance shi duk. Sai kuma Dabrasi, shi ma mujalladi goma ne, irin wannan guda biyar, an gwama bi-biyu a daya. Akwai sabon bugu wanda aka yi shi dai-da-,daidai. To, shi Dabrasi ya kan bi Dusi. Shi Dusi, ya rubuta littafin nan shekara kusan dubu da suka wuce, wafatinsa hijira 460. Kuma ya rubuta wannan tun kafin nan da shekaru, a cikin littafansa na farko farko. Wanda aka ce ma, an taba kama shi aka kona littafansa; sarakai suka kona littafansa. Yana da littafai da yawa ban da wannan. Yana da Tahzib da Istis-sar, yana cikin manya manyan malamanmu. Aka ce da suka kona littafansa ya tafi Najaf, ya rufe daki, sai da ya shekara bai fito ba; yana ta rubutu duk abin da yake tunawa daga littafansa da aka kona. Har mahaifiyarsa ta ce, kai ka zo garin Amiril Muminina, ko ka je ka kai ma shi ziyara? To, shi ne ya bude taga ya ce “Assalamu Alaika Ya Amiril Muminin.” Mahaifiyarsa ta ce, da kunne na na ji ya ce Wa;alaikas-salam ya waladi…… IDAN BA SAK SAMI KARANTA KASHI NA FARKO BA, KANA IYA SHIGA CIKIN WALL DINA ZA MU KAMMALA GOBE INSHA ALLAH
Posted on: Mon, 05 Aug 2013 20:57:53 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015