Bari mu soma magana kan Hadisin da muke nufi: AL KITABU WAL - TopicsExpress



          

Bari mu soma magana kan Hadisin da muke nufi: AL KITABU WAL “ITRA” KO ALKITABU “WAS SUNNAH” 3 Wannan Hadisi ya zo ta hanyar sahabbai da dama. Dukansu suna cikin wadanda ‘yan Shi’ah suka jingina ma ridda bayan wafatin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam. Kamar su Abu Huraira da Zaid bin Arqam da Jabir bin Abdillah da Amr bin Auf da Abu Sa’id Al Khudri. Amma kuma suna azzama Hadisin kwarai da gaske da ruwaya guda daya daga cikin ruwayoyinsa wadda suke ganin ta karfafi akidarsu. Haka kuma sukan hautsina ruwayoyin hadisin don su fitar da wacce suke bukata. Zamu tattauna kan wannan Hadisi – cikin yardar Allah – ta fuska uku: Fuska ta farko ita ce, hanyoyin da aka samo Hadisin da su. Domin abinda bakin malamai ya hadu a kansa ne cewa, Hadisi ba ya zama hujja a addinin Allah, har a iya jingina shi ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam sai an amince da hanyar da aka samo shi. Ma’ana sai maruwaitansa sun zamo masu sheda ta kwarai daga bakunan wadanda suka san su, suka yi hulda ta ilimi da su. Wannan ma shi ya sa aka kai matsaya kan amsar hadisan sahabbai baki daya ba tare da wariya ba. Tunda yake muna neman wanda muka amince ma ne, sai muka sami su Allah ya ce ya amince masu. Mun kuwa sani wannan maganar ba karama ba ce, kuma Allah Ta’ala da ya yi ta ya san abinda take nufi, kuma bai taba warware ta ba. Saboda haka Ahlussunnah sun wadatu da shedar mahaliccinmu a kan su. Amma duk Wanda ba su ba sai an tambayi ‘yan zamaninsa an ji labarinsa sannan ne in ya cancanta ake sanya shi cikin amintattu. Yawan hanyoyi kawai ba ya sa a inganta Hadisi a wurin masana ballantana shahararsa kamar a same shi a littafi 100 misali. Wannan kadai ba ya sa a karbe shi sai an yi nazarin tsanin da aka taka aka dauko shi. Shi ya sa wanda bai sani ba sai ya rudu da yadda ‘yan Shi’ah ke yi; su jejjero sunayen littafai da na malamai don tabbatar da ingancin Hadisi maimakon mayar da hankali a kan isnadinsa. Ga shi kuma ba su Jin kunyar su fesa karya, su jingina magana ga wanda bai yi ta ba, sannan su kai matsayar ce ma Hadisi mutawatiri ne wanda babu kokwanto a kansa, alhalin rubabben hadisi ne da ba ya da madogara ko kwara daya ingantatta. Wannan shine abinda bawan Husaini, ina nufin ABDUL HUSAIN AL MUSAWI ya yi a littafinsa mai suna AL MURAJA’AT wanda a yau shi ne wasu ke kwafowa suna tinkaho, suna cika baki kamar sun zo da wani ilimi mai amfani. Uzurinsu shine ba su sani ba, kuma ba su iya gane basu sani ba ballantana su koma makaranta. To, amma ko wannan uzurin zai ishe su gaban Allah? Rokon da muke yi Allah ya hada mu da su a kan shiriya baki daya. Fuska ta biyu da zamu kalli wannan Hadisi ita ce lafuzzan da ya zo da su. Hadisi ya kan iya zuwa da lafazi biyu ko abinda ya fi. A kan kuma iya samun dukansu sun inganta matukar ba su ci karo da juna ba. Haka kuma Ana iya samun daya daga cikinsu kuskure ne ko ma ganganci daga wani maruwaici wanda ba amintacce ba. Irin nan da zaran an samu son zuciya sai ka ga wasu sun rike wancan lafazin wanda yake kuskure ne sun azzama shi, sun masa wanka da ado har da fesa turare don daukar hankali. Amma duk wannan bai hana masanan Hadisi su jajirce su rarrabe zare da abawa. Fuska ta uku ita ce ma’anarsa da fikihun da ya kunsa. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam balarabe ne. Kuma da harshen larabcin ne ya bayyana duk wata karantarwa da ya yi. Don mu fahimci abinda yake nufi kuwa dole ne mu san wannan yare kuma mu yi amfani da sanin cikin fahimtar maganarsa. Haka kuma kowace magana da ta fito daga tsarkakakken baki to, malamai sukan fitar da fikihunta da abinda take koyarwa. DANDALIN AHLULBAITI DA SAHABBAI. mansoor sokoto.wordpress
Posted on: Tue, 03 Sep 2013 13:23:47 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015